Neman Tabarruki2Musulmai sakamakon soyayyar da suke da ita ga manzon Allah, idan suka ji labari cewa ga wani wuri inda sawun Ahmad Mahmud (s.a.w) yake, zasu ta fi cikin shauki domin su gane wa idanunsu wannan alama ta shi. Abubuwan da suka shafi wannan a cikin tarihin rayuwar Manzo (s.a.w) suna da yawa ta yadda a zamu iya kawo su duka ba a nan, amma zamu kawo wasu daga cikinsu a matsayin misali kamar haka: 1-Sahabbai Suna Kawo Jariransu Ga Manzo Duk lokacin da aka haifi wani yaro a Madina sahabban Manzo sun kasance suna kawo shi wajen Manzo kafin ya fara cin komai domin neman albarka, sai Manzo ya sanya masa wannan jariri dabino a bakinsa a matsayin ya buda masa bakinsa kenan, kuma sai Manzo ya yi wa wannan yaro addu’a. Ibn Hajar yana cewa: Duk yaron da aka Haifa a Madina bayan hijira tabbas Manzo ya gan shi, domin kuwa sahabbai sun dora wa kanzu cewa duk lkacin da aka haifar musu jariri sai sun kawo wajen Manzo domin ya bude masa bakinsa. A’isha tana cewa: Ana kawo yara wajen Manzo domin neman tabarruki. Abdurrahman Bn Auf yana cewa: Ba za a haifar wa wani sahabi jariri ba face ya kawo shi wajen Manzo (s.a.w) domin ya yi masa addu’a. Lokacin da aka haifi Abdullahi Bn Abbas Manzo da Ahlul baitinsa sun kasance a sha’abi Abi Dalib inda Manzo ya bude masa baki da yawunsa. 2-Neman tabarruki ta hanyar Manzo ya shafi kawunan sahabbai Ba kawai jarirai ‘ya’yan sahabbai ba ne ake kai wa man zo domin ya shafi kawunansu a matsayin neman tabarruki, har sahabbai da kansu sun kasance suna zuwa wajen Manzo domin ya shafi kansu don neman albarka. Ziyad Bn Abdullah yana daga cikin wadanda Manzo ya yi wa addu’a sannan ya shafi kansa. A wannan lokaci ya shafi kansa har zuwa hancinsa. A kan haka ne mawaki yayin da yake yabon bin ziyad inda yake cewa: Ya kai dan wanda Manzo ya shafi kansa, Kuma ya yi masa addu’ar alheri a masallaci. [1] 2-Neman Tabarruki Da Ruwan Alwalar Manzo Da Na Wankansa Daya daga cikin abubuwan da suka shahara a zamanin rayuwar Manzo shi ne, sahabbai sun kasance suna neman tabarruki da ruwan alwala da na wankan Manzo (s.a.w) ta yadda sam ba su bari digon ruwan alwallarsa ya fadi a kasa, idan har ya kasance mai yawa sai su shanye shi, idan kuwa ba shi da yawa sai su shafa ga fuskarsu.
|