Sayyid Khamna'i



Wasu bayanai game da rayuwar sayyid khamna'i

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

TAMBAYA: Sheikh Muhammadi Golgaygani, kana daga cikin mafiya kusanci da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, idan har ka yarda zan so in yi maka wasu tambayoyi kansa. Da farko dai, zan fara tambayarka ne dangane da yanayin lafiyar mai girma Jagoran. Kamar yadda ka sani cikin 'yan kwanakin nan kafafen watsa labaran kasashen waje suna ta maganganu kan lafiyar Jagora, musamman ma cikin wannan wata da muke ciki. Don haka muna son ka yi mana bayani kan yanayin lafiyar mai girma Jagoranmu?

AMSA:Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai, Ina gode maka da wannan tambaya da ka min, a yayin amsa wannan tambaya taka, zan so in bayyana cewa daya daga cikin tarko abokan gaba, shi ne kaddamar da yaki na kwalkwalwa don gamawa da abokan hamayyansu. Bisa la'akari da cewa a yau din nan babban jigon Juyin Juya Halin Musulunci shi ne mai girma Jagora, kuma kamar yadda ka sani ne bai canja ba daga irin matsayar da Marigayi Imam (r.a) ya dauka kuma yake kai ba, a hakikanin gaskiya ma dai ya yi tsayin daka wajen kare wannan tafarki na Imam, don haka makiya ta hanyoyi daban-daban sun yi ta kokarin bayyana sabanin hakan amma dai ba su yi nasara ba. Don haka ne makiyan yanzu kuma suka koma wajen yada irin wadannan jita-jita da kararraki don haifar da damuwa da karyewar zuciyar al'umma da kuma masoyansa.

Shakka babu, a dabi'ance 'yan Adam sukan kamu da ciwo nan da can, to amma ina son in sanar da kai cewa lalle Jagora kan yana nan cikin koshin lafiya. Ina ga watakila zai ba ka mamaki idan na sanar da kai cewa ya kan je wasan hawa dutse sama da sau guda a kowani mako, kuma a kowani zuwa ya kan dau awoyi a can, kuma ma da dama daga cikin matasa ma ba za su iya karawa da mai girma Jagora ba a wannan bangaren.

TAMBAYA:Shin akwai wani lokaci na musamman ne da mai girma Jagoran ya ke zuwa hawa dutsen?

AMSA:Hakan yana da alaka ne da yanayin da ake ciki, misali a lokacin sanyi lokacin da kankara take zubowa akan duwatsu, to mai girma din ba ya tafiya hawa dutse a wannan yanayi, don haka ba zai yiyu a fayyaye wani lokaci na musamman ba, kamar yadda kuma babu wani waje na musamman da yake zuwa. Anan yana da kyau a gane cewa Mai girma Jagora yana da wata jumla mai kyau gaske dangane da wasannin motsa jiki, ina babu laifi idan mai karatu ya san cewa Jagora yana daga cikin mutanen da suka fi kowa kwadaitar da al'umma wasannin motsa jiki, ya kasance ya kan ce:"Wasannin motsa jiki yana da kyau ga matasa kana kuma wajibi ne ga tsoffin mutane".

TAMBAYA:Mun sami labarin cewa a wasu lokuta ma ya kan yi sallar Asubahi a daya daga cikin duwatsun da suka bayan birnin Tehran?

AMSA:Na'am, a wasu lokutan ya kan yi sallar Asubahi a kan duwatsun, a wasu lokuta ma ya kan haura can kololuwa.

TAMBAYA:Shin ka taba samun damar raka shi?

AMSA:E a wasu lokuta. Amma kasan ni tsoho ne, ka san ba zan iya tafiya da shi kowani lokaci ba. Amma duk da haka dai na riga da na san tsare-tsaren ayyukansa. Ina son in sanar da kai cewa da a ce ba shi da koshin lafiya da ba zai iya yin irin wannan wasannin motsa jiki ba, musamman ma dai hawan dutse, wanda kamar yadda ka sani ne, wasa ne mai tsananin wahala. To amma Alhamdu Lillahi yana cikin koshin lafiya da walwala.

TAMBAYA:A dali'ance a duk lokacin da ya je hawa dutsen sauran mutane da kuma wadanda su ma suka zo wajen don hawa dutsen za su ganshi, shin ka taba ganin irin wannan ganawa da Jagoran wacce ba a riga da an tsara ta ba?



1 2 3 next