Musulmin Duniya



 

Da SunanSa Madaukaki

Amincin Allah ya tabbata ga Annabi da Alayensa

 

Idan muka dauki musulmi muka dora su a sikelin rahamar ubangiji kan talikai sai mu ga sun yi hannun riga da wannan! Sai wani bangare tun farkon tarihin wannan addini suka riki gaba da gidan Manzon Allah (s.a.w), kuma guggubin wannan koyarwar ta sanya kyamar yabo ko nuna matsayin Annabi (s.a.w), kuma a yau ta haramta tawassuli da shi ko yin bukin murnar haihuwarsa.

Mafi munin ayyukan wannan tunani da yake yaduwa a duniya cikin wadannan shekaru 30 na karshe shi ne kokarin rarraba kawukan musulmi. Idan ya ga dan Sunna yana riko da mazhabar da ba tasa ba, yana tunani da ya saba wa nasa musamman idan yana riko da darikun waliyyai ne, to sai ya kira shi mushriki. Idan ya ga dan Shi'a sai ya kira shi kafiri, ko ya jingina masa kin sahabbai.

Su wadannan mutane su ba Sunna ba, su kuma ba Shi'a ba, amma sun fi kowa da'awar su suke riko da Sunna. Wallahi da sun yi riko da Sunna da sun riki wasiyyar Manzon Allah (s.a.w) ga al'ummarsa ta yin riko da littafin Allah da Ahlin gidansa kamar yadda ya zo a hadisai mutawatirai gun Sunna da Shi'a duka. (Koma wa; Muslim, Mustadark, da Masnad Ahmad d.s.s).

Wannan akida mai kiyayya da koyarwar wasiyyar Annabi (s.a.w) babu wani sakamako da ya yi wa Annabi (s.a.w) sai bata surar sakonsa a idanun duniya, har ma ya kasance idan ka ji sunan ta'addanci a yau to tunanin yamma yana kallon musulunci ne. Ba don komai ba, sai domin wannan tunanin ba shi da wani aiki sai kira ga rarraba ko kashe bayin Allah, ya sanya bamabamai a masallatai, an sanya wa kananan yara da mata, an sanya a makarantu, babu wani mutum da ya tsira, babu musulmi balle waninsa.

Don haka ne muke ganin wautar masu jingina ta'addanci ga musulunci, alhalin suna ganin wannan Akidar hatta da Manzon Allah da ya zo mana da sako yana ganinsa kamar ambulan ne na wasika. Don haka masu kiran musulunci da ta'addanci a yammancin duniya ba su yi masa adalci ba, domin ko musulmi bai tsira daga wannan ta'addancin ba! Sannan kuma idan ma'abota wasu addinai suka yi ta'addanci don me ba ma ganin an jingina shi ga addininsu. Ta'addanci fa yana nan ta'addanci, ko daga musulmi a maiduguri -da ya harbe wanda bai ji ba bai gani ba kamar yadda Jazira suka nuna shi, ko kuma wanda ya kashe dan sanda mai bayar da kariya ga al'ummar kasa- ko daga Kirista da yake garin Jos! duk sunansa Ta'addanci.



1 2 3 4 5 next