Ajali KoWa'adi



[8] Gurarul Hikam: 6361.

[9] Gurarul Hikam: 4178.

[10] Hashari: 9.

[11] Nurus Sakalain: 5/285/53.

[12] Tanbihul Khawatir: 1/172.

[13] Nurus Sakalain: 5/285/52.

[14] Nurus Sakalain: 5/470/20.

Yin Kwadago (Kodago)

Kwadago ko kuma Kodago shi ne mutum ya yi aikin lada, kamar ya yi aikin gini domin a biya shi wani kudi a matsayin ladan aikinsa bisa yarjejeniyar gwargwadon kudi da yanayin aiki da yawansa ko girmansa ko adadinsa wani lokaci da lokacisa. Ubangiji madaukaki yana fada game da hakan: "Shin su ne suke raba rahamar ubangjijinka mu ne muka raba arzikinsu a tsakaninsu a duniay kuma muka muka fifita su a kan wasu da darajoji domin wasu su riki wasu 'yan aiki, kuma rahamar ubangjinka ita tafi daga abin da suke Tarawa"[1]. Da kuma fadinsa game da Annabi Musa (a.s) "Dayarsu ta ce ya baba ka dauke shi aiki domin fiyayyen wanda zaka dauka aiki shi ne mai karfi amintacce"[2]. Da wannan muna iya sanin cewa lamarin yin kwadago ko aikin lada -aikin kudi- wani abu ne wanda yake sananne tun kafi musulunci, kuma musulunci ya zo ya zartar da shi a matsayin daya daga cikin hanyoyin rayuwar mutane.

Ayoyin da suka gabata suna nuna mana cewa; Allah ya hore wa wasu mutane wasunsu, wato akwai alakar ubangida da yaronsa a tsakanin mutane ko dan kwangila da mai aiki, da shugaba da dan aiki da makamantan hakan, kuma wannan alaka ba ta iya nuna fifiko a tsakinnsu a wurin Allah sai dai tana nuna mana yadda ya sanya sassabawar mutane ta fuskanci hore musu abin duniya da zai iya kaiwa ga tsarin rayuwarsu da samun alakoki tsakaninsu, da kuma neman abin rayuwar juna daga junansu, don haka babu wani alfahari da mai kwangila zai nuna wa dan kwangila, ko kuma mai aiki ya nuna wa dan aiki, ko mai gidan haya ya nuna wa dan haya, ko mai motar haya kamar mai tadi da zai nuna wa dan tadi ko kuma fasinja ba shi da wani alfahar ko fifiko da zai nuna a kan direba. Ita wannan alaka an sanya ta ne domin a tsara musu rayuwarsu a tsakaninsu babu dadi babu ragi, don haka ne ma ake neman girmama juna a cikin wannan lamarin domin dadada alaka da kyautata ta, da kuma cika alkawura da yarjejeniyar juna.

Ta wani bangaren kuma muna ganin yadda daya ayar ta yi nuni da cewa idan zaka dauki mai aiki to ka dauki wanda yake da ilimi kan aiki da karfin yin aikin da kuma rikon amana kamar yadda aka yi nuni da ya kasance amintacce. Wadannan sharudda suna da muhimmanci a cikin aiki, kuma muna iya ganin abin da ya rusa kasashenmu na Afurka da wasu nahiyoyinma yana komawa zuwa ga wadannan lamuran, ta yadda akan dauki mai aiki domin sanayya ko dangantaka ko nasaba ko kuma ta cin hanci da rashawa, sai a sanya wadanda ba su cancanta ba a wurin wadanda suka cancanta kuma wannan tabbas yana dukusar da kasa ya lalata ta, ya kuma karya kashin bayan tafiyarta, sai aikin da ya kamata a yi shi cikin shekaru takwas ya dauki shekaru talatin ko sama da hakan, domin duk sa'adda aka yi ba daidai ba, to wannan yana nufin maimakon a yi gaba an yi baya, maimakon a yi gyara an yi barna kenan, kuma maimakon a samu ci gaba an samu ci baya kenan, da haka ne sai komai ya tsaya cik.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next