Ayyuka da Sakamako 2Kalubale Na Uku Ayyuka sun kasu zuwa gida biyu, wadansu ana iya yinsu a madadin wani (kamar hajji da sadaka) wadan su kuwa ba za a iya yinsu ba a madadin wani mutum daban ba (Kamar azumi da salla), saboda haka ta yaya ne wani zai iya yin wadannan ayyukan a madadin wani, alhalin ba a wakiltar wani a cikin wadan ayyukan! Amsa Dangane da ayyukan da ake iya wakiltar wani da wadanda ba za a iya wakiltar wani ba, dole su samo asali daga shari’a, misali karbar musulunci ba ya daga cikin abin da za a iya yi a madadin wani, idan da mutum zai yi kalmar shahada sau dari a madadin kafiri, wannan kafiri yananan a matsayinsa na kafiri ba tare da wani canji ba, amma azumi kamar yadda ya zo a cikin ruwaya ana iya wakiltar wani a cikinsa. Manzo (s.a.w) yana cewa: “Duk wanda ya mutu ana binsa azumi sai waliyyinsa ya yi a madadinsaâ€.[9] Da makamantan wannan ruwayar kamar yadda muka ambata a farkon wannan Bahasi, sannan ta yaya ne wannan mutum zai ce ba a wakiltar mutum a wajen yin salla, amma ya amince da ana iya wakiltar mutum a wajen hajji, domin kuwa dawafi a wajen aikin hajji yana tattare da yin salla, idan har abu ya zamana a wani wuri ana iya wakiltar wani to ai babu bambanci a ko’ina ana iya wakiltar mutum a wajen wannan aikin. Hakim ya ruwaito a cikin Mustadrak dinsa daga Manzo (s.a.w) yana cewa: Yasin zuciyar Kur’ani ce, babu wanda zai karanta ta alhalin yana neman gafarar Allah face sai Allah ya gafarta masa, don haka ku karanta ta ga mamatanku.[10] Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP) Facebook: Haidar Center - December, 2012
|