Kabarin manzo



 Wata sheda kuma a kan wannan batu shi ne,bayan rasuwar  Manzo wani balarabe ya shigo Madina yana karanta wannan aya damuka ambata, sai ya ce:"Na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina kuma ina mai neman ceto gareka zuwa ga Ubangijina".Wafa'ul Wafa 4:1361 Adduraru sunniya:21.

  Sannan muhimmin abu kamar yadda Subki yake cewa:Kiran al'ummar musulmi da su ziyarci manzo kuma su nemi gafara da bukatunsu daga garesa wata alama ce ta karrama manzo da girmama sa.Kuma tabbas wannan girmamawa ba ta kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda girma da mukamin ruhinsa a wajen Allah wani abu ne wanda bai mai shakku a kansa kuma madawwami ne, saboda haka bai kebanta da wani zamani ba sabanin waninsa.

 Saboda haka ne malaman Tafisri suka tafi akan cewa, girmama manzo bai kebanci lokacin rayuwarsa ba,saboda haka dole ne a kiyayesa har bayan rasuwarsa.Harma ayar da ke umurta musulmi da su rika magana a hanakali a gaban manzo,tana nan a matsayinta  , inda Allah yake cewa:"Ya ku wadan da kuka yi Imani kada ku daga muryarku saman muryar Annabi".Hujuraat:2.

 Saboda haka bai kamata mutum ya rika magana da karfi a cikin haramin mazon mai tsaira ba.Sannan wannan aya an rubuta ta a kan kabarin manzo,wanda duk ya je wannan wuri ya gane wa idonsa hakan.

B: A Mahangar Sunna:

Mun ga hukunci da matsayin kur'ani akan wannan al'amri yanzu abin da ya rage shi ne ku ga kuma me sunnar manzo  ke cewa a kan hakan..

  Ruwayoyi da dama sun  zo akan wannan batu na ziyarar kabarin manzo,kuma malamai sun yi kokarin tattara su da kuma tabbatar da danganensu.Saboda haka anan a matsayin misali zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:

1-Takiyyud deen subki(ya yi wafati a sheka ta756h)a cikin littafinsa "Shifa'us sikam" ya ruwaito hadisi tare da dangane ingantacce.Shifa'us sikam 5-35.

2-Nuruddin Ali bn sahmudi(ya yi wafati 911H)ya ruwaito ruwaya 17 akan wannan batu, a cikin littafinsa na tarihin Madina sannan kuma ya inganta danganensu.Wafa'ul wafa fi akhbaril darul Mustafa:4:1336-1348.

3-Muhammad fukki daya daga cikin Malam Azahar tare da shafe dangane ya ruwaito matanin ruwayoyi 22 akan ziayar manzo.Attawasul wal ziyara fi shari'a islamiyya:48-50.



back 1 2 3 4 5 next