Hada Salloli Biyu



Abu Na Farko: Lokutan Salla

Malaman musulmi sun yi bincike game da lokacin salla, sun saba a kan cewa; shin wannan lokacin sharadin inganci ne ko kuma sharadin wajabci?

Mazhabar hanafiyya ta tafi a kan cewa ba sharadi ba ce ta wajabci, ba kuma shardin inganci ba ce, domin suna cewa: Shigar lokaci sharadi ne na gabatar da salla, da ma’anar cewa; bai halatta ba a yi salla sai lokacin ta ya yi. Don haka ne muka samu sun hadu da wasu daga mazhabobi a kan cewa salla ba ta wajaba sai lokacinta ya yi, idan lokacin ta ya yi to a lokacin ne mai shari’a yake maganar yinta lokaci mai yalwa, da ma’anar idan ka yi ta a farkon lokaci ta yi, idan ba ka yi ba a farkonsa to ba ka yi sabo ba, idan ya riski salla dukkanta a lokaci to ya zo da ita kamar yadda mai shari’a ya nema daga gareshi kuma ya sauke nauyi, kamar yadda idan ya yi ta a farkon lokaci da tsakiyarsa, amma yin salla gaba dayanta bayan lokaci ya fita ta yi sai dai ya yi sabo da jinkirta ta ga barin lokacinta[3].

Idan salla ba ta inganta sai bayan lokaci ya shiga sai mu ce idan sharadi ne ta aiwatar da salla, ko sharadi ne na inganci ko sharadi ne na wajabci, to wane lokuta ne aka shar’anta yin salloli biyar a cikinsu gun mazhabobi, yaya zamu san su?

Muna sanin lokutan salla da karkatar rana da kuma inuwa da take faruwa bayan karkatar rana, da wannan ne muke sanin lokacin azahar da shigar lokacin la’asar, sannan sai faduwar rana da shi ne muke sanin magariba, sannan sai boyuwar shafaki ja ko fari a kan wani ra’ayi, da wannan muke sanin shigar lokacin issha sannan sai farin da yake bayyana a sasanni da shi ne ake sanin lokacin assuba[4].

Amma lokacin salloli biyar a mazhabar Ahlul baiti (A.S) to asalinsa yana daga abin da ya zo daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce; “Jibril ya zo wajan Manzo Allah (S.A.W) sai ya sanar da shi lokacin salla, ya ce ka yi sallar asuba yayin da alfijir yaketo, ka yi sallar farko yayin da rana ta karkata, ka yi sallar la’asar bayanta, sallar magari idan kaskon ya buya, sallar issha idan shafaki ya buya, sai ya zo masa washegari, sai ya ce: Ka waye da safiya sai ya waye da ita, sannan sai ya jinkirta azahar yayin lokacin da ya sallaci la’asar a cikinsa, ya yi sallar la’asar bayanta, ya yi sallar magariba kafin faduwar shafaki, ya yi sallar issha yayin da sulusin dare ya tafi, sannan sai ya ce: tsakanin wadannan lokuta biyu lokaci ne”[5].

Da wannan ne lokutan salla biyar da aka wajabta ya zama guda uku, lokacin sallar azahar da la’asar da lokacin sallar magariba da issha da lokacin sallar asuba, ubangiji madaukaki yana fada: “Ka tsaida salla da karkatar rana zuwa duhun dare da kuma ketowar alfijin, hakika ketowar alfijir abin halarta ne”[6].

Faharur Razi yana cewa: Idan muka fassara duhu da farkon bayyanar duhun, wanann yana nufin farkon lokacin magariba, koda yaya ne, ayar tana maganar lokuta uku na salla ne: lokacin karkatar rana, da kuma lokacin magariba, da kuma lokacin alfijir, wanan kuma yana nufin karkatar rana ya zama lokacin azahar da la’asar sai ya zama lokaci ne na tarayya tsakanin azahar da la’asar, farkon magariba kuma lokaci na tarayya tsakanin azahar da la’asar, wannan kuma yana nuna halarcin jam’i tsakanin azahar da la’asar da kuma tsakanin magariba da issha kai tsaye, sai dai dalilai ya zo a kan cewa jam’i a lokacin zama ba uzuri bai halatta ba, sai ya zama ya halatta saboda uzuri na tafiya da ruwan sama da sauransu[7].

Allama hilli ya ce: Azahar da la’sar kowanne yana da lokaci biyu; Lokacin da yakebanta da kuma lokacin da yake na tarayya, wanda yakebanta azahar daga karkatar rana zuwa daidai lokacin yin ta (gwargwadon yin raka’a hudu) la’asar kuma daidai gwargwadon yin ta a karshen lokaci, amma tsakanin nan duka lokaci ne da suka yi tarayya a ciki.

Magariba da issha su ma suna da lokuta biyu; Wanda yakebanta da magariba shi ne gwargwadon yin ta bayan faduwar rana, issha kuma daidai gwargwadon yin ta a rabin farko na tsakiyar dare, sauran lokacin da yake tsakanin haka ya na zama tarayya tsakaninsu, saboda haka babu wata ma’ana ga jam’i a gunmu (domin kowacce an yi ta ne a lokacinta), amma waninmu su sun kebe wa kowacce daga azahar da la’asar  lokacinta, haka ma magariba da issha kowacce da lokacinta saboda haka su a gun su akwai ma’ana ga jam’i[8].

Abu Na Biyu: Hukuncin Hada Salla Biyu Da Dalilansa Gun Mazhabobi

Idan mun san lokutan salloli biyar dalla-dalla, muka kuma san lokacin da yakebanta da kowacce da kuma lokacin da yake na tarayya, sai mu tambaya, menene hukuncin shari’a a hada salloli biyu; sallar azahar da la’asar da kuma sallar magariba da issha a lokaci daya?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next