Yahudawa



Yahudawa

Wannan Hadisi ruwaya ce daga Sadiku Ahlil Bait (A.S) game da tattaunawar Manzo da Ma'abota wannan addini wanda a cikinsa akwai usulubi mai kyau na muhawara da ma'abocin wata Akida da ta saba ta da mai muhawara, wanda a cikinta zamu koyi muhawara da mukabala da munazara da hanyar da take mafi kyau kamar yadda aka yi umarni da (Bil lati Hiya Ahsan). Yana kuma koyar da Hanyoyin kafa dalili Mubashir wato dalili na kai tsaye da kuma Gaira mubashir, da kuma Jawabil halli wato Hanyar warwara da kuma Jawabin Nakdi, wato Hanyar kama mutum da abin da ya yarda ya kuma yi imani da shi. A lokaci guda kuma yana iya nuna mana hakikanin manufar wannan Addini da yadda ma’abotansa suke fassara Akidojinsa. Kuma tana nuna mana yadda aka canja koyarwar Addinin da ya gabata, al'amarin da wannan al'umma ba ta tsira daga irinsa ba ta hanyar riko da Raunanan maganganu ko kuma Tafsirin da ya kafu bisa mahanga ta kuskure da yakan kai ga kurakarai wajan fahimtar Addinin Allah.

Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su, al’ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ma ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su zuwa ga rarraba zuwa Mazhabobi da Kungiyoyi na Akida daban daban. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne al’ummar nan ta bambanta da sauran al’ummu, domin su wadancan al’ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa’ar canza Addinin nasu gaba daya a kuma kautar da Akidunsu daga sahihancinta kamar Yahudawa da Kiristoci da Zartush da Sa’ibawa da sauransu. Amma wannan al’umma Allah ya yi alkawarin kare littafinta, shi ya sa ma duk wanda yake ganin wani yana da Alkur’ani daban da wanda yake hannun musulmi to yana ganin Allah Ajizi ne daga alkwarin da ya dauka na kare littafinsa, kuma irin wadannan mutane suna a matsayin wadanda suka kafirce wa Allah ta hanyar kafircewa Ayar Alkur’ani mai girma.

MUNAZARAR MANZO (S.A.W)

Imam Assadik (A.S) ya ce: "Daga Babana Albakir (A.S) daga Kakana Ali Dan Al-Husain (A.S) daga Babansa Husain Shugaban Shahidai (A.S) daga Babansa Ali Dan Abi Dalib (A.S) cewa, wata rana ma’abota Addinai biyar suka hadu a wajan Manzon Allah (S.A.W); Yahudawa da Kiristoci da Dahariyya da Sanawiyya da Mushrikan larabawa.

Sai Yahudawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Uzairu (A.S) dan Allah ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka shiryuwa zuwa ga gaskiya, amma idan ka saba mana zamu yi jayayya da kai. Kiristoci suka ce: Mu muna cewa Isa (A.S) dan Allah ne da ya shiga cikinsa ya hade da shi idan ka bi mu mun riga ka zuwa ga gaskiya amma idan ka saba to ma ja da kai. Dahariyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa: Halittu ba su da farko ba su da karshe suna nan har abada, kuma mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mun riga ka fahimtar gaskiya idan kuma ka saba mana to ma ja da kai. Sanawiyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa haske da duhu su ne masu juya dukkan ala’amura, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka fahimtar gaskiya amma idan ka saba mana ma ja da kai. Mushrikan larabawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Gumaka Ubangizai ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mu mun fika mun riga ka zuwa ga gaskiya da shiriya amma idan ka saba mana to ma ja da kai.

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce Allah (S.W.T) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.

YAHUDAWA

Sannan ya ce da Yahudawa: Shin kun taru ne nan domin in karbi maganarku babu wata hujja sai suka ce: A’a. Ya ce: Me ya kai ku ga cewa Uzairu (A.S) dan Allah ne? Sai suka ce: Domin ya raya wa Bani Isra’ila Attaura kuma ba wanda Allah zai yi masa haka sai dansa. Sai Manzon Allah ya ce: Domin me Uzairu (A.S) zai zama dan Allah ga Musa (A.S) alhalin shi ne ya zo wa Bani Isra’ila da Attaura kuma aka ga mu’ujizozi daga gare shi kamar yadda kuka sani. Idan kuwa Uzairu (A.S) zai zama dan Allah saboda karamar raya Attaura, me ya sa kuka kira shi dan Allah ba Musa ba? Sai suka ce: Saboda ya raya wa Bani Isra’ila Attaura bayan ta bace, ba kuma yadda zai ba wani damar haka sai wanda yake dansa. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ya ya Uzairu (A.S) ya zama dan Allah ba Musa (A.S) ba wanda shi ne ya zo da Attaura din aka ga mu’ujizozi a hannunsa kamar yadda kuka sani?. Idan kuwa Uzairu (A.S) zai samu wannan matsayi saboda ya raya Attaura to Musa (A.S) shi ne ya fi cancanta da ya zama dan ba shi ba, domin shi ne ya zo da Attaurar tun farko.

Idan kuma shi Uzairu (A.S) ya cancanci girmama wa a matsayin da saboda ya raya Attaura to Musa ya cancanci matsayin da ya fi na da, domin ku idan kuna nufi da da ma’anar da kuke gani a Duniya na ‘ya’ya da iyaye suke haifarsu ta hanyar takinsu (kwanciya) daga iyaye maza ga su matan to kun kafircewa Allah kun kwatanta shi da bayinsa kun kuma wajabta masa a binda yake da siffa na fararru, saboda haka ya wajaba ke nan ya zama Fararre abin halitta a wajanku ya zama yana da mahalicci da ya fare shi.

Sai suka ce: Ba haka muke nufi ba, hakika wannan kafirci ne kamar yadda ka fada sai dai mu muna nufin girmamawa kamar yadda wasu malamai sukan kira wanda suke son girmamawa da wani matsayi da “Ya dana!” ko kuma ya ce: “Wannan dana ne” ba domin ya haife shi ba, domin saudayawa yakan gaya wa wanda ba su da wata nasaba da shi hakan. Haka nan yayin da Allah ya yi wa Uzairu (A.S) wannan ni’ima sai muka fahimci cewa bai yi masa haka ba sai don ya rike shi dansa ta hanyar girmamawa ba domin ya haife shi ba. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Wannan shi ne abinda nake gaya muku cewa, idan da wannan Uzairu (A.S) ya zama dansa to wannan matsayi ya fi cancanta ga Musa (A.S) kuma Allah zai kunyata duk mai karya da furucinsa da kansa kuma aniyarsa zata dawo kansa. Ku sani cewa abin da kuka kafa dalili da shi zai lizimta muku fiye da abinda ya wuce haka, domin ku (a misali) kuna cewa: Wani mai girma daga cikinku yakan gaya wa waninsa da ba su da nasaba: "Ya dana!" ba don ya haife shi ba, sai don girmamawa, kuma zaku iya samun wannan mai girma din yana gaya wa wani cewa: "Dan’uwana ne" ya kira wani kuma da "Wannan shehina ne" ko "Babana ne" ko "Shugabana ne" ko "Ya shugabana!" ta hanyar girmamawa, wato duk sa’adda aka samu wanda ya fi girma to sai ya dada masa kalma ta girmamawa fiye da dayan, idan kuwa haka ne a bisa abinda kuke cewa ya halatta Musa (A.S) ya zama "Dan’uwan Allah" ko "Shehinsa" ko "Babansa" ko "Shugabansa" domin ya fi Uzairu (A.S) daraja kamar yadda idan wani ya fi da daraja sai a ba shi girmamawa fiye da shi, sai ya ce masa: "Ya Shugabana!" ko "Ya Shehina!" da "Ya Ammina!" da "Ya Shugabana!" ta hanyar girmamawa domin Karin girma, shin ya halatta a ganinku Musa (A.S) ya zama Dan’uwan Allah ko Shehinsa ko Amminsa ko Shugabansa ta hanyar girmamawa domin girmansa ya fi na Uzairu (A.S) kamar yadda ake dada girma ga wanda ya fi da a fadarku  a ce da shi: "Ya Shugabana" "Ya Shehina" "Ya Ammina" "Ya Sarkina" .

Imam Assadik (A.S) Ya ce: Sai mutanen suka dimauce suka ce "Ya Muhammad! ka saurara mana mu yi tunani tukuna game da abinda ka ce. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ku yi duba da zukata masu kudurce yin adalci, Allah ya shiryar da ku.

 Imam Assadik (A.S) ya ce: Sai suka ce : “Zamu duba al’amarinmu”. ya ce: “Na rantse da wanda ya aiko shi (S.A.W) da gaskiya kwana uku bai yi musu ba sai da suka zo wajan Manzon Allah (S.A.W) suka musulunta, sun kasance mutane ishirin da biyar ne; Biyar daga kowace Kungiya. Suka ce: Ya Muhammad! Ba mu ga Mai dalili kamar naka ba, mun shaida kai Manzon Allah ne!!.”



1