Shi'anci Da Shi'a



Haka ne, hakika ziyarar kaburburan imamanAhlul Baiti (A.S) da abin a ake fada na tarihinsu, da matsayinsu na jihadi tana tuna wa zuriya masu zuwa abin da wadannan masu girma suka yi saboda ci gaban musulunci da musulmi na sadaukarwa, kamar yadda kuma wannan yana karfafa su ta hanyar sanya musu ruhin sadaukarwa da sadaukantaka, da zabin wasu a kansu atafarkin Allah.

Wannan al'amari aiki ne na hankali damutuntaka, mu sani al'ummu suna dawwamar da ambaton manyansu da suka kafa musu ci gabansu, suna kuma raya ambatonsu ta kowace hanya, domin wannan yana sanya musu alfahari da jin karfi, kuma yana dada musu janyo hankalin al'ummu zuwagaresu da kuma ci gabansu.

Wannan shi ne abin da Kur'ani ya so manayayin da yake karfafa mana matsayin annabawa da waliyyai da salihai da kumaambaton kissoshinsu.

31- Shi'a suna neman ceton annabi daalayensa, kuma suna tawassuli da su (A.S) domin neman gafarar zunubansu, da biyan bukatunsu, da ceton marasa lafiyarsu, domin Kur'ani mai girma ya ba su damar haka, kuma ya yi kira zuwa ga hakan, yayin da yake cewa: "Da ma yayin da suka zalunci kawukansu sun zo maka, sai suka nemi gafarar Allah, sai manzu ya nema musu gafara, to da sun sami Allah mai yawan karbar tuba, mai yawan rahama[18].

Kuma ya ce: "Da sannu ubangijinkazai ba ka sai ka yarda"[19].Wannan kuwa shi ne matsayin ceto.

Yaya kuwa za a ce Allah ya ba waannabinsa matsayin ceton masu sabo sannan kuma ya ba shi matsayin wasila da biyan bukatar masu bukatu, sannan kuwa sai ya hana mutane neman wannan ceton,ko kuma annabi ya haramta neman hakan?!

Shin Allah bai ba mu labarin 'ya'yanannabi Ya'akub (A.S) ba yayin da suka nemi ceton babansu suka ce masa: "Ya babanmu ka nema mana gafarar zunubanmu, mu mun kasnace masu kuskure ne"[20]. Amma wannan annabi ma'asumi mai girma  bai hana su ba, kuma ma ya nema musu gafara yana cewa: "Da sannu zan nema muku gafarar ubangijina"[21].

Ba yadda za a yi wani ya yi da'awar cewaannabi da imamai (A.S) matattu ne, don haka neman addu'a a wajensu ba ya amfani. Domin kuwa annabawa rayayyu ne musamman annabi da ubangiji madaukaki ya fada game da shi cewa: "Haka nan muka sanya ku al'umma madaidaiciya domin ku kasance sheda a kan mutane, kuma manzo (S.A.W) ya kasance sheda akanku"[22].

Ya ce: "Kuma ka ce: Ku yi aiki, dasannu Allah da manzonsa da muminai zasu ga ayyukanku"[23].

Wannan aya tana gudana kuma mai ci gabace har zuwa ranar kiyama kamar gudanar rana da wata, da ci gaban juyawar dareda rana.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next