MACE DA WAYEWAR DUNIYANCIHaka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar kasar Iran mai suna lddila'at ta bayar a adadinta na 20,401 daga kamfanin dillancin labaran Iran da ke birnin Rom na kasar Italiya, cewa: "Matsalar halayyar rashin tausayi na kara matufcar tsananta a tsakanin iyalan Italiyawa, domin halin kashe iyaye a hannun `ya'ya da kashe 'ya`ya a hannun iyaye ya karu fiye da yadda ya kasance a da can. Haka wata jaridar Kasar Italiya, a adadinta na baya-bayan nan, ta dauko wani rahoton Kididdigar shekara-shekara na kungiyar Eruospas cewa: cikin watanni goman farkon na shekara ta 1994, an rubuta halin rashin tausayi har 192 a cikin iyalan Rasar Italiya, wadanda 129 daga wannan adadi suka Kare da kisa. Kamar yadda wannan rahoto ya nuna, irin wannan nau'i na rashin tausayi a shekara ta 1993 adadin shi ya kai 112, wanda kusan wannan adadin ya kare da halin kashe-kashe. wani abu, da ya zama dole a nuna shi ne cewa kimanin kashi 40 bisa dari na laifuffukan iyali ya faru ne a arewacin Italiya, kuma kashi 40.8 bisa dari daga cikinsu sun faru ne a kudancin kasar, alhali kashi 16.1 bisa dari ya faru a tsakiyar kasar. Kuma mafi yawan kashe-kashen iyali da aka yi a shekara ta 1994 sun faru ne a lardin Lombardi da ke arewacin Italiya". Haka nan jaridar 'Jumhuri Islami', a adadinta na 4,485, fitowarta shekara ta 1994, ta bayar da rohoton cewa:'Mujallar Epidemiology (ilimin annoba) da ke Karkashin hukumar lafiya ta duniya (WHO), a adadinta na 11, na shekara ta 1993 ta rubuta alkaluman Kididdiga na karshe da ya Kunshi adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki (AIDS) a duniya baki daya, inda aka rarraba alkaluman daidai da yankunan duniya dabam-dabam. Alkaluman na nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar kan jiki da suka tabbata ga wannan hukuma har zuwa shekara ta 1993, ya kai kimanin 718,893. Kimanin 371,086 na wannan adadi na wadanda suka kamu da cutar Kan jiki sun fito ne daga nahiyar Amirka, yayin da kimanin 247,577 suka fito daga nahiyar Afrika, kimanin 92,482 kuwa sun fito ne daga nahiyar Turai, adadin da ya kai 4,188 sun fito ne daga Australiya, 3,561 kuwa daga nahiyar Asiya. Wan aka bi kasa-Kasa kuwa, Kasar da ta fi kwasan adadi mai yawa ita ce Amirka, wadda ta kwashe adadin wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta kimanin 289,320, sai kuma kasar Tanzaniya da ke biye mata da kimanin 38,719, sai Kasar Birazil mai 36,481, sai Kenya da 31,185, sai Uganda mai 34,611, sai kuma Biritaniya mai 26,955, sai Faransa mai 24,226, sai kuma kasar Zaire mai 21,008, sai Spain mai 18,347, sai Italiya mai 16,860, sai Congo (Brazavill) mai 14,655, daga nan sai sauran kasashe su biyo baya. Kamar yadda za a iya lura, ba kawai kasar Amirka na matsayi na daya ba ne ta fuskar adadin wadanda suka kamu da cuta mai karya garkuwa jiki, a'a har ma akwai sabani mai yawan gaske tsakanin ta da Kasashen da ke biye mata. Kuma idan muka dauki wadannan alkaluma na adadin dari, za mu sami wadanda suka kamu da wannan mummunan cuta a kasar Amirka sun kai kashi 40 bisa dari na dukkan wadanda suka kamu da ita a kasashen duniya 150, wannan kuwa duk da cewa adadin mazauna Amirka bai wuce kashi 5 bisa dari na dukkan al'ummar duniya ba'. Haka nan ya zo cikin wani rahoto da jaridar Ittila'at ta kasar Iran ta kawo, a adadinta na 20,482, fitowarta ta 21 ga watan Maris na shekara ta 1995, daga wakilinta a Madrid ta kasar Spain, inda yake cewa: "A shekara ta 1995 kashi 72 bisa dari na Rananan yara na raye ne a KarKashin ubanninsu, amma yanzu kimanin kashi 60 bisa dari daga cikinsu suna raye ne ba tare da ubanni ba. Yawan saki da fitinun uwaye sun sa maza sun gudu daga gidaje. Marubucin nan dan Kasar Amirka (David Blanc Horn), bayan ya bayyana wadancan alKaluman Kididdiga a cikin wani littafi na shi, ya kuma bayyana cewa: "Samun iyaye maza na gari na buKatar samun kyakkyawan misali na mata (wato yana bukatar samun mata na gari), wannan shi ne dalilin gudun iyaye maza daga gidajensu a Amirka.' Haka nan wakilin jaridar Faes ta Fcasar Spain, a wani rahoto na shi da ya bayar daga Amirka, ya bayyana cewa: Himmatuwa mai yawa da matan Rasar Amirka ya kare da cutar da ubanni da haramtawa `ya `ya inuwar ubanninsu". A wani rahoto da jaridar Itiila'at, a adadinta na 20,407, fotowar ranar 31 ga watan Yulin shekara ta 1995 ta dauko daga ofishin kamfanin dillancin labaran Iran (IRNA) da ke London game da yanayin da kananan yara ke cikin a Biritaniya, am bayyana cewa: "Majalisar Dinkin Duniya, a wani rahoto nata, ta yi kakkausar suka a kan yanayin da yara ke ciki a Biritaniya, da kuma dokoki da tsarin lura da yara a wannan kasa. Rahoton, wanda hukumar kiyaye hakkokin yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, ya nuna cewa dokokin da ake amfani da su a kan abin da ya shafi lafiya da ilimin kananan yara da shigar da su cikin al'umma a Biritaniya, ba a yi la'akari da cewa ya wajaba dokokin su lura da amfanonin yaran ba. Masana a hukumar kiyaye hakkokin yara ta Majalisar Dinkin Duniya na ganin cewa dokokin da suka kebanci kananan yara a Biritaniya sun fi mayar da hankali a kan yin ukuba da kulle yara da balagaggun matasan da suka karkace. Daga cikin wuraren da ake suka a cikin wannan rahoto akwai karuwar yawan kananan yara da ke rayuwa cikin halin talauci a Biritaniya, da karuwar alkaluman rabuwar aure, da raguwar tallafin hukuma ga matalautan iyalai, da karuwar yawan yara da samari da ke sake suna kwana a tituna. Haka nan masu rubuta rahoton sun bayyana damuwarsu da mummunar mu'amala da amfani da miyagun kwayoyi da fyade da ke fuskantar kananan yara. Kamar yadda majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana, rahotannin majalisar game da yanayi kananan yara a kasashen Sweden, Norway da Denmerk sun yi soke-soke kamar irin na rahoton kasar Biritaniya".
|