‘Yan Shi'a Na Farko



'Yan Shi'a na Farko su ne: Jundub dan Junadata, Abuzar algifari, da Ammar dan Yasir, da Salman alfarisi, da Mikdad dan Ammar dan Sa’alaba alkindi, da Huzaifa alyamani ma’abocin sirrin Annabi, da Khuzaima dan Sabit al’Ansari zusshahadatain, da Khabbab dan Arat alkhuza’i dayan wadanda suka sha azaba saboda Allah, da Sa'ad dan Malik, da Abu Sa’idul alkhuduri, da Abul Haisam dan Attihan al’Ansari, da Kais dan Sa'ad dan Ubbada al’Ansari, da Anas dan Alhardan Munbah dayan shahidai Karbala, da Abu Ayyubal Ansari, da khalid dan Zaid wanda Annabi ya nemi bakuncinsa yayin da ya shiga Madina, da Jabir dan Abdullahi al’Ansari dayan sahabban bai’ar akaba, da Hashir dan Abiwakkas almirkal wanda ya bude Jalula’, da Muhammad dan Halifa Abubakar dalibin Imam Ali (a.s) kuma dan renonsa, da Malikul Ashtar Annakha’i, da Malik dan Nuwaira wanda Khalid dan Walid ya kashe shi, da albarra’u dan Azib al’Ansari, da Ubayyu dan Ka’abu sayyidul kurr’a’u, da Ubbada bn Samit al’Ansari, da Abdullahi dan Mas’ud ma’abocin ruwan alwalar Manzo (s.a.w) kuma daya daga shugabannin masu kira’a, da Abul’aswad Addu’uli wato; Zalim dan Umair wanda ya assasa tubalin ilimin nahawu da umarnin Imam Ali (a.s), da Khalid dan Sa'id dan Abi Amir dan Umayya dan Abdusshams na biyar din wanda ya musulunta, da Usaid dan Sa’alaba al’Ansari daga mutanen Badar, da Al’aswad dan Isa dan Wahab daga mutanen Badar, da Bashir dan Mas’ud al’Ansari daga mutanen Badar kuma daga wadanda aka kashe a waki’ar yakin Harra a Madina, da kuma Sabit dan Abu Fudhalatal Ansari daga mutanen Badar, da Haris dan Nu’uman dan Umayya al’Ansari daga mutanen Badar, da Rafi’u dan Khudaij al’Ansari daga shahidan Uhud bai balaga ba, amma Manzo (s.a.w) ya ba shi izini. Da Ka’abu dan Umair dan Ubadatal Ansari daga mutanen Badar, da Sammak dan Kharasha Abu Dujanatal Ansari daga mutanen Badar, da Suhail dan Amrul Ansari daga mutanen Badar, da Atik dan Attihan daga mutanen Badar, da Sabit dan Ubaida al’Ansari daga mutanen Badar, da Sabit dan Hudaim dan Udayyil Ansari daga mutanen Badar, da Suhail dan Hanif al’Ansari daga mutanen Badar, da Abu Mas’ud Ukuba dan Amru daga mutanen Badar, da Abu Rafi’i bawan Manzo (s.a.w) wanda ya halarci dukkan yakokin Annabi (s.a.w) tare da Imam Ali (a.s), kuma daga wadanda suka yi bai’a biyu ta Akaba da ta Ridwan kuma ya yi hijira biyu zuwa Habasha tare da Ja’afar da Madina tare da musulmi, da Abu Buraida dan Dinar al’Ansari daga mutanen Badar. Da Abu Umar al’Ansari daga mutanen Badar, da Abu Katada Alharis dan Rib’i al’Ansari daga mutanen Badar, da Ukuba dan Umari dan Sa’alaba al’ansarri daga mutanen Badar, da Kurza dan Ka’abul Ansari, da Basher dan Abdulmunzir al’Ansari daya daga zababbun bai’ar Akaba, da Yazid dan Nuwaira dan Haris al’Ansari daga wadanda suka samu shaidar aljanna daga Annabi (s.a.w) da Sabit dan Abdullahil Ansari, da Jabala dan Sa’alaba al’Ansari, da Jabala dan Umair dan Aus al’Ansari, da Habib dan Badil dan Warka’ul Khuza’i, da Zaid dan Arkam al’Ansari da ya halarci yaki goma sha bakwai tare da Annabi (s.a.w), da kuma A’ayun dan Dhabi’a dan Najiya Attamimi, da Asbag dan Nabatat, da Yazid Al’aslami daga ma’abota Bai’ar Ridhwan, da Tamim bn Khuzam, da Sabit dan Dinar Abu Hamza Assumali ma’abocin addu’ar nan shahararriya, da Jundub dan Zuhair al’azdi, da Ja’ada dan Habira almahzumi, da Harisa dan Kudama attamimi, da Jubair dan Janab al’Ansari, da Habib dan Mazahir al’asadi, da Hakim dan Jabala al’abdi allaisi, da Khalid dan Abidujanata al’Ansari da Khalid dan Walid al’Ansari, da Zaid dan Suhan allaisi, da Alhajjaj dan Gariba al’ansari, da Zaid dan shurhabil al’Ansari, da Zaid dan Jibilatal tamimi, da Budail dan War’ka’ al’khuza’I, da abu Usman al’Ansari, da Mas’ud dan Malik al’asadi, da Sa’alaba abu Umratal Ansari, da Abuttufail Amir dan Wa’ila Allaisi, da Abdullahi dan Hizam al’Ansari shahidin Uhud, da Sa'ad dan Mansur assakafi, da Sa'ad dan Haris dan Samadul Ansari, da Haris dan Umar Ansari, da Sulaiman dan Surad alkhuza’I, da Shurhabil dan Murratal Hamdani, da Shabib dan Rattul Namiri, da Sahal dan Umar ma’abocin Marbad, da Suhail dan Umar dan’uwan Sahal da aka ambata a baya, da Abdrrahaman alkhuza’i, da Abdullahi dan Kharash, da Abdullahi dan Suhail al’Ansari, da Ubaidullahi dan Al’azir, da Udayyi dan Hatim atta’I, da Urwa dan Malik Al’aslami, da Ukuba dan Amiris Salami, da Umar dan Hilal Ansari, da Urwa dan Malik Al’aslami, da Ukuba dan Amir Salami, da Umar dan Hilal Al’ansari, da Umar dan Ansa dan Aunil Ansari daga ma’abota Badar, da Hindu â€کYar Abi Hala Al’asadi, da Wahabu dan Abdullahi dan Muslimi dan Junada, da Hani dan Urwa Al’muhiji, da Habira dan Nu’uman Alja’afi, da Yazid dan Kais dan Abdulllahi, da Yazid dan Hurit Al’ansari, da Ya’ala dan Umair Alnahadi, da Anas An Mudrik Alkhas’ami, da Amrul Abdi Allaisi, da Umaira Allaisi, da Alim dan Salma Attamimi, da Umair dan Haris Assalami, da Alba’u dan Alhaisami dan Jarir da Babansa Alhaisam daga jagororinn yaki a yakin da aka yi da Farisa a Zi-kar, da Aunu dan Abdullahil Azdi, da Ala’u dan Umar Ansari, da Nahshal dan Dhamratal Hanzali, da Almuhajir dan Khalid Almakhzumi, da Makhnaf dan Sulaim Al’abdi Allaisi, da Muhammad da Umair Attamimi, da Hazim dan Haabi Hazim Annajli, da Ubaid dan Attihan Al’ansari, wanda shi ne farkon wanda ya yi bai'a ga Annabi (S.A.W) a daren Akaba, da Abu Fudhalatal Ansari, da Uwais Alkarni Al’ansari, da Ziyad dan Nadir Alharis, da Aiwad dan Alad Assulami, da Ma’azu dan Afara’ul Ansari, da Abdullahi dan Sulaim Al’abdi Allaisi, da Ala’u dan Urwatul Azdi, da Alkasim dan Uslaim Ala’bdi Allaisi, da Abdullahi dan Rukayya Al’abdi Allaisi, da Munkiz dan Nu’uman Al’abdi Allaisi, da Haris dan Hassan Azzuhali, ma’abocin tutar Bakir dan Wa’il, da Bujair dan Dalja, da Ayazid dan Hujjiyya Attamimi, da Amir dan Kais Adda’i, da Rafi’ul Gadafani Al’ash’ja’i, da Salim dan Abi Ja’ad, da Ubaidillahi dan Abil Ja’ad, da Ziyad dan Abil Ja’ad, da Abbana dan Sa'id dan Asi dan Umayya dan Abudsshams daga jagororin yakoki lokacin Annabi (s.a.w), Kuma Daya Daga Sahabban Imam Ali (a.s) na musamman, da Harmala dan Al’munzir Atta’i Abu Zubaida, dukkansu dari da talatin da Uku..

Wannan kadan ke nan ko kuma misali ke nan na wasu daga Shi'a da muka kawo ba tare da wani tacewa ko zaba ba, kawai na bi littattafan ilimin Rijal ne (na sanin tarihin majazen ruwayar hadisai) ne sai na kawo wadannan daga ciki, kuma wadannan littattafai masu zuwa sun kawo maganar shi’ancinsu[1].

Bayan mun lura da wannan jama’a ta farko daga Shi'a wasu al’amura masu muhimmanci suna bayyana garemu cewa a maganarmu wannan da zamu bujuro da ita ne gaban mai karatu wayayye mai bin gaskiya da ilimi. Domin kuwa da yawa a kan samu masu karatu da idanuwansu ba sa iya wuce abin da sadarori suka kunsa. Wani lokaci kuma yakan karanta amma ba ya son ya gaskata abin da yake karantawa tare da cikar sharuddan ingancin abin da yake karantawa, kuma tare da samun nutsuwar rai ga abin da yake karantawa, sai dai wanil lokaci abin da rai da kwakwallwa suka ginu a kansa tun yarinta, ta yada yakan kusa zama tamkar wani abu daga dabi’ar da dan’Adam ya tashi a kanta ne, sai ya kasance ya kasa barin abin da ya taso a kansa na akida.

 

Bayanin â€کYan Shi'a Na Farko

Wadannan kalamai da zan kawo zasu kunshi wani bayani ne game da nau’in Shi'a na farko kamar haka:

Na farko: Wadannan Shi'a da muka ambata duk da sun kasance suna ganin al’amarin halifanci na Imam Ali (a.s) ne domin shi ne wajibi a yi masa biyayya saboda nassin shari'a gareshi, tare da wannan imanin nasu da cewa duk wanda ya wuce ya sha gabansa to ya dauki abin da ba nasa ba ne, da kuma kin da yawancinsu suka yi na kin bai’a ga halifa na farko da kuma rikonsu ga gidan Imam Ali (a.s) duk da haka ba a samu wani daya daga cikinsu ya zagi wani daga sahabbai ba, ko kuma ya yi masa wani abu ta hanyar da take ba ta halatta ba, sun kasance ne dai kawai sun dage kan imaninsu da akidarsu. Ga dukkan alamu al’amarin zage-zage ya zo ne sakamakon wasu raddodi kan wasu ayyukan da suka gabata da zamu yi nuni kan haka nan gaba- duk da haka ba su riki yin zagi ba ga hukumomi ko wata magana ta banza, domin sun san cewa hakkoki ba sa iya dawo wa ta hanayr zagi, kuma zagi ba ya daga dabi’ar gwaraza, kuma nuna wani zalunci da aka yi ko kuma wani hakki da aka kwace to wannan ba zagi ba ne, sai dai akwai wasu hanyoyi masu sauki domin kai wa ga hadafi. Kuma Imam Ali (a.s) ya kwadaitar da mabiyansa kan wannan tafarki mai sauki kamar misalin abin da Nasar dan Muzahim ya ruwaito yana cewa: Imam Ali (a.s) ya wuce wasu sahabbansa da suke tare da shi a cikin rundunar yaki a Siffain sai ya ji suna zagin Mu’awiya da sahabansa, sai ya ce da dan Udayyi da kuma Umar dan Al’hamki da wasu mutane: Ina ki muku ku kasance masu la’anta masu zagi, kuna masu zagi kuma masu barranta, amma dai da zaku siffanta ayyukansu munana ku ce; suna yin kaza da kaza, kuma sun aikata kaza da kaza da ya fi kyau, kuma ya fi yanke uzuri, da maimakon la’anar da kuke yi musu da kuma baranta daga garesu zaku ce: "Ya ubangjiji ka kare jininmu da nasu ka gyara tsakaninmu da tsakaninsu, ka shiryar da su daga batansu har sai wanda ya jahilci gaskiya ya gane ta daga cikinsu, kuma wanda yake kan bata da kiyayya ya tsorata ya bari, da wannan ya fi soyuwa wajena kuma ya fi muku alheri. Sai suka ce: Ya Amirul muminin mun karbi wa’azinka kuma mun tarbiyyantu da ladabinka[2].

Wannan abu ya nuna mana cewa hanyar zagi hanya ce kaskantacciya ba ta da karimci, sannan kuma tafiyar da karfi ne a banza da za a iya amfani da shi da kuma juya shi domin wani aiki mai kyau, hada da cewa zagin yana kawo muzantawa ga abubuwan da mai zagin yake tsarkakewa, don haka ne ma malamai suka harmta zagin gumaka idan ya kai ga zagin Allah suna masu amfana daga wannan fadin na Allah madaukaki: "Kada ku zagi wadanda suke kiran wasu sabanin Allah sai su zagi Allah bisa gaba ba tare da ilimi ba". An’am: 108.

Don haka ne ma aka umarci Shi'a da tsarkake harsunansu daga zgin domin wannan ya fi nisantarwa ga mummuna kuma don haka ne ma muka ga da yawa daga masu talifofi masu ilimi suna karfafa siffantuwar Shi'a na farko da wannan siffa ta gari tare da cewa suna tabbatar da akidarsu ta fifita Imam Ali (a.s) a kan waninsa, daga cikinsu akwai:

a- Dakta Ahmad Amin:

Yana cewa: Irin wannan matsakaita din su ne wadanda suke ganin Abubakar da Umar da Usman da dukkan wadanda suka goya musu baya sun yi kuskure domin sun yarda da halifofi ne tare da cewa sun san fifikon Ali (a.s) da kuma cewa ya fi su[3].



1 2 3 next