Ma'ajin Sirri da Wakilci



  Yahya ibn Ummi Dawil, “Kofarâ€‌ Imam Sajjad an kashe shi, mummunan kisa.[5]  Jabir ibn Yazid Alju’fi kofar Imam Bakir kuwa dole ta sa ya sa rigar hauka kuma wannan labarin ya watsu ya zama dalilin tsirarsa daga kisan da halifa ya riga da ya bayar da umurninsa â€کyan kwanaki kadan kafin yaduwar labarin haukacewarsa. Muhammad ibn Sinan kuwa â€کkofar’ Imam Sadik (a.s) korarsa  Imam ya yi, kora ta zahiri duk cewa Imam ya bayyana yardarsa gare shi da yabonsa a wasu wuraren. Ba don komai aka yi masa haka ba sai domin shigarsa irin wadannan hadura. kamar yanda sanarwar Imam  barrantarsa daga wani sananne  mashahurin marawaici wanda kuwa ya rabauta da sanarwar yarda daga Imam, Sau da dama yana ishara bisa ra’ayi mai karfi cewa, dabara ce ta tsare-tsare.

  Irin wannan makoma tana fuskantar “wakiliâ€‌ shi ma. “Wakiliâ€‌ shi ne mai nauyin tara dukiyoyin da suke da alaka da Imam da kuma rarraba su. Shi ma ya san sirrori masu yawa, alal akalla, sunayen masu bayarwa da na masu karba. Wadannan bayanan, makiya Imam basu raina su. Mafificin hujja kan haka shi ne makomar Mu’alla ibn Kunais, wakilin Imam Sadik (a.s) a Madina da kalmomin Imam game da Mufaddal ibn Umar, wakilinsa a kufa, wadanda ya fade su bisa takiyya.

  Lakabin nan guda uku: kofa da wakili da ma’abocin sirri, wadanda muke samun cewa masu su wadansu wanyan mutane ne daga mazajen shi’a 46 suna bayar da haske kan halin da shi’a ke ciki da alakarsu da Imam da kuma harakar tsare-tsare ta shi’a.

  Da wannan dubi muna iya fahimtar cewa shi’a su ne jama’ar mutane masu sajewa da junansu, jama’a mai manufa, mai himma, mai matattara a kan wani ginshiki mai tsarki wanda yake watsa haske kan mataimakansa ta hanyar umurce-umurce da kuma shiryarwarsa. Su kuma mataimakan suna da alaka da shi, suna kawo masa bayanai, suna kame motsin rai suna kuma fin kafin zuciyarsu albarkacin wasice-wasicensa na hikima. Suna kuma lizimtar salon sirri wajen aiki, kamar kiyaye sirrori da karancin magana da rashin shiga mutane da aikace –aikacen jama’a da kuma nisantar al’amuran kawo juyi.


[1]  Rijalul kashshi  380.

[2] Manakib  Ibn  Shahrashub.  4:248

[3] Alkafi  2 : 219.

[4] Wannan lafazi ana ciro shi ne daga wani nassin Imam (a.s).

[5] An sare kafarsa da ransa, sannan aka kashe shi- Rijal Kashshi.



back 1 2