Ra'ayoyin Jagoranci



Me kafa tsarin zaman jama’a da ci gaban gudanarsa yake bukata?. Da farko yana bukatar wata manufa ko akida (aidiyolojiyya) mai shiryarwa wacce daga gare ta ne wancan tsarin  yake bubbugowa kuma ita take zayyana shi. Na biyu yana bukatar karfin zartarwa mai iya kutsawa cikin wahalhalu da matsaloli da kangiya domin tabbatar da manufar tsarin. Mun san cewa aidiyolojiyyar (ko kuma akida) Imamai ita ce musulunci. Shi kuwa musulunci  sako ne madawwami ga dan Adam, watau sakon da ke tattare da sinadarin wanzuwa da tabbatarsa.[7] 

Idan muka lura da wadannan mas’aloli, cikin sauki za mu iya fahimtar manhajar Imamai na Ahlulbaiti kuma wasiyyan Annabin rahama (s.a.w.a). Wannan manhajar tana da sassa biyu malizimta juna: na farkon yana dangantaka  da akida, na biyun kuma yana da alaka da samar da karfin zartarwa da zamantakewa. A sashen farko, Imaman suna fuskantarda kokarinsu da himomminsu ne wajen yada manufofin sako da kafa su, da tono 11  duk wani kaucewa gaskiya da karkata wadanda masu bin son rai suke sabbabawa; da bayyana ra’ayin musulunci kan sababbin mas’aloli da raya alamomi wadanda suka rushe, sakamakon karo da amfanin ma’abota iko da masu fada a ji; da faiyace abin da ya boyu wa hankula na daga littafin Allah mai girma da sunnar Ma’aiki. Ana iya takaita zance kan nauyin sashen farko da cewa kare rayayyen sakon musulunci ne mai ginuwa, tsawon zamani.

A sashen na biyu kuwa gwargwadon abin da yanayin siyasa da zamantakewar al’ummar musulunci suke hukuntawa, suna kokarin samar da shimfida da ake bukata wajen karbar ragamar shugabancin al’umma da kansu a kusa, ko kuma shimfida domin imamin da zai ci  gaba da tafiyar tasu a nan gaba ya kuma karbi shugabanci bayan zango mai tsawo.

Wannan a takaice shi ne manufar rayuwar tsarkakan Imamai, kuma wadannan su ne tsarin manufofinsu a game, saboda su suka rayu kuma dominsu suka yi shahada. Idan tarihin rayuwar Imamai wanda ya zo mana ba ya tabbatar da ra’ayin da muka tafi a kai, to akidarmu kan Imamai ta isa ta sauwara mana rayuwarsu ta wannan fuskar kadai. Mene ne zatonka idan tarihi yana ba da shaida da take gamsar da ko wane mai bincike cewa rayuwar Imaman Ahlulbaiti tana kan wannan mafuskantar?.


[1] Duba biharul anwar J. 47 / sh. 172, kamusi Rijali J /sh 509.

[2] Mansur ya mutu ya bar tsabar kudi dirhami milyan dari shida da dinari miliyan goma sha hudu a cikin taskarsa  Dubi littafin Asrul-Izdihar  sh.60-70.

[3] Philpil Hitti: History of the Arabs (Tarihin Larabawa)

[4] Petroshivisky: Musulunci a Iran.

[5] Suratul hadid : aya 25.

[6] Nahjul balaga /huduba ta 16, yayin da aka masa mubayaa  a madina.

[7] Wani daga cikin wadannan  sifofi shine kasancewar tsarin shari’ar musulunci ya kunshi  hukunce-hukunce tabbatattu da kuma masu canjawa watau wadanda suke dogaro da yanayin al’umma da lokaci  da wuri. Misali: ka’idar  “ Mafi saukin masu cutarwa” ( Ahaffu dara’raini)



back 1 2 3 4