Farisancin Shi'anciBabi Na Biyu A Cikinsa Akwai Wasu Fasaloli Fasali Na Farko: Farisancin Shi’anci Wannan maudu’i yana daga cikin maudu’ai da aka fiye yawaita magana a kansu, kuma a bisa hakika ana neman kange Shi’anci ne kawai kamar yadda a baya na yi nuni da hakan. Masu gaba da Shi'a da dukkan wanda ya bi su na daga mustashrikai da dukkan wani mai neman ganin bayan Shi'a sun sanya wannan lamari ne da suka yarda da shi kuma suka reni dalibansu da su yi riko da shi, kuma suka yi duk wani kokari ta kowace hanya domin ganin sun karfafa wannan lamari da dasa shi a cikin tunanin mutane, kuma ba su bar wata hanya ba domin tabbatar da Farisancin Shi’anci sai da suka yi amfani da ita. Wani abin mamaki shi ne har yanzu wannan kage ba a daina yayinsa ba tare da bayyanar gaskiyar lamari da yaduwar ilimi da bayyanar gaskiya karara, don haka ne ma zan yi bincike kan wannan dalla-dalla saboda muhimmancinsa. Shi’anci a ma’anar lugga yana nufin taimakekeniya da kuma kaunar juna, da jibantar lamarin juna, amma a isdilahi ana nufin imani da wasu akidu da suka hada akidun Shi’anci kamar riko da Ahlu-baitii (a.s), idan kuwa haka ne yaya za a yi Shi’anci ya kasance bafarise? Domin mu tattaro dukkan bayanan da suka shafi wannan al’amari ba makawa mu yi sharhi da bayanin wasu bayanai kamar haka: Na daya: Abin da Shi’anci ya kunsa gaba daya shi ne musulunci, kuma duk wani abu da ya fita daga musulunci da ya shafi akida da hukunci to Shi’anci ya barranta da shi saboda madogarar Shi’anci abubuwa hudu ne a jere: a- Littafin Allah Mai Tsarki: Shi ne abin da aka saukar da lafuza na musamman da usulubinsa kebantacce kuma aka kuma dauke shi a matsayin Kur'ani, kuma shi ne tattararrun wadannan takardu tsakanin bangwaye biyu wanda yake hannun musulmi kuma ya tsarkaka daga tawaya da jirkitawa wanda barna ba ta zo masa ta bayansa da kuma ta gabansa kuma kalmominsa mutawatirai ne kuma haruffansa sun zo bisa yakini tun lokacin Annabi mai daraja har zuwa yau wannan zamani, kuma an hada shi tun lokacin Annabi kamar yadda yake din nan, Jibril (a.s) yana karanta masa shi kowace shekara.
|