Tattalin Arzikin IyaliMACE DA TATTALIN ARZIKIN IYALI
Daga cikin manyan matsalolin da suka addabi al'umma,akwai matsalar kudi da hanyoyin shiga ga mutane; da aunawa tsakanin abin da ke shigowa da wanda ake kashewa; hakan na faruwa a tattalin iyali da zarafinshi na kudi wajen ciyarwa da hada-hadar gida. Barnar abinci, abin sha, kayan kwalliya, sutura, mazauni da sauran hidimomi na daga mafi hadarin matsalolin dan Adam; domin akwai almabazzaranci da kashe kudi ba tare da basira ba da ke gurgunta tattalin arzikin iyali, al'umma da gwamnati, wadanda so tari ba sa dacewa da hanyoyin shigar iyali da abin da yake samu. Saboda tsara ma'aunin tattalin arzikin al'umma ne Musulunci ya yi kira zuwa ga daidaito wajen ciyarwa, ya kuma haramta barna kamar yadda ya yi hani ga, matsolanci, kwauro da rowa. Daya daga cikin manyan matsaloli wajen ciyarwa ita ce matsalar biyan bukatun iyali da kasafin sa, wadanda mace ke da babban alhakin da ya hau kanta wajen tsara shi da iyakance dabi'arsa. Hakika shari'ar Musulunci ta sanya gamammun asasai don tsara ciyarwa daga sakewarsa; kamar yadda ta tsara iyakoki na asasi wajen biyan bukatun iyali da kasafinsa a iyakance; daga irin wannan za mu ambaci abin da Allah Ya siffanta "Bayin Mai rahama° da shi a matsayin wani madaukakin abin koyo wajen tsari da lizimci, wanda kuma ya bayyana mikakken tafarkin wajen ciyarwa irin wanda aka yi kira ga mutane su yi riko da shi, Allah Madaukaki Yana cewa: "..Kuma wad'anda idan suka ciyar ba sa almubazzaranci kuma ba sa yin kwauro, sai dai ya kasance tsaka-tsaki ne". Surar Furkani, 2s:67. A wani wuri kuma AIKur'ani na hani da almubazzaranci kuma yana tsanantawa a kan haka da fad'arsa: "...kuma ku ci ku sha, amma kuma kada ku yi almubazzaranci, hakika shi Allah ba Ya son masu almubazzaranci". Surar A'arafi, 7:31. Da fadarsa: "Kuma ku bai wa makusanci hakkinsa, da miskini da matafiyi; kada ka batar (da dukiya) ta hanyar almubazzaranci. Hakika almubazarai dangin shedanu ne; shedan kuwa mai yawan kafirce wa Ubangijinsa ne". Surar Isra'i, 17:26-27. "Kuma kar ka kunkunce hannuwanka a wuyan ka (wato yin kwauro), kuma kar ka shimfida gaba daya (wato yin almubazzaranci), sai ka wayi gari abin zargi (saboda kwauro), mai nadama (saboda almubazzaranci)". Surar Isra'i, 17:29. "Kuma ku zaunar da su (mata) ainda kuka zauna daidai halinku, kuma kar ku cutar da su (da kwauro) don ku kuntata musu; idan kuwa sun kasance masu ciki ne, sai ku ciyar da su har sai sun sauke abin da ke cikinsu; sannan idan sun shayar muku (da `ya'yanku), sai ku ba su ladaddakinsu, kuma ku daidaita tsakaninku da kyautatawa; idan kuma abin ya gagara daidaitawa, sai wata (matar) ta shayar masa (da jaririn). Ma'abucin yalwa ya ciyar daga yalwarsa, wanda kuwa aka kuntace masa arzikinsa sai ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi, Allah ba Ya dora wa rai face abin da Ya ba ta, da sannu Allah Zai sanya sauki bayan matsi". Surar Dalaki, 65:6-7.
|