Hanyoyin Tarbiyya



Na biyar: Nisantar kalmomin banza da gulmar wasu da duk abin da bai dace ba a gaban yaro, da dukkan wani abu mummuna, domin shi ma ya yi koyi da na gaba. Abubuwan da aka hana munana yin su a gaban yaro yana dada munana su, domin yana nufin bata asasin ginin al’umma wato Yara.

Na shida: Yi wa ‘yayanka addu’a kullum da alherin Duniya da na Lahira, wannan ya zama abin da ba zaka taba mantawa da shi ba, koda kuwa ka manta da yi wa kanka addu’o'i to kuskure ne babba ka manta da yi wa yaranka.

Na bakwai: Shawartar yaro kan wasu abubuwa kamar abin da ya shafi rayuwar gida da zai iya bayar da nasa ra'ayi, ko inda zaku je ziyara a gidajen 'yan'uwa, ko wurin wasannin yara.

Wata rana da watan Azumi wani daga dalibanmu na bangaren Hausa a Jami’ar Azad da take birnin Tehran ya gayyace mu gidansa shan ruwa sai na ji yana sharwartar ‘yarsa wane kallo ne ya kamata ya sanya mana? Ita kuwa sai ta mayar wa Uban da cewa: Zabi yana hannunmu duk wanda muke so. Kafin nan shi da dansa da suka zo daukarmu a mota sai yakan ce da shi dan da yake tuka mu cewa: Ai wannan abokina ne kuma dana.

Na takwas: Yana da muhimmanci a rika gode wa yaro duk sa’adda ya yi wani abu na kirki, da yabonsa kan haka don a kara masa himma a kan abubuwan da yake yi na alheri.

Godiya ga wanda ya kyautata wani abu ne da yake kara masa himma yake karfafa shi, kuma yana nuna masa irin kaunar da mai godiya yake yi masa, sannan yana faranta masa rai. Sai dai godiya iri-iri ce, wani lokaci da baki za a gode, wani lokaci kuma godiyar aiki ce. Dukkaninsu ana bukatarsu; sai a yi masa godiya da harshe idan ya kyautata, sannan kuma wani lokaci a biya masa wasu bukatu nasa da suke damunsa, ta yadda zai fahimci cewa; kirkinsa ne ya sanya ake yi masa wannan alherin.

Na tara: Nuna wa yaro kuskure kan abin da ya yi na kuskure, da nuna masa cewa; zai iya kai wa ga wani abu da zai cuce shi a Duniya ko a Lahira ko a duka gida biyu. Kurakuran da yara suke yi kamar na manya ne ta fuskacin cutuwa, sau da yawa wani kan yi kuskuren da har ya mutu yana nadamarsa, wani kuwa yakan yi kuskuren da hatta da a lahira sai ya kasance masa azaba. Don haka nuna wa manyan gobe irin wannan darussa yana da muhimmanci matuka.

Na goma: Hanyar kwadaitawa ta fi yawa a kan hanyar tsoratawa, wato a fi gaya masa Allah zai ba shi kaza a Lahira in yana biyayya ga iyaye ko wani aiki na alheri maimakon a rika cewa: Ai in ka mutu, mu binne ka a kasa, kuma kunama, da maciji, da mala’ika mai sandar wuta, su kama ka, su cije ka.

Irin wannan ya zama kadan ne; domin yana iya sanya masa tsoron komai, da sukewa daga rayuwa, da kashe karfin zuciya, da sanya shi gajiya wurin aikata kyakkyawa, ko ya sa masa kosawa daga jin nasihar, idan tsoro ya yi yawa yana iya hana shi sukuni a rayuwa.

Muhimman Bayanai

Yaro yana daidai da farar takarda ce wacce duk wata tarbiyya da aka ba shi, ita ce takan yi masa tasiri a rayuwarsa. Kuma yaro yana dauke da yiwuwar ya zama kamilin mutum wanda kyakkyawar tarbiyya ce zata iya daidaita shi, ko kuma ya samu mummunar tarbiyya mai rushe wannan karfin kasancewa salihi da yake dauke da shi. A nan zan so rufe wannan littafin dan karami a girma, amma babba a muhimmanci da cewa:



back 1 2 3 4 5 next