MACE DA WAYEWAR DUNIYANCI



MACE DA WAYEWAR DUNIYANCI

Karanta tarihin al'ummu da kasashe a tsawon zamunansu, yana fito mana da wahalhalun mace, kuntata mata da takura mata.

Babu wani tsari ko akida da ya yaye wa mace mayafin zalunci da kuntatawa in ba ka'idojin Allah da suka hadu da mafi kyawun surarsu a sakon Musulunci madawwami ba.

Kafin mu bayar da bayani game da kimar mace, hakkokinta da matsayinta mai ban sha'awa a Musulunci, yana da kyau mu kawo wasu alkaluman kididdiga wadanda

ke magana a kan wahalhalun mace da masifun da ta sha a karkashin wayewar duniyanci na zamani karkashin jagorancin Amirka da kasashen Turai, wadanda ke daga taken 'hakkokin mace'.

Alkaluman kididdiga na ta'akidi a kan cewa, dan Adam din da ya ji jiki a karkashin wannan wayewa, kuma ya zama bawa da na'urar jin dadi shi ne: Mace. Ga wasu daga cikin alkaluman kiddidiga na cewa:­

"Wani rahoto da kamfanin dillacin labaran kasar Faransa ya kawo ya bayyana cewa: kashi 70 bisa dari na mutane biliyan 1.3 da ke raye a cikin halin mugun talauci a duniya su ne mata, kuma akwai kimanin mata biliyan 2.3 da ba su iya karatu da rubutu ba a duniya. Haka nan kashi uku bisa hudu na daukacin matan kasashen Norway, Amirka, Holland da Newzaland na fuskantar hare-haren fyade. A Amirka kuwa, cikin kowadanne dakikoRi 8 mace daya na fuskantar mummunar mu'amala; haka cikin kowadanne dakikolti 6 ana sace mace daya"8

Rahoton ya kara da cewa:­ Kimanin mata rabin miliyan daya ke mutuwa a kowace shekara saboda ciki da suka dauka da cutukan shi, kuma kimanin kashi 40 bisa dari na wannan adadi yan mata matasa ne. Kuma albashin mata miliyan 828 da ke aiki a fagagen tattalin arziki ya fcaranta daga albashin maza da abin da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa kashi 40 bisa dari, kuma irin dan tagazawar nan na bankuna da ake ba ma'aikata a duniya ba sa samun fiye da kashi 10 bisa dari na wadannan agaje-agaje".9

Haka nan ya zo cikin wani rahoton cewa:­

"A bisa wani bincike da ma'aikatar adalci ta kasar Amirka ta aiwatar, an gano cewa adadin sace mutane ko yunkurin sace mata na faruwa a Amirka har sau 310 a kowace shekara, wannan kuwa ya ninka alkaluman da hukumar 'yan sandan cikin Amirka ta F.B.I. ta bayar."lo

Kuma kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga Washigton ya bayar, a kowace shekara akwai halin yi wa mata fyade har sau rabin miliyan a Amirka; alhali kuwa hukumar 'yan sanda ba ta bayar da sanarwar adadin samuwar sace (mata) ko yunkurin sace su a Amirka ba face dubu 140, kamar yadda alkaluman kididdigar hukumar F.B.I. ya bayyana.



1 2 3 next