Bada'i(Canjawa)Tambayoyi Da Amsa Game Da Imani Da Bada
Akwai tambayoyi da aka yi game da Bada kamar haka; 1- Imani da Bada yana iya kai wa ga wasa ya zo daga Allah (S.W.T) domin tare da ya san cewa za a samu canji a lokacin bayar da labari, ya zama wasa kenan. Amsa: Wasa yana kasancewa ne idan an kaddara ba wani manufa da amfani da bayar da labarin zai samar, wannan kuma ba zai yiwu a iya tabbatar da shi ba domin akwai yiwuwar samun amfani da manufa da amfanin yana komawa ga bawa ne. 2- Idan annabi ya bayar da labari da faruwar wani abu sannan sai aka sami Bada a labarin farko ba makawa ya zama ya dogara ne da wani abu wajan bayar da labarin farko, kuma yaya annabi ko imami zai yi game da bayar da amsa kan abin da ya fada a baya?. Amsa: Bari mu bayar da misali; Da wani zai sha guba mai halakarwa da zata kai ga mutuwa tabbas kana iya bayar da labarin mutuwarsa bayan awowi kuma wannan labari gaskiya ne idan an yi la’akari da abin da ya kai ga mutuwar, da mutuwar ba ta faru ba to dole ya zama saboda faruwar wani abu da ya hana afkuwar hakan, kamar zuwan likita da zai yi masa magani da cikakkiyar kwarewa, wancan bayar da labarin ba karya ba ne kuma ba a ganinsa bayar da labari ba dalili, haka nan al’amarin wahayi da yake bayar da labarin abin da zai faru a nan gaba duk gaskiya ne idan an yi la’akari da sababi wanda yake da sharadin rashin faruwar abin da zai hana aukuwar hakan, saboba haka a nan babu wani abin ki da zai lizimci wannan magana sai dai rashin sanin annabi ko imami da faruwar abin da ya hana aukuwar hakan, muna iya cewa Allah yana iya ba wa annabi labari da faruwar abin amma ya ki ba shi labari da abin da zai hana afkuwarsa saboda wata maslaha da take ga bayi[23]. 3- Faruwar Bada yana iya kaiwa ga tuhumar annabi ko imami da karya?. Amsa: Tuhumar annabi ko imami da karya zunubin yana kan wanda ya yi haka ne, domin tuhumar idan ta zo daga kafiri to wannan ba mamaki domin da ma ya ki duk imani da Allah da annabta da makoma, idan kuma ya zo daga mumini to imaninsa zai hana shi, idan kuwa bai hana shi ba to wannan mai raunin imani ne. Muhimmi a nan shi ne Bada ba dalili ne na hankali ba da zai sa tuhuma da karya, da yawa ma Bada yana bayar da yakini ne kamar a kissar Annabi Ibrahim (A.S) da aka umarta ya yanka dansa, fansar dan da wani abu yana bayar da yakini ne na farko da yanka dansa Isma’il (A.S). Ba don labarin farko ya zama gaskiya ba da ba a umarce shi da yanka rago ba maimakon dansa, domin fansa a nan tana nufin canji (Bada). Bayanin Abin Da Ya Gabata A Takaice
Bada da ma’anar samun canjin ra’ayi mustahili ne ga Allah madaukaki kuma imamiyya ba sa imani da shi, wanda ya yi imani da hakan a wajansu kafiri ne kuma dole a barranta daga gareshi[24]. Na’am Bada wanda yake hankali ya yarda da shi kuma wajibi ne a yi imani da shi, shi ne wanda ayar kur’ani mai girma ta yi bayaninsa: “Allah yana shafe abin da ya so yana kuma tabbatar (da abin da ya so) kuma a gunsa akwai Ummul kitabiâ€. Wannan shafewa da tabbatarwa ga abin da Allah yake bayyanarwa a harshen annabinsa ko waliyyinsa a zahiri yana zama domin maslahar da take cikin bayyanarwar ne, sannan sai ya shafe shi, sai abin da ba shi ne ya bayyanar ba ya faru tare da cewa Allah ya san hakan tun farko.
|