Hakkin RaiDon haka sarrafa jiki da rai take yi kamar rimot ne da abin da yake sarrafawa na kayan fasaha, da suka hada da talabijin, da radio, da sauran kayan kere-kere. Ba tana shiga cikin jiki ba ne, ba kuma wani bangare ne na jiki ba, sai dai ita kamalar samuwar mutum ce, sannan bajiki ce, don haka babu wanda zai iya riskarta da mariskai na zahiri. Sannan akwai batun mutuwa wacce take wani bangare ne mai muhimmanci a rayuwar mutum, domin mutuwa wani bangare ne na zatin mutum, kuma babu yadda za a guje mata kamar yadda mutum ba zai iya gujewar motsi daga jikinsa ba, haka nan ba zai iya gujewa mutuwa daga ransa ba. Sai dai mu sani mutuwa ita ce yanke alakar da take tsakanin rai da jiki, ba tana nufin lalacewar rai ba kamar yadda jiki yake zama kasa ya lalace. Mutuwa cirata ce daga wannan gidan na duniya zuwa wani gidan na barzahu, kamar yadda mutum yake cirata daga cikin uwa zuwa wannan duniya haka nan yake cirata daga wannan duniya zuwa duniyar barzahu, haka nan zai sake cirata daga barzahu zuwa duniyar lahira. Kuma a kowace duniya ana rayuwa ne sai dai rayuwa ce da ta bambanta da sauran, har sai an je lahira da take kunshe da rayuwar da ba ta karewa. Wadannan duniyoyin sun fara tun daga cikin uwa ne da dan ciki yake samun canji a jikinsa a kodayaushe, kuma jikinsa da ransa suna da rauni, daga nan ne sai ya fado wannan duniyar da take gidan neman kamalar duka jiki da rayuka, a nan ne zamu karfafa domin samun ci gaba. Daga nan kuma sai ya cirata zuwa duniyar barzahu wacce take kama da baccin wannan duniyar tamu, a barzahu bangarorin rai suna da karfi matuka fiye da wannan duniya, za a yaye hijabin da yake tsakanin mutane da abubuwa masu yawa. Kamar yadda dan ciki bai san wannan duniyar ba sai dai ta hanyar tasirin da yake ji, kamar idan an bugi cikin uwa sai ya motsa domin yana ji shi ma, haka nan idan ya zo wannan duniyar ba ya sanin barzahu sai ta hanyar mafarki, wanda yake shi wata kofa ce ta riskar wasu abubuwa da suke kama da duniyar barzahu. Sannan idan mutum ya tafi barzahu haka nan ne zai samu wata alaka mai rauni da duniyar lahira, sai ni'imar aljanna ta rika samunsa idan salihi ne, ko azabar wuta ta rika samunsa idan mujrimi ne. Muna iya ganin wannan baro-baro a cikin ayoyin Kur'ani da suka yi nuni da azabtar da Fir'auna da mutanensa, da kuma ni'imar da shahidai suke cikinta. Don haka ne a kowace marhala ta samuwa tana da alaka da mai biye mata kamar yadda take da alaka da wacce ta gabace ta. Idan mutum yana wannan duniyar yana iya ganin dan ciki musamman ma da samuwar ilimi a yanzu, haka nan wanda yake barzahu zai iya ganin na wannan duniya shi ma idan ya samu dama sakamakon iliminsa da kamalarsa a duniyar barzahu. Kuma dai shi ne hakikanin lamarin da yake wakana ga wanda yake a lahira, zai iya ganin duk wani abu da ya gabace shi, don haka ne ma idan mutum ya yi musu a lahira, sai a yaye dukkan abubuwan da suke da alaka da shi a duniya sai kowa ya gan su, kuma su bayar da sheda a kansa. Haka nan kuma rayuwar da take ga samammu take bambanta daidai gwargwadon yanayin duniyoyin da suke ciki. A cikin uwa ba zai yiwu mu zauna sama da shekara ba, da zara mun kai wata 6-9 to sai duk kowa ya kagu da ganin bayyanarmu a wannan duniya musamman uwa da da yake cikinta da jikinta. Kamar yadda ita kuma wannan duniyar da zarar mun yi shekaru 60-90 a cikinta zata yi kokarin ganin ta haife mu domin mu bayyana a duniyar barzahu. Sanna ita ma duniyar barzahu da zarar mun zauna cikinta mudda ta zamani dubunnan shekarun duniya sai ta furzar da mu zuwa lahira. A barzahu za a iya yin miliyoyin shekaru ko dubunnai kafin zuwa lahira, amma ita rayuwar lahira rayuwa ce ta har abada babu yankewa. Da wadannan matakai masu daraja da wani yake bin wani ne ubangiji mai hikima ya tsara mana yadda zamu rayu har mu kai ga inda zamu dawwama babu karewa. Wannan kuwa domin rai tana son dawwama ne, to sai ta kai ga jiki mai dawwama don haka babu bukatar mutuwa, kamar yadda mutuwa zata kasance babu ita a lahira haka nan babu bakin ciki da sauran miyagun halayen rai kamar hassada a lahira, domin kafin shiga aljanna za a cire wa rai dukkan wadannan cututtukan. Da wannan ne rai zata dawwama cikin sa'ada da rabauta har abada, domin babu wata tawaya ga jikinta, sannan ita kuma babu wani aibi da take da shi, sannan ba zata taba lalacewa ba domin ita abu ne da yake sidif ba mai hauhawa ko yanki-yanki da bangarori ba ce. Da wadannan bayanai ne zamu fahimci cewa rai a duk idan take tana bukatar jiki, sai dai nau'insa yana iya sassabawa daidai gwargwadon yanayin inda take rayuwa. Wannan lamarin babu bambacni idan muka ce mutum ruhi ne kawai shi ko kuma ruhi da jiki ne, ko kuma ba mu ma san hakikaninsa ba, yana nan dai a mutum babu wani canji, sai dai yana da muhimmanci mu san cewa alakar jiki da rai alaka ce ta tarayya ba alaka ce ta kamar kwanduwa da bawon kwai ba. Amma masu ra'ayin komai jiki ne, kuma dukkan abin da ba jiki ba -wato abin da ba a riskar sa da mariskai na zahiri- to ba shi da samuwa, sun fada cikin dimuwa. Sannan abin mamaki fushinsu yayin da ake siffanta su da dabbobi ko ba su da hankali yana nuna lallai akwai abin da ya raba su da sauran samammu, kuma yana tabbatar da samuwar bangaren zatin samuwarsu da shi bajiki ne, wanda muka fi sani da rai.
|