Neman Ceto



Mala’iku Da Ceto

A ayoyin da suka gabata ba a ambaci sunayen masu ceto ba, kawai an ambaci siffofinsu ne, amma a wasu ayoyin an ambaci sunayen masu ceto. kamar haka:

“Da yawa daga cikin mala’iku a sama cetonsu ba ya wadatar da komai, sai bayan Allah ya bayar da izini ga wanda ya so ya kuma yarje masaâ€‌[8]. A cikin wannan aya an yi nuni da wasu mala’iku a sama wadanda zasu yi ceto a cikin yanayi na musamman.

Ceton Masu Matsayi Abin Yabo

Kur’ani mai girma yana bayyana Manzo a matsayin abin yabo, sannan ruwayoyi suna fassara wannan da cewa, wannan makamin na ceto ne. Dangane da haka ne Kur’ani yake cewa:

“Don gabatar da sallar dare ka ta shi wani bangare na dare, da sannu Allah zai tayar da kai matsayi abin yaboâ€‌[9].

Zamakhsahri yana rubuta cewa: Matsayi abin yabo, wacce wannan aya take ambata, yana nuni ne da matsayin da Manzo zai samu na wanda yarda da shi, duk wanda ya ga Manzo a wannan matsayi zai yabi Manzo a kan samun wannan matsayi, wane matsayi wanda ya fi na ceto wanda dukkan wadanda suka halarci tashin kiyama zasu yabi Manzo a kansa?[10]

Sheikh Tabarasi yana cewa: Dukkan malama tafsiri sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da wannan matsayi abin yabo shi ne mukamin ceto da Manzo zai samu a ranara kiyama, sakamakon haka ne zai samu yabo daga dukkan halitta. Sannan dukkan annabawa zasu kasance karkashin wannan tuta ta Manzo, shi ne kuma farkon wanda zai yi ceto kuma farkon wanda za a karbi cetonsa.[11]

Ruwayi mutawatir suka zo domin bayyana hakikanin wannan aya suna cewa: Abin da ake nufi da wannan matsayi abin yabo shi ne makamin ceto da Manzo zai samu ranar kiyama, Suyudi a cikin Durrul Mansur, Bahraini a cikin tafsirin burhan sun ruwaito hadisai daga shugabannin addinin musulunci, domin mu takaita ba zamu samu halin kawo su ba a nan.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 next