Karamomin WaliyyaiMatsayi Da Karamomin Waliyyan Allah Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id Samun Karfi Mai Wuce Misali Babu shakka an halicci mutum ne tare da iko wanda yake mai iyaka, da wannan karfi na shi ne yake rayuwa a cikin wannan duniya kuma yake neman taimako daga sauran wasu abubuwan halitta domin ya tafiyar da rayuwarsa. Wannan shi ne iko da karfin da Allah ya bai wa kowane mutum. A kan haka akwai wasu gungu daga cikin bayin Allah wadanda suke da wani karfi da iko wanda ya dara wa na sauran mutane, ta yadda suke iya aiwatar da wani aiki wanda sauran mutane ba su iya aikata shi. Domin samun wannan karfi da iko wanda ya wuce na al’ada akwai hanyoyi guda biyu: 1-Ta Hanayar Tsananin Tarbiyya
|