Girmama Kaburbura Masu Tsarki



 Ruwayoyi da suka zo dangane da son Manzo da iyalansa sun wuce gaban mu kawo su a cikin wannan littafi, saboda haka a nan zamu taikata da wasu ruwayoyi a matsayin misali dangane da wannan al’amari, muhimmin abu a nan shi ne mu san ta yaya wannan soyayya zata tabbata, domin mutum ya isa zuwa ga wannan hadafi akwai hanyoyi guda biyu:

1-Mutum ta hanyar magana da ayyukansa ya yi koyi da koyarwar Allah da manzonsa, ta yadda zai kasance a rayuwa ya yi kokari ya ga bai kauce wa koyarwarsu ba, domin kuwa idan mutum ya zamana yana tsananin soyayya ga wani ba zai taba saba masa ba. Saboda haka ne ake cewa “soyayya ita ce biyayya”. wato sonka da abu yana lizimta maka da yi masa biyayya.

 Sannan Imam Sadik (a.s) a wasu baituka yana bayyana bambanci tsakanin soyayya ta gaskiya da nuna soyayya da ba ta hakika ba, Inda yake bayani akan cewa:

kana sabon Allah alhali kana nuna soyayya gare shi,

wannan ba zai taba yiwuwa ba.

Domin da sonka ya kasance a gaskinya ne to da ka yi biyayya a gare shi,

domin kuwa masoyi yana bin abin da yake so. [18]

2-Bayyana soyayya ta hanyoyi daban-daban kamar haka:

 A- Nuna farin cikin yayin da masoyi yake cikin farin ciki. Da nuna bakin ciki yayin da masoyi yake cikin bakin ciki.

 B-Gabatar da buki na farin cikin a lokacin haiwuwar Manzo ko lokacin tayar da shi a matsayin ma’aiki.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next