Ziyarar Kabarin Manzo Mai GirmaMawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma A Mahangar Malaman Hadisi Da Fikihu

Tare da bibiyar maganganun manyan malaman hadisi da malaman fikihu, zamu ga yadda kodayauhse malaman musulunci suke karfafawa a kan kasantuwar ziyarar kabarin Manzo a matsayin mustahbbi mai karfi, Sannan suna kiran mutane zuwa ga ziyarar kabarin Manzo mai tsarki.

 Takiyyuddin Subki Shafi’i (ya rasu shekara ta 756) Wanda yake daya daga cikin manyan malaman karni na takwas. Yayin da yake kalu balantar akidun Ibn Taimiyya wanda yake inkarin ziyarar kabarin Manzo (s.a.w), ya rubuta littafi mai suna (shifa’us sikam fi ziyarati khairil anam) a cikin wannan littafi ya yi kokari ya tattaro ra’ayoyin malaman AhlusSunna tun daga karni na hudu har zuwa lokacinsa a kan wannan al’amari, a cikin wannan littafi nasa ya yi kokarin tabbatar da nuna cewa ziyarar kabarin Manzo yana daga cikin abubuwan da aka sallama a cikin fikihu a kan cewa mustahabbi ne. Manyan malaman hadisi da fikhu sun ruwaito hadisai daban-daban a kan kasantuwar ziyar Manzo a matsayin mustahabbi, sannan suka ba da fatawa a kan hakan. [1]

 Allama Amini wanda yake bincike na wannan zamani kuma mai tsanantawa wajen bincikensa (1320-1390), a cikin babban littafin nan nasa “Algadir” Ya yi kokari wajen cike abin da ya ragu a kan wannan magana ta ziyar kabarin Manzo, inda ya yi kokari ya zo da ra'ayoyin malamai arbai’n wadanda suka hada da malaman hadisi da na fikhu har zuwa malaman zamaninsa.[2]

 Wannan marubuci shi ma ya yi kokari ya samo wasu daga fatwoyin da ba su zo ba a cikin wadancan Littattafan guda biyu da muka ambata. Ta yadda ya kawo su a cikin wani karamin littafi da ya rubuta a cikin harshen larabci.

 Kai har da babban mai fatawar Kasar Sa’udiyya wato sheikh Abdul Aziz Bn Baz ya ba da fatwa a kan mustahabancin ziyarar kabarin Manzo mai girma.[3]

 Kawo dukkan maganganun malamai a kan wannan al’amari, ba zai yiwu ba a wannan wuri, saboda haka kawai zamu wadatu da kawo wasu daga ciki ne kawai kamar haka:1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next