Imamanci Da NassiIdan bai’a ta kasance to tana karfafa imami da biyayya gareshi ne bayan an tabbatar da samuwarsa. Shin zai iya yiwuwa garemu mu ce: Bai’a sharadi ce ta inagancin biyayya ga imam, ko kuma sharadi ce ta wajabcin biyayya gareshi ta yadda zai zama idan babu bai’a ba shi da imamanci, ko kuma babu inganci ga binsa? Sai mu ce: Bai’a tana karfafa dankon wajabcin lizimtar wilayarsa da biyayya ga jagoracinsa ne, ba tana kafa ko samar da assassin asalin wilayar ba ne ko kuma ta zama sharadi na inagncin biyayya gareshi, domin biyayya da imamanci ba sun tsayu ba ne a kan bai’a ga wanda wilaya ta tabbata gareshi da nassi. Shi ya sa zamu samu cewa, Manzo (S.A.W) ya yi aiki da bai’a a lokacin rayuwarsa kamar yadda yake a fili a bai’ar Akaba ta farko, da bai’ar Akaba ta biyu, da bai’ar Gadir. Wannan sura ta bai’a da ta faru ga Manzo (S.A.W) tare da cewa wilaya ta tabbata gareshi tun kafin wannan bai’a din. Bai’ar da musulmi sukan yi masa ko rashin bai’ar su gareshi (S.A.W) a game da amsa kiransa ko jihadi ko shugabanci, ba ya canza hakkin Manzo a kan al’umma na biyayya ga al’amarin kira da jihadi da jagoranci. Haka nan shugabancin imam Ali (A.S) bayan Manzo (S.A.W) da ya tabbata a Gadir, Bai’ar da musulmi suka yi masa a rannan ba ita ce zata tabbatar masa da shugabanci ba ta fuskacin sharia’a duk da Manzo ne ya umarce su da su yi masa tun yana raye, ita wannan bai’ar ba ta kara kimar wilayarsa ta nahiyar shari’a a kan karfafa wilaya da biyayya, Kuma da dama daga malaman Ahlussunna sun tafi a kan kasancewar jagoranci yana samuwa ne ta hanyar wasiyya. Suka ce: Idan wani halifa ya yi wasiyya zuwa ga wani bayansa to bai’ar sa ta kullu domin yardar al’umma da ita ba a la’akari da ita, dalilin haka shi ne bai’ar Abubakar ga Umar ba ta tsayu a kan yardar sahabbai ba[42]. Wannan kenan, tare da cewa ba mu samu bai’a ba tsakanin Abubakar da Umar, abin da ya faru kawai ya yi wasiyya da halifanci ne kawai ba wani abu ba. Idan haka ne wanda Annabi ya yi wasiyya gareshi shi ya fi cancanta a bi ba tare da wani dalili ba a kan sabawa hakan, kuma al’amarinsa zartacce ne, kuma da wannan ne halifanci ya tabbata ga Ali bayan Manzo kai tsaye, shin al’umma ta yi masa bai’a a kan biyayya ko ba ta yi ba. Bai’a tana kasancewa ne daga alkawarin biyayya da karbar tafiyar da hukunci da tafiyar da al’amuran al’umma, wannan kuwa ba ya yiwuwa sai da bai’a, kuma Abbas ya halartowa Ali da ita sai ya ki karba sai dai a fili a gaban mutane a masallacin Annabi. Sannan da aka zo yin bai’a a kan hakan ne mutane suka yi masa bai’a, haka nan al’amarin ya kasance game da Imam Hasan (A.S), shi ya sa yayin da sauran imamai da Allah ya zabe su ga jagorancin al’umma ya zama ba a yi musu bai’a ba sai aka kange su gabarin tafiyar da hukuma da al’amuran al’umma, amma kuma wannan ba ya cire musu hakkinsu na imamanci, sha’anin al’amarinsu yana daidai da na annabawa ne da al’ummarsu suka saba musu suka hana su tafiyar da jagoranci da shiryarwa da fuskantarwa, ba tare da wannan ya cire musu matsayinsu da Allah ya ba su ba[43]. Ashe kenan matsayin bai’a a lokacin halartar imami ma’asumi ba komai ba ne sai karfafawa ga wanda jagoranci ya tabbata gareshi ta hanyar nassi. Kamar yadda bai’a ba ta iya samar da wilaya ga mutum da aka yi nassin binsa kamar Manzo ko imami, nassi ga imami yana wajabta binsa da haramcin rashin yi masa bai’a.
|