Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma



 A wani wurin ciki Kur’ani Allah madaukaki yana zargin munafukai da cewa duk lokacin da aka neme su da su je wajen ma'aiki don ya nema musu gafara sai su kiya: “Idan a ka ce musu ko zo Manzo ya nema muku gafara, sai su juya fusakunsu (don nuna rashin amincewa) zaka ga suna kin maganarka suna masu nuna girman kai. “[15]

 Shehin malamin nan kuma AhlusSunna, Takiyyuddeen Subki, Ya yi imani da cewa: Msuslmi a wannan lokacin ma tare da amfani da wannan aya suna iya zuwa wajen Manzo su nemi gafararsa kuma Allah ya gafarta musu. Ya kara da cewa duk da yake wannan aya ta shafi lokacin da Manzo yake a raye ne, amma neman gafara ta hanyarsa bai kebanta da lokacin da yake a raye ba. Saboda wannan wani matsayi ne wanda aka bai wa Manzo (s.a.w) don haka sakamakon rabuwarsa da duniya wannan matsayi ba zai kau ba.

 Mai yiwuwa a ce: Wannan abin da ya zo a cikin wannan aya da muka ambata a sama, ya kunshi nuna matsayi da daukaka ta Manzo ne kawai, amma aiwatar da wannan ya kebanci lokacin rayuwarsa ne kawai, amma ba lokacin da baya duniya ba, ta yadda alakarmu da shi ta yanke.

 Amma wannan magana sam ba abin karba ba ce, domin kuwa dalilan da zamu ambata a nan gaba suna bayyana cewa rasuwar Manzo sam ba ta da wani tasiri akan wannan al'amari, don haka mutuwa da rayuwarsa babu wani bambanci duk daya ne:

1-Mutuwa ba tana nuna karshen dan Adam ba ne, mutuwa wata sabuwar kofa ce don shiga wata sabuwar rayuwa kuma duniyar da duk abin da yake a ckinta ya fi abin da yake a duniyar da ta gabata ga rayuwar dan Adam, saboda haka mutum rayayye ne a waccan duniya yana gani kuma yana ji. Musamman shahidai wadanda bayan sun dandana shahada zasu cigaba da karbar ci da sha daga Allah madauakin sarki, kuma suna cikin jin dadi na musamman ta hanyar ruhinsu. Saboda haka zamu yi bayani akan wannan a nan gaba a cikin bahasin rayuwar barzahu. [16]

2-Ya zo da yawa a cikin ruwaya cewa: Salatin da musulmi suke yi wa Manzo akwai mala'iku na musamman masu isar da wannan salati zuwa ga Manzo (s.a.w) don haka duk inda mutum yake idan ya yi wa Manzo salati zai isa zuwa ga manzon. Kamar yadda yake cewa: “Ku yi mani salati, salatin yana isa zuwa gare ni daga duk inda kuke”[17]

3-Musulmi a wajen tahiyar salla an umurce su da su yi wa Manzo sallama, sannan su yi masa gaisuwa, “Assalamu alaika ayyuhan nabiyu warahamatullahi wa barakatuhu” Wannan gaisuwa ba wai kawai an umurci musulmi ba ne da su yi ta zuwa ga Manzo amma shi ba ya jin abin da suke yi, Manzo yana raye kuma yana sauraren mu lokacin da muke yi masa salati.

 Wadannan abubuwan da muka fada a sama suna nuna cewa Manzo yana raye a rayuwar barzahu, sannan yana da alaka da mu kuma yana jin abin da muke yi. Sannan yana jin rokonmu kuma yana biya mana bukatunmu a lokacin da ya dace. Saboda haka a nan ya kamata mu ce wadannan ayoyi da muka yi bayani a sama, Suna da ma'ana mai fadi, saboda haka yanzu ma suna kiranmu da ziyarar Manzo a kabarinsa kuma mu nemi gafara kuma ya nema mana gafara ga Allah, sannan mu nemi bukatunmu daga gareshi. Saboda haka ya zo a cikin ziyarar Manzo da ake karantawa a haraminsa cewa mai ziyara ya nemi gafarar Allah ta hanyar manzon tare da kula da ma'anar ayar da muka yi bayani a sama. Saboda haka ziyarar Manzo ba wani abu ba ne sai kawai yin salati ga Manzo da kuma neman bukatu da gafarar Allah ta hanyar mazon. Saboda haka wadanan ayoyi na sama suna iya zama sheda akan inganci da mustahabbacin ziyayarar mazo (s.a.w)

 Wata sheda kuma a kan wannan magana ita ce, bayan rasuwar Manzo wani balarabe ya shigo Madina yana karanta wannan aya da muka ambata, sai ya ce: “Na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina kuma ina mai neman ceto gareka zuwa ga Ubangijina”[18]

 Sannan muhimmin abu kamar yadda Subki yake cewa: Kiran al'ummar musulmi da su ziyarci Manzo kuma su nemi gafara da bukatunsu daga gareshi wata alama ce ta karrama Manzo da girmama shi. Kuma tabbas wannan girmamawa ba ta kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda girma da mukamin ruhinsa a wajen Allah wani abu ne wanda bai mai shakku a kansa kuma madawwami ne, saboda haka bai kebanta da wani zamani ba sabanin waninsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next