Farisancin Shi'ancib- Sunna Madaukakiya: Ita ce maganar ma’asumi ko aikinsa ko tabbatarwarsa wacce ta zo mana ta hanya ingantacciya daga amintattun adalai, wacce ba zamu iya fahimtar hukuncin shari’a ba sai da ita, kuma dalili ya zo daga Kur'ani a kan cewa hujja ce a fadinsa madaukaki: "Abin da Manzo ya zo muku da shi to ku rike shi, abin da kuma ya hane ku to ku hanu" Hashri: 7. c- Haduwar Malamai: Wannan shi ne haduwar dukkan malamai da take nuna cewa akwai yardar ma’asumi a cikinta, kuma masu haduwar suna da yawa ko kuma ba su da shi, kuma yana nuna dalili ne na Littafi ko Sunna ko hankali, ko kuma akwai wata hanyar da take nuna mana yardar ma’asumi, wacce take dalili ne daga Littafi ko Sunna ko Hankali ba. d- Dalilin Hankali: Wannan yana komawa zuwa ga hankali da dokokinsa yayin da aka rasa nassi ko kuma dalilai suka yi karo da juna kamar yadda aka yi sharhi a mahallinsa. A takaice: Shi ne rizkar hankali a matsayinsa na hankali ga abin da yake kyakkyawa da mummuna a cikin sashen wasu ayyuka da suka lizimci riskar hankali garesu da hankula suka hadu a kansa, wannan kuwa sakamakon halittar hankali a kan hakan, kuma tunda mai shar’antawa shi ne shugaban masu hankula to lallai ya tabbata yanke cewa ya zartar da hukuncin shari’a game da hujjar hankali. Duba zuwa ga sanin muhimmancin wannan madogarai dalla-dalla to zan wakilta wanda yake son bayaninta da fadi zuwa ga wasu littattafai masu zuwa: Cewa wadannan madogarai kuma littattafai na shar’antawa su ne suka hada kashin bayan shari’a da ittafakin dukkan musulmi bisa sabani mai sauki game da bayananta dalla-dalla, kuma tun da madogarar shar’antawa gun Shi'a su ne wadannan to babu ma’anar Farisancin Shi’anci. Idan masu bincike suna nufin Farisancin Shi’anci da cewa dukkan akidunsa ne. to wannan wani abu ne da nake korewa kuma nake nisantarwa, kuma ban ga wani wanda zai iya yin wannan da’awar ba, domin ba yadda za a yi wani ya yi tsammanin kawo hukuncin shari’a daga kabilanci, don haka ne ma masu kawo batun Farisancin Shi’anci sai dai su kawo wani abu daban ba wannan ba. Akwai wasu masu tunanin cewa ma’anar farisncin Shi’anci shi ne; akwai wani irin ci gaban al’adu da wayewar Farisanci da ta shiga cikin Shi’anci kamar yadda yake bisa ma’anarsa ta isdilhi ta hannun wadanda suka karbi Shi’anci daga Farisawa kuma ba su fahimci Shi’anci ba, amma sai aka samu wasu bangare na akidunsu suka shiga Shi’anci, kuma ta wanzu cikinsa tun daga kakanni har zuwa jikokinsu. Wannan kuwa wani abu ne da wasu suka kawo shi, sai dai nan gaba kadan zamu yi nuni zuwa ga irin wasu ra’ayoyi kamar haka:
|