Hanyoyin TarbiyyaBai kamata ba tarbiyyar yara ta zama an gina ta bisa tsorotarwa, da fadin karya, ko yaudara, ko tsanantawa, da sauran hanyoyin da malaman tarbiyyar ba su aminta da su ba. Yana da kyau a dora tarbiyya bisa sanin Allah, sauran hanyoyi da malaman tarbiyya suka yi nuni da su, kamar kyautatawa, da kauna, da tausasawa. Sannan kuma ya kasance ana cakuda abubuwa biyu ne: sai a cakuda nuna kauna da kuma murzawa, da lallashi da horo mai dacewa da yanayinsa, a cakuda masa yin afuwa da yi masa gargadi. Tarbiyyar yara tana farawa tun daga zaba masa uwa ne, ruwayoyi masu yawa sun zo suna masu nuni da wannan muhimmin lamarin kamar haka: Wani mutum ya zo wajen Imam Hasan (a.s) domin ya ba shi shawara game da mijin da zai zaba wa ‘yarsa. Sai Imam Hasan (a.s) ya ce: “Ka aura mata mutum mai tsoron Allah, domin shi idan ya so ta, sai ya karrama ta, idan kuwa ya ki ta, to ba zai zalunce ta ba[1]. Fiyayyen halitta yana cewa: Ku kiyayi mace mai kyau da ta tashi ta girma a cikin mummunan gida kaskantacce[2]. Imam Sadik (a.s) yana cewa: Farin ciki ya tabbata ga wanda mahaifiyarsa ta kasance kamammiya[3]. Sannan hatta da yanayin kusantar iyaye da juna yana da nasa tasiri kan rayuwar yara: ya zo a cikin wata ruwaya cewa: “Idan lokacin kwanciya da kulluwar ciki suna da zuciya mai nutsuwa, da halin kwanciyar hankali, da annashuwa, kuma jijiyoyinsu suna kan halinsu na dabi’arsu, da kuma rashin raurawa a cikin jikinsu, to yaron zai yi kama da iyayensa ne[4]. Sannan idan yaro ya zo duniya sai kuma a kyautata sunansa: Imam Bakir (a.s) yana fada game da al’amarin suna mai kyau: “Mafi soyuwar sunaye su ne wadanda suke nuna bauta ga Allah madaukaki, kuma mafi kyawu daga garesu su ne wadanda suke sunaye ne na annabawa[5]. Wata hanya mai amfani shi ne hanyar shagaltar da yaro da kayan wasa a gida musamman idan lokaci ne ba na karatu ko bacci ba, da daukarsa wani lokaci zuwa filin yara don ya yin wasanni kamar lilo, da kwallo, da guje guje. Wannan kan iya sanya yaro ya taso da farin ciki da nishadi, da alfahari da iyayensa da ganin kyautatawa gare shi. Sannan wasa yana kyautata tunanin yaro da bude masa tunani. Ubangiji madaukaki yana cewa: “Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji dadi, kuma ya yi wasa, kuma lalle mu masu tsaro ne gareshiâ€[6]. Wani lokaci wasannin har da na kwamfita, amma kada a rika sanya masa na harbe-harbe da duk wasanni da malaman tarbiyya suka yi umarni a nesantar da yaro daga gare su, domin yawancinsu sukan kashe wa yara tausayi.
|