Tarbiyyar Yara A MusulunciShi ya sa Malaman tarbiyya suke cewa: Yana da wahala ga mutum ya canja da wuri bayan ya yi shekaru arba’in kan wani ra’ayi, misali idan mutum ya kai shekara arba’in ba ya sallar dare to yana da wahala ya iya jurewa ya dage a kai, Shi ya sa idan saurayi ya dore a kan hanya ta gari to yana da wahala ya canja Sai dai idan ya zama akwai wani sirri tsakaninsa da Allah da ba shi da kyau, ko kuma lallai zuciyarsa ba ta kama hanya ta gari ba, ko ba ta doru bisa mahanga sahihiya da Allah ya dora Addininsa a kai ta hannun Manzonsa (S.A.W) ba. Haka ma idan ya zama yana da dauda a zuciya kamar hassada ko mugun kulli Shi ya sa ya zo a wata ruwaya cewa: Kada a duba tsawon ruku’u ko sujadar mutum, ta yiwu wata al’ada ce da ya saba da ita, idan ya Haka ma yaro idan ya saba da wani abu haka zai taso da shi a matsayin saurayi, idan da ya saba da karatu sai ya zama saurayi to ba zai iya Kur’ani Ya Yi Nuni Da Mu’amala Da Yara
Kur’ani mai girma ya himmantu da tarbiyyar yaro da kula da shi, don haka ne a ayoyi masu yawa ya yi magana game da ‘ya’ya da hakkokinsu, da yadda ya kamata a kalle su, da zama da su, da zamu iya kawo su a dunkule kamar haka: 1- ‘Ya’ya adon rayuwar duniya ne: Kahafi: 46. 2- ‘Ya’ya su ne asasin jarrabawa daga Allah: Tagabun: 15. 3- Wasu daga ‘ya’yanmu makiyanmu ne: Tagabun: 14. 4- Kada ku damu da nauyin ‘ya’yanku a kanku: An’am: 151. 5- Kada ku yi alfahari da yawan ‘ya’yanku:
|