Karamomin Waliyyai



3-Kiyayewa Daga Tunane-tunane Marasa Amfani

Daya daga cikin abubuwan da mutum yake guri shi ne yayin dayake ibada ya zamana ya bar duk wani tunani sai na Allah madaukaki. Wadanda suke tunane-tunane yayin da suke yin ibada, wannan ya samu ne sakamakon kasantunwarsu sunacikin tunani marar kaidi na rayuwa, sakamakon hakane suka kasa mallakar tunaninsu yayin da suke bautar Ubangiji. Don haka ne suke gabatar da salla mai raka’a hudu cikin tunane-tunane mararsa iyaka, wato suna gabatar da wannan ibada ba tare da ruhi ba.

4-Fitar Ruhi Daga Jiki

A cikin wannan rayuwar jiki da ruhi kowane yana da bukatar juna, kamar yadda ya kasance ruhi yana so ya juya jiki, yana kokari ne ya kare jiki daga baci da lalacewa. Ta bangare guda ruhi yana bukatar jiki, ta hanyar wasu gabobi na jiki ne yake iya ji kuma yake gani. Amma wani lokaci ruhi sakamakon karfi da kamalar da yake samu, yana wadatuwa daga amfani da jiki, don haka yana iya fita daga jikin.

Dangane da sauran mutane wadanda suke kallon duniya a matsayin kawai wannan duniyar da muke iya gani ta dabi’a yana yi musu wahala su fahimci wannan al’amari. Amma dangane da wadanda suke bisa hanyar Allah suna ganin wannan wani abu ne mai sauki kuma duk lokacin da suke so ruhinsu ya rabu da jikinsu zasu yi hakan. A cikin rayuwa mun san wasu daga cikin mutane yin hakan wani abu ne wanda ya zame musu jiki sam bashi da wata wahala a gurinsu.

5-Ganin Jikunkuna Masu Taushi

Daya daga cikin alamun kusanci zuwa ga Allah shi ne ta yadda mutum zai rika ganin jikuna masu taushi, (ajsamul latifa) a cikin halittar da Allah ya yi akwai wasu halittu wadanda ba a iya ganinsu da idanuwa na zahiri, amma ta wata hanyar mutum yana iya ganin mala’iku suna cikin ta shi a sama. Kur’ani yana cewa:

“Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasai, wanda kuma ya sanya mala’iku a matsayin ma’aika wadanda suke da fikafikai biyu, uku, ko hudu[6].

Don haka a nan zamu iya fahimtar cewa mala’iku jiki ne da su kuma suna da fika-fikai amma ga shi mu ba ma iya ganin wadannan jikuna. Amma bayin Allah na gari wadanda suka kusanci Allah ta hanyar tsarkin ruhi suna iya ganin mala’iku a matsayin jiki. Kamar yada ya zamana Sayyida maryam (a.s) ta ga jibril a cikin siffa ta musamman. kamar yadda Kur’ani yake cewa: “Jibril ya bayyanar mata a cikin siffa ta cikakken mutum”. [7]

Allah madaukaki ba kawai yana ganin mala’iku ba, har ma yana sauraren sautinsu. Imam Ali (a.s) yana bayyana rayuwarsa tare da Manzo a farkon manzanci, ga abin da yake cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next