Iyaye da ‘Ya’yansu



A addinin musulmi madaukaki mai daraja an yi nuni da wannan al’amari muhimmi da aka gwama shi da biyayya ga Allah madaukaki, kuma aka yi gargadi mai tsanani da nuni da wajebcin kare kai daga wuta da kuma tsamar da iyalai daga fadawa cikin fushin azabar Allah, kuma sananne abu ne cewa; babu wani da ya fi kusanci da hakki mai nauyi a cikin iyali fiye da â€کya’ya, kuma yin tarbiyya garesu yana iya kai duniya dan Adam ga gaci da mafita daga dukkan bala’o’in da musibun da ta fada, musamman a wannan zamani da ake bukatar gyara dan Adam da tsamar da shi daga halaye na dabbanci da fifita kayan alatu da tarkacen duniya akan mutumtaka da halaye kyawawa.

Kuma lallai mun sani a fili yake cewa; babu wani wanda zai iya yin wannan aiki koda kuwa hukuma ce mai karfin gaske inbanda iyaye da suke sane da sirrin â€کya’yansu. Don haka ne ma a matakin farko su ma kenan abin kaddarawa shi ne; cewar iyayensu sun tarbiyyatar da su domin su shayar da na gabansu wannan tarbiyyar. Kuma lallai wannan nauyi ne kuma aiki ne mai nauyi da Allah madaukaki ya dora shi akan iyaye, ba wai abu ne na ganin dama ba, kuma idan suka kiyaye wannan to lallai zasu fitar da sakamako mai kyau ga al’ummarsu da zata cigaba har kiyama ta tashi tana tunawa da su tana yi musu addu’a. tunda iyaye ne suke farawa, sannan kuma â€کya’ya bayan sun girma su ma su kiyaye nasu janibin nauyin da ya hau kansu, don haka ne ma ya kamata mu fara da batun hakkokin da suka hau kansu sannan sai mu gangara zuwa ga na â€کya’yansu.


[1] Surar Isra’i: 23.
[2] Surar Tahrim: 6.

 



back 1 next