Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai



Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ina Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un

A wannan karon ma hannayen makirai (makiya) masu son haifar da fitina sun sake nufo al'ummar musulmi da kuma aikata irin wannan danyen aiki.

Hakika wannan danyen aiki na tada bama-bamai a haramin Samarra da keta hurumin hubbaren Imamain al-Askariyayn (Imam al-Hadi da Askari) amincin Allah Ya tabbata a gare su ba wai kawai zukatan 'yan shi'a ne ya sosa ba face dai dukkanin al'ummar musulmi masoya zuriyar Ma'aikin Allah (s). Wannan wani makirci ne ga duniyar Musulmi da manufar hakan ita ce haifar da yakin basasa a kasar Iraki da fitinar mazhaba da rarrabuwa tsakanin Musulmi.

Ko shakka babu kungiyoyin leken asirin 'yan mamaya da yahudawan sahyoniya su ne suka tsara wannan danyen aiki ko da kuwa sauran gyauron 'yan jam'iyyar Ba'ath na Saddam (Husain) ne ko kuma 'yan kungiyar wahabiyawa ko Salafawa wadanda aka ruda ne suka aikata shhi (a zahiri).

A kokarin da suke yi na cin kafafun gwamnatin da al'ummar (Iraki) suka zaba da kuma samar wa mamayan da suke yi halalci ya sanya 'yan mamayan share hanya ga 'yan ta'adda wajen aiwatar da ayyukan ta'addancinsu da rura wutar fitina tsakanin musulmi.

Shekara da shekaru wannan harami mai tsarki ya yi a garin Samarra tsakankanin 'yan Ahlussunna, babu wani lokaci da wani ya taba keta hurumin wannan waje mai tsarki. Amma a halin yanzu a lokacin 'yan mamaya wannan shi ne karo na biyu da aka aikata wannan danyen aiki ga wannan waje mai tsarki. Babu yadda 'yan mamaya za su iya wanke kansu daga wannan danyen aiki.

Don haka dole ne 'yan'uwa 'yan Ahlussunna da 'yan Shi'a su yi hankali kada su fada tarkon wannan makirci na makiya. Dole ne dukkan al'ummar Musulmi a duk inda suke a duniyar Musulmi su yi taka tsantsan kan wannan bakar siyasa ta rarraba kansu da makiya suke gudanarwa.

A halin yanzu a kasashen Iraki, Palastinu, Labanon da sauran kasashen musulmi makiya na nan na kokarin haifar da fitina da rikici na mazhaba, kabilanci da kungiyanci tsakanin Musulmi da kokarin sanya su fada tsakaninsu. Bai kamata musulmi su taimaka musu wajen cimma wannan bakar manufa tasu ba.

Dole ne malaman Ahlusunna su yi Allah wadai da wannan danyen aiki da barranta daga wadanda suka aikata wannan danyen aiki, su kuma malaman Shi'a dole ne su kirayi mabiya Ahlulbaiti (a.s) da su kwantar da hankulansu, dukkanin malaman musulmi su kirayi mabiyansu zuwa ga so da kaunar sauran 'yan'uwansu.

Ina taya mai girma Baqiyatullah, rayukanmu su zamanto fansa gare shi, juyayin wannan babbar musiba da sauran musibun al'ummar musulmi.

Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya kare al'ummar musulmi daga sharrin azzalumai ma'abuta girman kai da kafiran (duniya).



1