Tattaunawa Ta UkuIna ganin maganar gaba da Ahlul Bait (a.s) ta fi rana bayyana, komawa tarihi ka sha mamaki. Duba littattafan Ahlussunna kan Ahlul Bait (a.s), duba daya daga ciki kamar makatilul Talibiyyin. Sannan kuma abin da ya faru tun farko ga kakarsu wacce ta nuna zaluntarta da aka yi, ta hanyar umarni da in banda â€کya’yanta da mijinta Imam Ali (a.s) ba wanda ya san kabarinsa. Misalin da zan ba ka domin ka taba: Idan bayahude ya yi mana gorin cewa suna girmama jikokin Annabi Dawud (a.s) har na hawa sittin a lokacin da aka kashe jikan Manzo (s.a.w) wanda shi da kansa ya rena. To ni ina gaya maka tabbas da bayahuden ya san sirrin musulunci da abin da musulmi suka yi bayan Annabi (s.a.w) da ya yi mana gori fiye da hakan, da ya yi gorin cewa; idan mun isa mu nuna kabarin â€کyar manzonmu (a.s). Shin wannan bai isa ya sanya musulmi jin kunya ba! Shin wannan ba ya nuna zaluntar da aka yi wa Ahlul Bait (a.s) tun farkon wafatin Annabi (s.a.w)! Sannan tambayar mai musun tafarkin Ahlul Baiti (a.s) game da sunnarsu sai na ce maka: Sunnar Ahlul Bait (a.s) ta zo ne daga manzon Allah (s.a.w) da ya ce a yi riko da ita domin ya san ba zata saba wa tasa ba, kuma ba su da wani sabani domin ita bayani ne na abin da ya bari. Ahlul Baiti (a.s) sun yi umarni ga Shi'a su yi tarayya da musulmi a komai na zamantakewar al’umma; Idan ka ga sabanin haka; kamar mu’amala maras kyau to daga Shi’a ne. Amma mas’alar azumi da shan ruwa da ka ce Shi'a suna yi daban wannan wani abu ne na fikihu da kana iya samun sabani hatta da tsakanin Sunna kansu, sannan kuma yana komawa ga fahimtar mene ne ma’anar “Lailâ€‌ da aka ce “summa atimmus siyama ilal lailâ€‌. Amma tambayarka mai cewa: A ina aka ruwaito cewa wanda yayi imani a yau ya fi sahabbai 50?. Sai na ce maka: Koma littattafan Sunna da na yi maka nuni da su: kama ga Masnad Ahmad bin Hambal har zuwa sauran, a cikin bayanin satin da ya gabata. Amma hadisin nan na "Duk wanda ya mutu bai yi imani da imamin lokacinsa ba ya yi mutuwar jahiliyya, da kuma rashin imaninka da imamin zamaninka, da kuma nuna yawaitar jikokin Annabi (s.a.w) masu yawa haka: sai na ce maka; Ka duba littattafai kamar haka: Masnad Ahmad bn Hambal: j 2, shafi 83. 154, da j 3 shafi 446, da 4/ 96, Mustadrak alassahihain, majma’azzawa’id, kanzul ummal, Dabarani, da sauransu. Ka duba kuma; Almahim walfitan, shafi: 168, daga Imam Ali (a.s) da Mu'awiya, da ibn Umar, da Ma’azu bn Jabal da Abuzar. Don haka an karbo hadisin daga sahabbai daban-daban. Sannan kuma akwai: Yanabi’ul mawadda na Kanduzi, wani abin sha’awa shi ya fadi cewa wilayar aali Muhammad tana daga cikin jiga-jigan imani tare da cewa shi bahanife ne. sannan kuma ya karafafi maganar da wannan hadisin. Sannan kuma da ka ce: ba ka yarda da Imamin zamani ba, to kai ne Imamin zamaninka ke nan, sai ka zama hujjar Allah a kanka, idan kuwa ka ce ba kai ba ne imamin kanka, to waye ka mika wa bai’a da jagoranci a matsayin imamin zamaninka yanzu? Domin wanda ya mutu ba shi da jagora ya yi mutuwar jahiliyya. Sannan kuma jikokin Annabi (s.a.w) Allah ya kara mana yawansu ba su ne imamai ba wanda shari’a take ce musu: aali Muhammad ko Ahlul Bait (a.s) da ake yi wa salati. Domin na gaya maka Annabi (s.a.w) ya fassara su da cewa su sha uku ne, wadanda hudu a lokacinsa suna raye; wato; Ali da Hasan da Husain da Fadima (a.s) wadanda yake nuni da su yana fadin “Allahumma ha’ula’i Ahlu baitiâ€‌ yana kuma tsayawa a bakin kofarsu kusan wata bakwai har ya yi wafati yayin sallar asuba yana maimaita wannan suna garesu. Sauran tara kuma ruwayoyi masu yawa ne suka zo da su. Amma idan kana nufin Ahlul Bait (a.s) da ma’anar lugga kamar da nufin zuriyar mutum, kamar yadda ake gaya wa sharifai a yankinmu wannan haka nan ne mana, kuma su ne wanda shari’a ta yi magana cewa bai halatta su ci sadaka ba. Wato sun yi tarayayya da aali Muhammad tsarkaka sha uku a kan wannan hukunci, sannan kuma sha biyu wato idan ka cire Zahara (a.s) su hujja ne na Allah a kan talikai kowannensu a zamaninsa. Don haka kada ka samu cakudewa. Shari’a ba shirme take yi ba ta ce maka: wadannan miliyoyin mutane tsarkaka ne kuma ayyukansu da zantukansu da sauransu hujja ne. Don haka yana da kyau ka san me Shi'anci yake cewa: kuma ka riga ka sani cewa; hatta da mafiyawan shi'a a yankunanmu ba zurfi suka yi cikin sanin mazhabin Ahlul Bait (a.s) ba. Amma maganarka ta ce; Don Allah a koma ma Kur'ani da ingattatun sunnonin Annabi (SAW) ko a samu tsira duniya da lahira. Wannan shi ne abin da ya kamata ga dukkan musulmi, amma ka sani cewa: ba zaka iya sanin Kur’ani ba ko sunnar Annabi sai da abin da shi annabin ya yi bayani. Kuma maganganunka suna nuna cewa: har yanzu ba ka kawo ayar Kur’ani daya ba da ka fassara ta daidai kamar yadda Annabi ya fassara, ka ga ke nan akwai bukatar ka samu nutsuwa sosai da tunani kan cewa yaya Annabi ya fassara Kur’ani sabanin ra’ayoyin sauran mutane. Kuma su waye ya bari masu bayanin abin da ya bari na sunnarsa da zasu kasance makoma idan al’umma ta yi sabani. Bai kamata ba domin wani yana balarabe ko ya san larabci sai ya hau Kur’ani da fassara yadda ya so, idan haka ne sai mu ce: muna sha’awarku larabawa kun san Kur’ani, alhalin ba haka ba ne. Manzo (s.a.w) ya yi bayanin ma’anar Ahlul Bait, da zulkurba, da salla, da zakka, da humusi, da alwala, da aure, da azumi…, da dukkanin wani hukunci, amma kiyasi da ra’ayi bisa rashin sani ko son rai sun sanya jirkita da karkatar da ma’anar kalmomin addini, da hukuncin shari’a.
|