Matasa Da RayuwaLalle sun san inda aka haife su, kuma suna da alaka da wajen, don haka suke neman wurin har sai sun koma wajen; don su rayu cikinsa". Wannan malami ya sake kawo wata kissa mai ban mamaki dangane da rayuwar macijin ruwa...... Macijin ruwa ya kan yi hijira daga kogin da aka haife shi bayan ya girma, zuwa wani guri mai nisan gaske, inda zai je can ya rayu har ya mutu. Bayan isansu wannan guri da kuma haihuwa a wajen, 'ya'yayensu sukan sake shafe wannan tafiya mai nisan gaske su dawo inda aka haifi iyayensu, don su rayu a wajen. Ta haka ne dai wadannan halittu suke rayuwa. Babu shakka wannan kissa ce mai ban mamaki wacce za ta bar mu cikin tsananin tunani da kuma tambayoyin da Alkur'ani mai girma ya amsa su cikin wadannan ayoyi: "....Ubangijinmu Shi ne Wanda Ya bai wa dukkan kome halittarsa, sa'an nan Ya shiryar". (Surar Daha, 20: 50) Lalle Allah Shi ne Wanda Ya shiryar da shi da kuma ba shi irin wannan ilimi. Hakika wadannan lamurra suna bayyana mana ma'anar fadinSa Madaukakin Sarki cewa: "..Malamai ne kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa....". (Surar Fadir, 35: 28) Hakika ba za mu taba sanin Allah Madaukakin Sarki ba sai ta ilimin nan dai da Alkur'ani mai girma ya kiraye mu da mu neme shi, kamar kuma yadda ya kiraye mu zuwa ga tunani da kuma amfani da hankali wajen sanin Allah Madaukaki, sanin halittunSa da kuma fahimtar littafinSa mai girma: "Shin to, ba za su kula da Alkur'ani ba, ko kuwa a kan zukatansu akwai makullansu?" (Surar Muhammad, 47: 24)
|