Isma Kyauta CeShin Isma Kyauta Ce Daga Allah Ko Kuwa Kokarin Mutum Ne? An yi bayanin Isma da cewa; ita ce martaba ta koli ta jin tsoron Allah, ko kuma shi ne ganin girman Allah da daukakarsa, ko kuma da ma'anar sanin ilimi cikakke da sakamakon sabo, ko kuwa ludufin Allah (s.w.t) ne wanda yake kusantar da bawa zuwa ga bautarsa. Muhimmin lamari a nan shi ne me ma'abota ilimin sanin Allah suke ganin isma; shin daga Allah take, ko kuwa kokarin dan Adam ne? A nan masu ilimin sanin Allah suke ganin cewa; daga Allah ne take, kuma shi ne yake ba bawansa da ya san zai kiyaye amanarsa wannan baiwa. Sharhu Aka’idus Saduk: 61. Wannan kuwa yana nuna mana ke nan asalinta kyauta ce daga Allah, sai dai bawansa Allah yana iya yin amfani da ita don kiyaye umarnin Allah, kamar yadda yana da zabin kin kiyayewa, sai dai Allah yana bayar da ita ga wanda ya so, kuma ya san ba zai saba masa ba. Wannan kuwa yana nuna mana cewa a fili yake cewa; isma ba ta kawar da zabi ga dan Adam. Allah madaukaki ya halicci ma'asumai daga tabon haske, sannan sai ya shirya musu hankali da ruhi mai karfi, wanda da su ne zasu iya sanin abin da yake sirrin samammu, kuma ya yi musu ludufin karkata da sanin halittun sama da kasa, da badinin samammu, don haka sai rayukansu suka kasance karkashin ikon hankulansu. Allawami’ul Ilahiyya: 169. Sannan muna ganin karfafar wannan lamarin a cikin shari'a yayin da Allah ya yi nuni da cewa; ya tsarkake Ahlul Baiti (a.s) Ahzab: 33, kamar yadda ya nuna yadda ya kebanci wasu annabawa (a.s), Almizan: j 16, shafi: 45-48. Sai dai wasu mutane suna ganin cewa; Idan dai Allah ya ba wa zababbun bayinsa isma ne, to ashe ke nan ba su cancanci yabo a kanta ba? kuma ba ta kasance abin alfahari da kamala garesu ba? Idan dai isma ta kasance tana hana zababbun bayi yin sabo a matsayinta na kyautar Allah, to ashe ke nan ba zasu iya sabo ba koda kuwa sun so, kuma ke nan ba su cancanci yabo ko lada ba don sun bar sabo? A nan muna iya cewa: Isma ba a bayar da ita sai ga mutumin da rayinsa ta kasance ta tsarkaka, kuma tana iya karbar wannan amanar ta kiyaye da ita, don haka ashe ke nan mai isma yana cancantar alfahari, kuma kamala ce gareshi. Kuma wannan tsarkakar ruhin da mai isma yake cancantar wannan baiwar ta Allah da ita, tana iya kasancewa kala biyu: Imma ta hanyar gado; kamar yadda 'ya'yan annabawa (a.s) suke gadon kamalar badini da ta zahiri daga iyayensu, domin a ilmance, da ruwayance ya tabbata cewa; kamalar iyaye tana da tasiri ga 'ya'yansu, don haka ne ma aka karfafi aure da na gari, don haka sai ka ga dan rago, ya taso rago, dan sadauki, ta taso sadauki, mai kaifin kwakwalwa da mai dadaddiyar basira, sai ka ga 'ya'yansu sun yo su. Don haka muka ga Allah madaukaki yana yabon 'ya'yan annabawa (a.s) da wasiyyansu yana mai kiran su zuriya ce sashensu daga sashe. Aali Imaran: 33. Sai dai wannan ba shi kadai ba ne; domin yana bukatar tarbiyyantarwa, da koyarwa, da kuma halittar Allah da hikimarsa ga 'ya'yan annabawa da salihai na gari, don haka rayuwa a irin wadannan salihan gidaje, da kuma al'umma saliha, da abokai salihai, yana iya sanya tasowa cikin tarbiyya ta gari, sannan kuma sai ludufin Allah da kyautarsa da yake ba wa wanda ya so.
|