Musulmin DuniyaWannan ra'ayin yana ganin saba masa a tunani da akida yana nufin batan daya bangaren ne, don haka yana ganin dole ne fahimtarsa ta kasance kowa ya yi riko da ita, idan ba haka ba kuwa to sauran bangarorin ba musulmi ba ne. Sakamakon wannan ra'ayi yana dauke da wannan fikira da akida, don haka ne ya kasance a kullum ba shi da wani kira sai neman kashe musulmi. Zaka ji mai dakon wannan tunanin bai sanya komai gaba ba sai kiran rarraba da zubar da jinni, zaka ji shi a radio da talabijin yana maimaitawa kamar Aku. Yana mai maimaitawa cewa ya kamata a dauki mataki kan masu tunani kaza, kai ya kamata a kashe masu kaza, masu kaza kafirai ne, babu wasu kalmomi na rahama a cikin wannan tunani ko kwarzane. Abin takaici yadda wannan ra'ayin ya rudi wasu masu da'awar son gidan Annabi (s.a.w) suna masu gafala ba su san abin da yakan kai ya komo ba, sai suka yi dakon irin wannan tunanin na rarrabar musulmi kyauta ba su sani ba. Babu wani aiki na cutar da musulunci da musulmi a yau irin gaba da jefa kiyayya tsakanin al'ummar musulmi ko jefa gabar wata jama'a saboda kawai tana da wata fahimta, balle a ce wannan jama'ar musulma ce. A daidai lokacin da ya kamata hatta da kirista da masu bautar gumaka mu kira su, mu ja su a jiki, domin mu sanar da su sakon Manzon Allah (s.a.w), sai ga wasu babu wani abu da suka sanya gaba sai rura wutar gaba tsakanin musulmi da gaba da koyarwar gidan Manzon Allah (s.a.w), suna masu tayar da jijiyar wuya sai sun rarraba musulmi. A yanzu ba abin mamaki ba ne kirista ta yi shekaru 35 a cikin birnin Kano amma ba ta taba sanin matsayin musulmi game da Annabi Isa (a.s) ba?! A yanzu muna ganin da Manzon Allah (s.a.w) ya kasance haka zamu samu labarin ma wannan rahamar sakon nasa ko da a rubuce a tarihi? Sannan muna haka muke tsammanin samun tsira! A yanzu jahiltar addinin musulunci da hadafinsa da shi kansa musulmi yake a kai laifin waye?! Sai aka bar fagen addini ga kowane mai magana, sai malamai suka yarda suka zubar da kimar matsayinsu, sai ka ga hadisai ana wasa da su. Kwanan nan ne na ga wani yana fassara hadisin a yi aure a hayayyafa yadda ya ga dama, babu wata diraya, ba tare da ya san yana da alaka da zamani, da wuri, da yanayi ba. Shi dai yana batun a hayayyafa da yawa, a watsa 'ya'yan, titi ya yi musu tarbiyya, ban sani ba ko yana ganin Annabi zai yi alfahari da tarbiyyar titi. Sai kowane mutum ya zama malami ko da bai kware da karatu a fagen ilimin addini ba, matukar ya iya buda baki ya yi magana to yana da mahanga a addini. Babu wani fagen ilimi kamar likitanci, ko kimiyya, ko rayuwar halittu da ake yi masa katsalandan ko cin zarafi irin fagen addini. Abin takaici hatta da wanda ya rayu a titi yana rigaita yana da mahanga a addini saboda reni ga addini. Sannan karancin wayewa da fadada tunani daga malaman kansu ta sanya ba su da ta cewa; a fagage masu yawa, sai suka wakilta wannan a hannun masu tunanin yamma domin su cike wadannan fagage. Yaya ake tsammanin Musuluncin da ake nuna wa duniya a yau cikin ayyukan ta’addanci da sunan musulunci zai samu karbuwa a yammacin duniya. Musulunci bai taba yarda ka kame wani ko kashe shi babu dalili na shari'a ba, kuma wannan ba ya hannun kowa sai hukuma, ita ma hukuma dole ne ya kasance bisa adalcin dokokinta. Sannan duk wanda wata kasa ta ba shi izini domin ya shiga cikinta to yana da kariyar da babu wani mai hakkin taba shi ko mai kuwa munanan ayyukansa, kamar yadda duk wanda aka ba shi izini don shiga wata kasa, musulunci bai yadda ya saba wa alkawarin da ya dauka na bin dokar wannan kasa ba, balle kuma ya kai ga cin mutunci ko zubar da jinin jama'arta. Don haka ne musulunci ya barranta daga dukkan munanan ayyukan da ake yi da sunansa ana bata masa suna!. Musulunci ya yi mana tarbiyyar kira da kalma mai taushi ko da ga mafi kafircin mutane ne: "… Ku gaya masa magana mai taushi…" (Taha: 44), ta yadda hatta da Fir'aunan da ya yi da'awar Ubangijintaka amma sai Allah ya yi umarni ga annabi Musa (a.s) da ya gaya masa magana mai taushi, balle kuma mutanen da ba su ji, ba su gani ba. Ba mu ce sauran addinai ba su da mabiya masu ta'addanci da sunan addinin ko da wata manufa ba, sai dai mu musulumi abin takaici ne a cikinmu a samu masu yi, kuma mafi muni a jingina wannan fahimta da musulunci alhalin abin da masu wannan tunanin suke yi ya yi hannun riga da koyarwar musulunci a fili.
|