ZamaninBayyana- Faruwar fitina da yaki mai tsanani da kashe sama da mutane miliyan uku, da rushe wasu birane da wasu garuruwa da dimuwa da firgici. - Yaki da kashe-kashe a Iraki da Bagadad, kuma da mamaye ta, kuma da abubuwa masu yawa da zasu faru a Iraki da Kufa da Basara da Bagadad. - Yunwa da Fari. - Zuwan tuta tamanin zuwa yakin larabawa. (Ta yiwu tana nufin kasashe tamanin ne). - Kashe wasu daga sarakuna. - Motsin wasu mutane da gwagwarmayar neman hakki kamar Yamani, da Sayyid Khurasani, da Hashimi daga Gilana. - Yaduwar wasu cututtuka masu kisa kamar annoba. - Faruwar wasu canje-canje a sama kamar sama ta yi ja ta takure, da alamomi a rana da wata kamar bayyanar fuskar Annabi Isa (A.S) a rana da kuma faruwar iska ja da baka. - Yaduwar wuta a wasu kasashe (tayiwu yaki ne a kan mai) - Lalacewar ‘ya’yan itace a kan bishiyoyi (tayiwu saboda lalacewar yanayi da waje ne)
|