Tattaunawa Ta TaraDaukar Annabi da rashin kimar da ibn Abdulwahab ya shelanta cewa; shi "Darish" ne, wato dan sakon da kawai ba shi da kima sai kimar sakon kawai. Kun sanya Annabi yana kokwanton annabtarsa har sai da wani kirista ya gaya masa ai kai Annabi ne sannan ya samu nutsuwa, amma wahayi ya sake jinkiri ya sake kokwanto har ya kusa kashe kansa. Kun sanya Annabi (s.a.w) yana koyon tauhidi wurin kirista. Kun sanya Annabi yana samun galaba daga shedan da hatta da a sakonsa sai ya gafala ya yabi gumaka maimakon kushe su. Kun sanya Annabi (s.a.w) kasan darajar sauran annabawa. Kun sanya Annabi (s.a.w) yana fushi da kausasawa har ya la'ani wasu mutane ba bisa hakkinsu ba. Kun sanya Annabi (s.a.w) bai san yadda ake auren dabino ba har shukar mutane ta lalace. Kun sanya Annabi (s.a.w) yana zaluntar 'yan Badar ya kama ribatattun babu hakki kuma ya karbi fidiya babu hakki. Kun sanya Annabi (s.a.w) yana fitsari a tsaye a Bolar mutane. Kun sanya yana kuskure da yawa har sai Umar ya gyara masa.
|