Tattaunawar Addinai
[1] - Surar Nahli: 125.
Sai suka ce: A’a, mu ba mu ga farko gare ta ba kuma ba mu ga karshe gareta ba. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Saboda me kuke hukunci da rashin farkonta da rashin karshenta har abada ga ku ba ku ga farkonta ba, kuma karewarta shi ya fi cancanta ya wakana fiye daga bayanin da irinku yake yi game da ita, sai a yi mata hukunci da faruwa da karewa da yankewa domin ba ku ga dadewa ko wanzuwa gareta ba har abada.
Ba kuna ganin dare da rana ba?. Suka ce: Na’am. Sai ya ce: Shin kuna ganinsu ba su gushe ba kuma ba zasu gushe ba? Suka ce: Na’am. Sai ya ce: Shin yanzu ya halatta ku yi hukunci da haduwar dare da rana waje daya? Suka ce: A’a, Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ashe kenan kowannensu rabe yake da dayan sai daya ya riga daya ya zama duk inda daya ya yanke dayan yana gudana bayansa. Suka ce: Haka yake. Sai ya ce: Kun yi hukunci a nan da faruwar abin da ya gabata na daga dare da rana alhalin kuma ba ku gan su ba, saboda haka kada ku musa wa Allah ikonsa.
Sa’annan sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin kuna cewa duk abin da ya gabata na daga dare da rana yana da karshe ko ba shi da karshe? Idan kun ce: Yana da karshe, to kun sami karshen da ba shi da farkonsa, idan kuma kuka ce: Yana da karshe to an sami lokacin da babu wani abu da ya kasance daga cikinsu. Sai suka ce: Na’am.
Sai ya ce da su: Shin kun ce Duniya Dadaddiya ce ba Fararriya ba kuna sane da ma’anar da kuke nufi da furucin da kuka yi da kuma abin da kuke musawa? Suka ce: E. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Wannan halittu da kuke gani sashensu suna bukatuwa zuwa ga sashe, domin kowanne ya dogara ne ga samuwa da daya sashen nasa kamar yadda zaku ga gini sashe yana bukatar sashe, in ba haka ba, da bai yi karfi ba bai hadu ba haka ma sauran abubuwan da muke gani.
Ya ce da su kuma: Idan wannan bangaren da sashensa yake bukatar sashe domin ya yi karfi ya cika shi ma Dadadde ne to ku bani labari da ya kasance Fararre da yaya ya kamata ya kasance? kuma yaya siffarsa ya kamata ta kasance?.
Imam Sadik ya ce: Sai suka dimauce suka san cewa ba yadda za a yi a samu Fararre da sifa da suke siffanta shi da ita sai sun same ta ga wannan abin da suka raya cewa Kadimi (Dadadde) ne. Saboda haka sai suka tage suka ce: Zamu duba al’amarinmu tukuna.
Sanawiyya
Sa’annan sai Manzo (S.A.W) ya fuskanci Sanawiyya da suka ce: Haske da Duhu su ne masu tafiyar da al’amuran rayuwar halittu, ya ce: Menene ya kai ku ga fadin haka? Sai suka ce: Saboda mun samu Duniya kala biyu akwai Sharri da Alheri, kuma muka sami Alheri yana kishiyantar Sharri, saboda haka sai muka yi musun ya zama mai aikata wadannan abubuwa ya zama daya da yake aikata abu sannan ya zo da kishiyarsa, don haka dole ne ya zama kowanne yana da mai aikata shi, shin ba ka ganin cewa mustahili ne kankara ta kona ruwa kamar yadda ba yadda zai yiwu wuta ta sanyaya ruwa? Don haka ne muka tabbatar da cewa akwai Dadaddu biyu Masu kagowa ga Duhu da Haske.
Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Shin ba kwa ganin Baki da Fari da Ja da Yalo da Kore da Bulu, kowanne yana kishiyantar juna, domin mustahili ne guda biyu daga cikinsu su hadu waje daya kamar yadda zafi da sanyi kishiyoyi biyu ne da mustahili ne su hadu waje daya? Suka ce: Na’am. Ya ce: Don me ba ku tabbatar da Kadimai da adadin launinsu ba, ku sanya wa kowanne daga cikin kishiyoyin nan Kadimi mai yin sa da ya zama ba mai yin dayan ba?. Sai suka yi shiru. Sannan ya ce: Yaya a ka yi Haske da Duhu su ka cakuda, alhalin wannan sha’aninsa shi ne ya yi sama wancan kuma ya yi kasa!? Shin kuna ganin da wani mutum ya yi Gabas yana mai tafiya wani kuma ya yi Yamma yana mai tafiya a ganinku zai yiwu su hadu? Suka ce: A’a,. Sai ya ce: Ashe kenan dole ne kada su Hasken da Duhun su hadu, domin kowanne ya fuskanci fuskar da dayan bai fuskanta ba! Yaya aka yi kuka samu faruwar haduwar wannan Duniya daga abubuwan da suke bai yiwuwa su hadu? Hakika su dai ababan juyawa ne ababan halitta. Sai suka ce: Zamu duba al’amarinmu.
Mushrikai
Sa’annan sai Manzo (S.A.W) ya fuskanci Mushrikan larabawa ya ce: Ku me ya sa kuke bautawa gumaka sabanin Allah (S.W.T)? Sai suka ce: Muna neman kusanci da Allah da wannan ne. Sai ya ce da su: Shin ita (gumakan) tana mai ji mai biyayya ga Ubangijinta ne kuma mai bauta gareshi shi ya sa kuke neman kusancin Allah da bauta mata da girmama ta? Sai suka ce: A’a. Ya ce: Ku ne kuka saka ta da hannunku? Suka ce: Na’am. Ya ce: To ai da ya halatta bauta ga wanin Allah, da ita tafi cancanta da ta bauta muku da fiye da ku ku bauta mata! Ashe kenan wanda ya umarce ku da bauta mata bai san maslaharku ba da sakamakon al’amarinku! Kuma ba shi da hikima cikin abin da ya kallafa muku.
|