Girmama Kaburbura Masu Tsarki 2Ibn Hajjaj Bagdadi (262-392) wanda yake mawaki ne shararre a iraki ya yi wata kasida ta yabon Imam Ali (a.s), sannan ya yi wannan kasida ne a haramin Imam Ali (a.s) acikin taron mutane, a farkon wannan kasida ga abin yake cewa: “Ya kai ma’abocin wannan hasumiya fara a garin Najaf duk wanda ya ziyarce ka kuma ya nemi ceton Allah daga gareka to Allah zai karbi cetonsaâ€. Wannan baiti yana nuna cewa kabarin Imam Ali (a.s) a farkon karni na hudu ya kasance yana da hasumiya. Abin mamaki a nan shi ne a mahangar ilimin Usul fikh haduwar mutane a kan hukuncin wani abu har zuwa karnoni da dama yana nuna ingancin wannan abin ne. Amma muslmi sun hadu a kan ingancin gine-gine a kan kabarin annabawa da waliyyan Allah tsawon karnoni masu yawa, amma mahangar wasu wannan bai isa ya zama dalili ba, ta yadda kowane lokaci suna kokarin kaucewa a kan yarda da wannan al’amari. Gine-Ginen Tunawa Da Bayin Allah Da Dalilai Masu Sabani A Kan Haka Mun yi bincike a kan dalilan da suke nuni da ingancin ziyar da girmama kaburburan bayin Allah daga Kur’ani da Sunna da tarihin magabata, amma yanzu lokaci ya yi da zamu yi bincike a kan dalilan masu inkarin hakan. Wanda sukan yi riko da hadisin Abil Hayyaj Asadi ne a kan hakan, yanzu zamu auna wannan hadisi ta yadda zamu ga kimarsa ta hanyar ma’aunin da ake gane ingancin hadisi. Muslim a cikin sahih dinsa yana ruwaitowa daga Abil Hayyaj kamar haka: “Ali bin Abi Dalib ya ce da ni: Ba na aike ba akan abin da Manzo ya aika ni a kansa ba, kada kabar wani hoto sai ka lalata shi, ko wani kabari mai tudu sai ka daidaita (baje) shiâ€. Masu adawa da wannan al’amari suna kafa dalili ne da wannan hadisin a kan haramcin gina haramin wani Imami daga cikin Imamai (a.s) sakamakon haka ne a shekara ta 1344Bh suka rusa makabartar “Bakiyya†a wannan rana ne kuma a cikin jaridar “Ummul kura†aka sanya tambaya da amsa dangane da dalilan da suka sanya aka rusa wannan makabarta, domin mu gane ta yadda a ka kafa hujja da wannan hadisi yana da kyau mu yi bincike a kan ma’ana da kuma dangane wannan hadisi: A-Sanadin Wannan Hadisi
|