Shi'anci Da Shi'a



Jama'arja'afariyya imamiyya

1-Wannan jama'ar ita ce aka fi sani da Shi'aimamiyya ja'afariyya, jama'a ce mai yawa a wannan zamani namu, kuma ana kaddara adadinisu da kusan kwata na yawan al'ummar musulmi gaba daya, kuma asalinsu a tarihi ya taso ne daga ranar saukar fadin Allah madaukaki a surar bayyina: wadannan da suka yi imani kuma da aiki na gari, wadannan su ne mafifitan al'umma[3].

Sai Manzo (S.A.W) ya dora hannunsa a kan kafadar Ali dan Abi Dalib (A.S) kuma sahabbai suna wajen, ya ce: Ya Ali kai da shi'arka ku ne mafifitan al'umma. (Ana iya duba misali: a tafirin dabari –jami'ul bayan- da durrul Mansur na suyudi bashafi'e, da tafsirul ma'ani na Alusi bagdadibashafi'e game da tafsirin wannan aya).

Daga nan ne aka kira wannan al'umma da Shi'awacce ake danganta ta zuwa ga imam Ja'afar assadik (A.S) saboda suna bin fikihunsa.

2-Ana samun wannan jama'a da yawa a kasashekamar Iran da Irak, da Pakistan, da Afganistan, da Indiya, kuma sun yadu da yawa a kasashen Kogin farisa, da Turkiyya, da Siriya, da Labanon, da Rasha da kasashen da suka rabe daga gareta. Kuma suna yaduwa a kasashen turai kamar Ingila, da Jamane, da Paransa, da Amurka, da Yankin Afrika, da kasashen Asiya ta gabas, suna da masallatai da cibiyoyin ilimi da wayewa ta zamantakewar al'umma.

3-Su jama'a ce daga jinsina daban-daban daluggogi, da launuka, kuma suna rayuwa tare da 'yan'uwansu sauran musulmi daga sauran jama'u na sauran mazhabobi cikin aminci da soyayya, da taimakekeniya a dukkan fagagen rayuwa da gaskiya da ikhlasi, dogaro da fadin ubangiji madaukaki: Hakika muminai 'yan'uwan juna ne[4].

Da fadinsa: Ku yi taimakekeniya a kan biyayya da takawa[5]. Da kuma riko da fadinsa mai girma (S.A.W): Musulmi hannu daya ne a kan waninsu[6]. Da fadinsa: Muminai kamar jiki daya ne[7].

4-Suna da ayyuka muhimmai da suka yi a tarihimasu girma na kariya ga musulunci, da kuma al'ummar musulmi, kamar yadda sun yi dauloli da hukumomi da suka yi hidima ga ci gaban musulunci, da kuma malamai masu ilimi da suka bayar da gudummuwa wajen wadatar da littattafan musulunci da wallafe-wallafe masu yawa da suka kai daruruwan dubunnai kanana da manya a fagagen tafsirin Kur'ani, da hadisi, da akida, da fikihu, da usul, da akhlak, da rijal, da palsafa, da wa'azi, da siyasa, da zamantakewa, da lugga, da magani, da adabi, da pizik, da kimiyya, da lissafi, da ilimin falaki, da sauran ilimomi na rayuwa. Kuma suna da muhimmiyar rawar da suka taka ta asasi wajen assasa ilimomi daban-daban: (A duba, littattafan: Ta'asisus Shi'a li ulumil Islam, da zari'a ila tasanifis Shi'a na Aga buzurg mai mujalladi 29, da kashaful zunun na Afande, da mu'ujamul mu'allfin na Kahala, da A'ayanus Shi'ana sayyid muhsir amin amuli da sauransu).

5-Sun yi imani da Allah daya makadaici wanda bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma wani bai kasance tamka da tsara gareshi ba. Suna korewa Allah jiki da jiha, da wuri, da zamani, da canjawa, da motsi, da hawa da sauka, da dukkan abin da bai dace da ubangiji ba madaukaki.

Kuma suna yin imani da cewa babu wani abin bautasai shi, kuma hukunci da shar'antawa duka suna hannunsa ne shi kadai ba tare da waninsa ba, kuma shirka da dukkan nau'o'inta karama ce ko babba, ta boye ko ta sarari duka zalunci ne mai girma kuma zunubi ne da ba a yafewa.

Kuma dukkan wannan sun dogara ne da hankali maihujja da aka karfafe ta da littafin Allah mai girma, da Sunna madaukakiya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next