ZamaninBayyana



ZamaninBayyana

A imanin Shi'a lokacin bayyanar imam Mahadi (A.S) wani abu ne wanda yake mai aukuwa a tilas da ba shi da makawa, koda kuwa rayuwar duniya ta rage saura kwana daya ne to sai Allah ya tsawaita wannan ranar domin ya zo ya kafa hukumar adalci.

A wannan mahanga imam Mahadi (A.S) shi ne misalin kadaita Allah a duniya a karshen zamani da bayyanarsa ne sunayen Allah kyawawa zasu samu bayyanar ma’anarsu kamar: Al’waliyyu, Al’adilu, Al’hakimu, Assuldan, Almuntakim, Al’mubiru, Al’kahiru, Azzahiru, bayyanar da ba su taba yin irinta ba da can, kuma matsayin halifan Allah a bayan kasa zai bayyana a aikace[1].

Ma’anar bayyana

Bayyana a mahangar Shi'a yana da ma’ana biyu ne kamar yadda zamu kawo a kasa:

1- Futowa daga cikin hijabin shamakin boyuwa.

2- Shelanta juyin juya hali da samar da juyin duniya mafi girma a kan zalunci.

Dukkanin wadannan ma’anoni guda biyu suna gaskata ga Bakiyyatul-Lah imam Mahadi (A.S), don haka zai zama shugaban duniya a zahiri a karshen zamani bayan fitowa daga shamakin labulen boyuwa da samar da juyin juya hali a kan zalunci a fili[2].

Amma game da yanayin duniya kafin bayyanarsa zamu iya kasa ruwayoyin da suka zo daga Shi'a kashi biyu kamar haka:

A- Ruwayoyin da suka zo suna nun alalacewar dan Adam a dabi’unsa da matsaloli da rushewar kyawawan dabi’u ta yanda zai zama mafi kaskanci daga dabbobi. Da yaduwar zalunci da fasadi a siyasance da al’ada da tafiyar da al’amuran al’umma, da tsaro da kekashewar zukata wanda daga karshe mutum zai tuke da kaiwa ga siffar kura da kyarkeci. A lokacin yanke kaunar samun gyaran yanayin duniya zai bayyana a fili.

Wadannan ruwayoyi zamu iya kasa su kamar haka:

1- Ruwayoyi mutawaitirai da suke nuna cikar duniya da zalunci gaba daya wadanda suke tawaturancinsu ya zo daga Sunna da Shi'a duka[3].

2- Ruwayoyin da suke nuna faruwar rikici mai yawa da rashin zama lafiya.



1 2 3 4 5 next