Iyaye da ‘Ya’yansu



Alakar Iyaye da â€کYa’yansu

Ubangijinka ya hukunta cewa kada ku bauta wa (kowa) sai shi, kuma ku kyautata wa iyaye…[1]

Ya ku wadanda suka yi imani ku kare kawukanku da iyalenku daga wuta…[2]

A cikin dukkan fadin duniya gaba daya akwai bukatar samuwar dokoki domin cigaban samuwar dan Adam wanda yake larure ne ga kamalar dan Adam. Wadannan dokoki suna iya tsara rayuwar mutum akansa da kuma acikin alakokinsa da sauran â€کyan Adam. Amma sanannan abu ne cewa mafi kusancin alakoki da tasiri su ne wadanda suke tsakanin gida daya kuma suke tsara tsakanin iyali. Kuma mafi girmanta ita ce wacce take tsakanin uwaye da â€کya’yansu, don haka ne ma a cikin wannan rubutu takaitacce zamu kawo wasu bayanai game da hakan.

Kuma tabbas idan aka samu kiyaye wannan alaka mai girma to za a samu kamala da gina iyali na gari, kuma daga karshe duniya kenan wacce daga daidaikun gidaje take haduwa zata kasance cikin kamala da sa’ada.

Bayan cewa; kiyaye hakkokin da suke tsakanin iyaye da mahaifa wani umarni ne na Allah da ya saukar da shi a littafin mai daraja na kur’ani mai girma, haka nan kuma wasu dokoki ne da zasu tsara wa duniya hanyar kai wa ga kamalarta, domin idan aka kiyaye wannan alaka mai girma, to za a sami al’umma mai cigaba ta kowane janibi. Kuma tarihin wannan alaka tsakanin iyaye da â€کya’yansu yana koma wa ne zuwa ga farkon samuwar dan Adam, kuma abu ne na fidirar dan Adam na kyautata wa ga mai ni’ima da kuma son na jikinsa.

Idan ba a samu kiyaye wannan alakoki ba, to maimakon samun al’umma saliha sai a samu al’umma asharariya da zata kama hanyar rushewa warwas.

A cikin al’adun musulunci an yi umarni da kiyaye wannan alaka umarni mai tsanani bayan kare hakkin Allah madaukaki, kuma ayoyi da yawa da ruwayoyi sun yi nuni da wajebcin kiyaye wannan alakoki. Idan an samu iyaye da suka tarbiyyatar da â€کya’yansu tarbiyya sahihiya to lallai wadannan â€کya’ya zasu kai ga daraja ta kamala mafi kololuwa, kuma zasu samu kaiwa ga kamalar da ake bukata ga dan Adam. Kuma tabbas irin wadannan â€کya’ya su ne kawai suke iya kiyaye hakkokin iyayensu da na al’ummarsu da suka hau kansu, kuma su ne wadanda idan suka riki kasa zasu tsayar da kyawawan dabi’u da gyara da kawar da barna daga kasarsu. Idan kuwa iyaye ba su tarbiyyantar da â€کya’yansu ba to duk wani abu da ya haifu daga garesu na daga barna a bayar kasa ba zai taba zamantowa abin mamaki ba.

Iyaye su sani â€کya’ya amana ce a hannunsu da Allah ya damka musu ita, idan ba su kiyaye wannan amanar ba, to su sani sun kauce wa hanya madaidaiciya. A cikin wannan bahasi namu zamu fara da binciken hakkokin yara akan iyayensu, sannan sai mu shiga na iyaye kan â€کya’yansu, domin idan aka fara samun kamalar kiyaye hakkoki ta janibin iyaye, to yana da sauki a samu kiyaye na iyaye a gun â€کya’yansu.

Karin bayani

Abisa dabi’ar mutum yana da son kamala wacce take kunshe a cikin ransa, kuma wannan kamalar tana bukatar samar da wasu dokoki da ka’idojin da zasu daidaita da tsara wa dan Adam motsinsa da ayyukansa na kashin kansa da na daidaiku da na jama’a da alakokin da yake tsakaninsu gaba daya cikin jimilla domin kaiwa gareta, kuma kamar yadda muka sani babu wata alaka da tafi kusa da ta mahaifa da â€کya’yansu, don haka ne ma muka ga ya dace mu kawo wannan al’amari da wani bayani takaitacce domin amfanar da al’ummarmu, da tunatar da ita, da kuma nuna mata hanyar da ya dace wajen yin alaka da manyan gobe, da kuma yadda ya kamata a girmama â€کyan jiya.

Mun riga mun yi nuni da cewa alakar â€کyan Adam musamman ta â€کya’ya da mahafansu wata aba ce da ta faru tun farkon samuwar dan Adam din, kuma wannan ba yana nuna komai ba ne sai abin da yake kunshe cikin fidirar bil-adama. 



1 next