Karya da Tsoro gun Yara



Ana cewa: Sakamakon budewar idanuwa da yaro yake samu lokacin da yake fara girma; idan yaro ya kai wata shida yakan fara tsoro, idan ya kai shekara daya yakan fara tsoron dabbobi kamar mage da bera, a shekara ta biyu kuwa yakan ji tsoron komai kamar kare, da mota, da sauransu.

Sau da yawa yaro yakan fara jin tsoron wani abu a sakamakon ya ga iyaye suna jin tsoronsa, yakan ji tsoron abin da ya saba wa dabi'ar rayuwa da aka saba da ita kamar tsawa, ko wani abu da a kan shuna masa shi, haka nan yakan ji tsoron kadaituwa, ko ya gigita saboda ganin fadan manyansa kamar iyaye.

Bai kamata ba a ba wa yara tsoro sai abin da aka san tabbas cutarwa ne garesu, irin wadannan abubuwa sun hada da nisantar rijiya, ko wuta, ko wani abu da cinsa yakan cutar da su, kuma abin da ya fi shi ne; nisanta su daga gare shi, ba kawai nisantar da shi daga gare su ba.

Da zaka ga yaronka ya taso da tsoro maras dalili to ya kamata ne kasan mene ne mafarinsa don kasan yadda za a yi maganinsa, misali idan ya taso matsoraci saboda miyagun tatsuniyoyi na ban tsoro da yake ji ne, to sai a rika ba shi labari da kissoshin jarumtaka da sadaukarwa har ya yi masa tasiri, amma tare da kiyayewar cewa abin da su jaruman suka yi abu ne na alheri da bai saba wa koyarwar musulunci ba. Sannan yana da kyau iyaye su saba wa yaro da iya kwana shi kadai a dakinsa domin ya saba da zama da kafafunsa a abubuwa da dama kamar jarumtaka.

Tsoratarwa da firgitarwa a tarbiyyar yaro tana bin sawun sauran abubuwa ne marasa kyau a tarbiyyar yara kamar zagi, ko duka. Abubuwa ne da ba su da amfani sai dai a lalurar haka, bisa shawara ko umarnin masana yadda ake tarbiyyar yara, ko kuma da yakini ko zato mai karfi na cewa zai kasance hanyar warwarar matsalar wani abu da yake yi na rashin tarbiyya.

Hafiz Muhammad Sa'id

www.hikima.org

hfazah@yahoo.com

Sunday, November 15, 2009


[1] Tuhaful Ukul, Ibn Shu'uba Alharrani, Shafi: 483.

[2] Mujallar Mojtamae, Adadi na 2, shekarar farko, shawwala; 1430 H, 2009 M.

 



back 1 2 3