Tattalin Arzikin IyaliHaka gamammun asasan kasafin iyali da kashewa da ciyarwa ke iyakantuwa cikin tsaikoki biyu na doka, tarbiyya da fuskantarwar halayya; su ne tsaikon zamantakewa da tsaikon iyali. Kuma gudummawar mace cikin gudanar da tattalin arzikin gida na bayyana wajen kiyayewarta ga kudaden iyali da lurar ta da daidaito wajen kashewa da kayayyakin kyale-kyale da (kiyayewa daga) nuna takama da son a sani wajen kashe kud'i. Uwa na iya bayar da wani kashi daga mashigar iyali ta ragewa namiji nauyin basussuka ta hanyar rage kashe kud'i da yin tasiri a kan yara, kai! a kan miji ma ta hanyar tsara siyasar ciyarwa madaidaici ga iyali, irin wanda ke daidai da bukatu da gwargwadon abin da ake kashewa. Yawan kashe kud'i da almubazzaranci a iyali na barin tasirinsa ba kawai a cikin iyali ba, har ma a kan yanayin tattalin arzikin mutane da gwamnati, domin farashin kayayyakin masarufi za su hauhawa a kasuwa saboda hauhawar ciyarwa da kashe kud'i, wad'anda ke haifar da fad'uwar darajar kud'i da tashin kayayyki; da haka sai yawan talauci ya karu, iyalai su rika nutsuwa cikin basussuka da matsalolin zamantakewa; kamar yadda takardun kud'i za su yawaita, sai matsalolin siyasa, tsaro da d'abi'u su kunno kai a sakamakon tabarbarewar yanayin tattalin arziki a cikin al'umma. Wayar da kan mace da kebance wasu darussa na masamman cikin tsare-tsaren karantarwa game da tattalin arzikin gida a Musulunci, da wayar da kan mace a kan daidaita wa wajen ciyarwa da tsara kasafin iyali, duk suna taimakawa wajen gina yanayin tattalin arziki da ceto shi daga matsaloli, masamman ma matsalar tsadar kayayyaki da rashi ga talakawa. Da wannan mace na bayar da gudummawa wajen ginin al'umma ta hanyar fuskantarwa da tsarin tattalin arzikin iyali, da daidaitawa wajen ciyarwa ta hanyar bin tsare-tsaren AIKur'ani da kiransa mai hikima. Kuma don mace ta sauke nauyin da ya hau kanta a matsayinta na mai lura da gidan mijinta, kuma wadda za a tambaya a kan shi kamar yadda ya zo cikin bayanin Annabi mai girma (s.a.w.a.). YIN AIKI A SHARI'AR MUSULUNCI Hakika shari'ar Musulunci ta yi kira zuwa ga yin aiki, ta kuma kara kwadaitarwa a kan shi da abin da ba ya bukatar kari a cikin nassosi da karantarwa da matsayi na aikace. Daga cikin su akwai fadar Allah Madaukaki: " (Allah) Shi ne Wanda Ya sanya kasa horarriya, saboda haka ku yi tafiya a cikin sassanta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma makoma zuwa gare Shi ne (kawai)". Surar Mulki, 67:15. Haka nan akwai fadarSa Madaukaki: "Sannan idan aka idar da Salla, sai ku bazu cikin kasa ku nemi falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa tsammaninku ku rabauta". Surar .Tuma'ati, 62:to. Haka nan akwai fadarSa:
|