Tattaunawa Ta ShidaWani lokaci ka nuna sukanka ga manyan malaman ahlussunna kamar Hakim, saboda sun yi laifin ruwaito abin da yake iya tabbatar da ko karfafa biyayya ga Ahlul Bait (a.s), ina ganin dukkan dalilai a wajenka komai karfinsu, sai ka yi musu hukunci da cewa; sun yi karo da Kur’ani, kai ka ce: kai ne Kur’ani kuma fahimtarka ita ce fadin Allah (S.W.T). kai mafi muni ma da kake nuna cewa Annabi (s.a.w) yana iya kuskure wal’iyazu bil-Lah! Kana ganin ko ya fadi magan to ai Allah ma ya fadi wata sabanin haka a Kur’ani, kana mai dogaro da ganinka da ra’ayinka na cewa; Annabi (s.a.w) bai san gaibi ba, wato; kai ka fi shi sanin abin da zai zo nan gaba ke nan, kuma kai ka fi shi fahimtar Kur’ani ke nan! Wal’iyazu bil-Lah! To malam abdussalam a irin wannan yanayi ka ga ke nan babu wani abu da zan iya cewa; sai dai kowa ya yi wa kansa hisabi kan addininsa tun kafin haduwa da Allah madaukaki, ya kuma shiryar da wanda ya kauce hanya kowaye shi daga cikinmu. Karancin saninka da mustalzamatil akaliyya a muhawararmu yana sanyawa ba ka ma fahimtar wasu abubuwan da kake fada balle kuma ka fahimci ni abubuwan da nake fada, ka ga ke nan muna magana alhalin ajujuwan maganarmu sun saba, don haka babu yadda za a yi a samu dan furamare kuma a yi masa laccar da ake yi wa masu yin digiri, ka ga ke nan babu wani amfani gareshi. Ka sani tumu ba a hawansa da ci, sai an cashe an surfe an nike an yi kari… an yi masa miya sannan sai ya zama a shirye yake domin a ci. Ba haka kawai ake watsa masa ruwan kuka ba sai a hau cinsa.! Yawan tanakudin maganarka kamar yadda na nuna a sama; misali; ka kore matan Annabi (s.a.w) daga kasancewa daga Ahlul Bait ne, a lokaci guda kuma ka sanya su, da cewa; ya ce; “anti minni bikhairâ€‌ ban san yadda wannan maganar zaka iya amfani da ita ba, wajen sanya su cikin Ahlul Bait. Maganarka a lokaci guda tana nuna kamar fitar da su daga ciki suka ne kuma garesu, abin da nake gaya maka ke nan, cewa ba ka san lawazimul akaliyya ba, tayiwu kyamarka ga mabiya Ahlul Bait (a.s) da kuma mummunar fahimta da ka yi musu ta sanya ka yi musu tawilin duk wata magana tasu kamar suka ce ga wani. Saba wa dukkan malaman musulmi gaba daya a cikin maganganunka, domin kana ganin hadisi mutawatiri komai adadin masu ruwaito shi matukar ya sabawa taka fassarar ga Kur’ani to bai inganta ba, wato; dukkan masana malamai na musulmi kai ka fi su sanin Kur’ani da sanin ingantaccen ra’ayi ke nan. Umar ya fada a cikin sahihul bukhari cewa bai’ar da suka yi wa Abubakar fitina ce da Allah ya kare musulmi sharrinta: Buhari; j8, sh26. Amma kai kuma kana nuna kafi Umar sanin bai’ar da aka yi wa Abubakar kana mai cewa; Allah ya ba wa abubakar. Yayin da kake cewa da ni: “Na ji ka ce manzon Allah (s.a.w) ya bar aliyyu RA a mtasyin halifansa. Allah kuma ya bada shi ga Abubakar RAâ€‌ A irin wannan yanayi da hatta wadanda suka yi bai’a kamar Umar dan Khaddab kai ka fi su sanin yadda abin ya wakana, to yaya kake son ni in gamsar da kai alhalin fadin Umar bai isa ya zama hujja ba a gun ka. Haka nan Umar bn Khaddab ya fadi cewa: “Akdhana Aliâ€‌ da ta shahara gunsa da littattafai masu yawa sun ruwaito shi, amma kai kana musun kasancewar Imam Ali (a.s) mafi ilimin sahabbai. To yaya kake zaton zan cigaba da ba ka dalili, idan na Umar ba shi da amfani a wajenka ni kuma nawa yaya zai zama mai hujja. Karancin sanin tarihi da kake da shi, da musun duk wani abu da al’ummar musulmi ta yi ittifaki a kan faruwarsa, idan kuwa haka ne sai ka yi musun sauran abubuwan da musulmi suka yi ittafaki a rayuwarsa, kamar ka yi musun dukkan samuwar musulmin farko ke nan. Kana mai musun la’antar Imam Ali (a.s) da Mu'awiya ya kafa, to sai ka yi musun yakarsa da sauran abubuwan da suka faru a tarihin musulmi. Ni da ni ne a makwafinka, ban gamsu da abin da nake a kai ba, da ban tsaya ina yaudarar kaina ba. Maimakon ka yi musun faruwar abun da al’umma ta kafu a kai idan ruhinka ya kasa dauka sai ka san wani abu da zaka yi wanda zaka samu nutsuwa da shi wajen Ubangijinka! Kana ganin aikin Annabi (s.a.w) yana iya sabawa fikihu kamar misalin da ka bayar a can baya na fikihu da sha a azumi wanda shi ne na yi tir da shi. Ka dauka addini kamar ramuwar gayya ce ba dalili ba, sai kai kuma ka yi tir da alwala da sallar da ta inganta daga Annabi (s.a.w). Allah ya sauwake! Idan mutumin da ba ma’asumi ba ne ya yi sabo, ba yadda zaka kafa hujja da shi akan hakan. Idan kuwa haka ne to sai mu halatta bautar gumaka domin su ma sun yi kafin musulunci ke nan. Ko kuma mu ya bi abinda aka yi wa Annabi (s.a.w) na tawaye a sulhun hudaibiyya, ko kuma mu ya bi kin biyayya gareshi a cikin bin rundunar Usama da hatta ta kai ga ya yi la’ana yana mai cewa: â€کla’anal-Lahu man takhallafa an jaisu Usamaâ€‌. Kai ya nemi a bari ya rubuta wasiyyarsa ma amma aka ki, kuma aka hana shi abin rubutu, wanda ibn Abbas yana kuka idan ya tuna wannan. Don haka ka koma wa musulunci da kyau, ka kalle shi da idanuwan basira, ba kallon bangare na mazhabanci ba, wallahi ina rantse maka da Allah madaukaki da ya halicci dukkan samammu da nine nake da shakku kan wajabcin biyayya ga Ahlul Bait (a.s) kiftawar ido da na bar su gaba daya na yi riko da abin da na gamsu da shi a hujja, sai dai ban samu wani abu da ya fi shi inganci ba, don haka idan kana ganin ka nutsu da abin da kake a kai to ka tabbata a kai, amma idan kana kokwanto kamar yadda maganganunka suke nunawa kana mai warwarar abubuwan da kake cewa; ko kuma ka yi musun abin da ya inganta a gunku, to ka sake komawa ka yi tunani a kanka. Idan ka gajiya kan wasu abubuwan to ka ce; ka gajiya, domin ka kasa ayyana jagoranka babu bukatar sai ka yi abin da duk wanda ya ji ya san ka kasa ne, sai ka koma ka yi tunani. Ka sani Annabi (s.a.w) ya bar mutane 12 da su ne jagororin al’umma har alkiyama ta tashi kowane zamani akwai dayansu kuma shi ne jagoran al’ummarsa. Idan ka ki yarda da su, to sai ka kawo naka ababan biyayya ba ka amsa da cewa; Annabi (s.a.w) ne. wannan ba ya nuna komai sai gajiyawarka. Ka nuna ka fi kowa sanin Kur’ani a cikin al’ummar Annabi (s.a.w), hatta da mutanen da kake takama da su, abin da suka kawo maka ba shi da kima. Kana yi wa ayoyin Kur’ani hawan da ka dama, ina yi maka nasiha da ka bar hakan, ka bari sai ka nuna, ba tun kana iri ba ka kai matsayin tofo ba ka ce zaka fara yin â€کya’ya. Kana cewa Allah ya ce: ruhama’u bainahum, kana kafa hujja da wannan da cewa ba zasu yi sabani ba, kana kuma ayyana wa Allah su waye ruhama’u bainahum, sannan kuma kana sabawa duniyar musulmi da ba ta tafi akan abin da ka ce ba. Duba ka gani Buhari ya kawo cewa: Fatima (a.s) ta yi fushi da Abubakar wata shida har ta mutu ba ta yi masa magana ba, kuma ba ta yarda ma ya halarci janazarta ba: Buhari, j5, sh:82. ko sh:139. sannan ga daruruwan sabani da yakoki da la’ance-la’ance da suka gudana da kashe-kashe duk tsakaninsu da dukkan al’umma ta yi ittifaki akan faruwarsu, amma sai ka kawo ayar Kur’ani kawai ka fitar da hukunci ka wautar da hankulan dukkan musulmi kana mai musun abin da suka samu tun daga wancan zamani da suka gani kuma suka ji har ya kawo ga wannan al’ummar. Ka koma wa tunaninka, idan kuma a bisa sani ne kake wa Littafin Allah tawilin da ka ga dama, to wannan kuma yana komawa tsakaninka da Ubangijinka ne. Ilimi yana da zurfin da ba ka tsammani, kuma Allah da manzonsa su ne suka fi kowa sani, sannan kuma Allah ya sanar da manzonsa abin da zai faru, kuma Manzo (s.a.w) ya dauki dukkan wani mataki akan hakan, don haka ya rage wa al’umma ta yi riko da abin da ya bari ko kuwa. Kuma duk wanda ya kauce bai cutar da Allah komai ba sai kansa. Allah ya wadatu gabarinmu, ba lallashinmu yake yi ba, kuma ba wani amfani zamu yi masa ba, sannan kuma ya wadatu gabarinmu, ba kuma gori muke yi masa ba cewa; mun yi imani, shi ne zai yi mana akan cewa ya shiryar da mu. Don haka ne ma ya hana annabinsa damun kansa da bakin ciki domin wani bai yi imani da abin da ya zo da shi ba!. Don haka ne ma nake ganin bahasi da wannan yanayi ba shi da wata kima sai bata lokaci, kuma muna fatan Allah ya shiryar da mu, ya kara mana fahimtar juna. Idan ka sake kawo maganar sahabbai ka fita daga maganarmu ta asali ba zaka sake ganin amsata ba, har abada. Haka nan idan na sake ganin sharri da kage. Hafiz Muhammad Kammala gyarawa 01 /July/ 2009
|