Ziyarar Kaburbura Masu DarajaBayan ya gama wannan baiti na waka sai ya nemi gafara ya tashi ya tafi abinsa. Wannan balarabe da muka ambata ya fahimci ma’anar ziyarar kabarin Manzo daga cikin zuciyarsa tsarkakka, saboda haka ne ya taso ya zo domin ya ziyarci shugaban halitta. Wannan ita ce hikimar ziyartar kaburburan ‘yan’uwa, masoya, malamai, shahidai a tafarkin Allah da shugabannin addini (a.s) wanda hankali da shari’a suke tabbatar da ingancinsa. A nan dole ne mu yi bincike ta mahanga daban-daban a kan ziyarar kabari kamar haka: 1-Ziyarar kabarin muminai a mahangar Kur’ani da Sunna. 2-Mata da ziyarar kabari. 3-Ziyarar kabarin Manzo a mahangar manyan malaman musulunci. 4-Ziyarar kabarin Manzo a mahangar Kur’ani da Sunna. A nan gaba zamu yi bahasi ne a kan wadannan abubuwa guda hudu da muka ambata a sama: Ziyarar Kabarin Muminai A Mahangar Kur’ani Da Sunna
|