Musulmin Duniya



 Mafi girman abin da ya kai mu ga fadawa cikin wannan halin bai wuce rashin fahimtar musulunci ba, da kyakkyawar koyarwar da ya bari cikin biyayya ga Kur’ani da Alayen Manzon Allah (s.a.w). Sai aka yi nisa da Kur’ani mai girma da koyarwarsa, Alayen Muhammad (s.a.w) kuwa aka yi watsi da su, ba ma kawai an yi watsi da su ba ne, sai da aka yi wa al’umma mummunar tarbiyyar kyamar Annabi (s.a.w) da Alayensa, sannan kuma aka kyamaci koyarwarsu.

Kuma abin takaici wannan lamari ya yi muni har zuwa yau, ta yadda hatta da fadar abin da ya faru kansu laifi ne, mafi muni shi ne yabon wadanda suka yi musu kisan kare dangi irinsu Yazid dan Mu’awiya, sannan kuma kyamar mazhabarsu da yi mata bita-dakulli. Masu jin cewa da suna raye aka kashe Alayen Annabi (s.a.w) da zuriyarsu da sun ba wa sarakuna tasu gudummuwa, sai suka ga bari su bi mabiyansu da takurawa da kashewa, don haka sai suka sanya dukkan karfinsu wurin gaba da mabiyansu da tafarkinsu.

Wani mutumin Sham ya ga Imam Hasan (a.s) yana haye kan dabba, sai ya rika la'antar imam Hasan (a.s), shi kuwa Imam Hasan (a.s) bai  yi masa raddi ba. Yayin da ya gama sai Imam Hasan (a.s) ya zo wajensa ya yi masa sallama ya yi dariya ya ce: Ya kai wannan tsoho ina tsammanin kai bako ne a wannan gari, ta yiwu ka yi batan kai. Amma da ka roke mu da mun ba ka, kuma da ka nemi shiryarwarmu da mun shiryar da kai, da ka nemi mu hau da kai da mun ba ka abin hawa. Idan kuwa kana jin yunwa ne to sai mu ciyar da kai, idan kuwa kana da tsaraici ne to sai mu tufatar da kai, idan kuwa kana da talauci ne sai mu wadata ka, idan ka kasance korarre ne sai mu ba ka wajen zama, idan kuwa kana da wata bukata ne sai mu biya maka. Yayin da mutumin nan ya ji wannan magana sai ya yi kuka ya ce: Na shaida kai ne halifan Allah a bayan kasa, Allah ne kawai ya san inda yake sanya sakonsa. ( Manakib: Mujalladi 4, shafi: 19).

Wannan shi ne jikan Manzon Allah (s.a.w) na farko imam Hasan dan Ali da Fadima (a.s), amma Mu'awiya dan Abu Sufyan ya tarbiyyantar da al'umma kan kin su, sannan ya sanya matar Imam Hasan (a.s) ta sanya masa gubar da ta kashe shi, sannan ya wajabta la’antar dan’uwan Manzon Allah -kuma baban Hasan wato Imam Ali da yake baban zuriyar Annabi (s.a.w)- a kan mimbari da ake kiran wannan la'anar da Sunna har tsawon shekaru tamanin sai a zamanin halifancin Umar dan Abdul’aziz sannan ya hana wannan Sunna -ta la'anar Imam Ali- da aka sanya mata hadisai masu nuna falalarta.

Sannan ga yunkurin cire shaidawa da manzancin Manzon Allah (s.a.w) a kiran salla da shi ma bai ci nasara ba. Amma duk da haka sai ga al’ummar musulmi ta karbi wannan tafarkin sai ‘yan kadan da Allah ya yi wa ludufinsa. Don haka ya hau kan al’ummar musulmi su tashi tsaye domin fahimtar meye musulunci sahihi da Annabi ya zo da shi, wanda yake wajabta girmama Annabi (s.a.w), da riko da Kur’ani da Alayen Annabi (s.a.w), wanda ya fadi sunansu da kansa da cewa su sha biyu ne bayansa.

Ta yiwu wani ya ce: Duk da mun san cewa; Annabi (s.a.w) ya bar mana halifofi kuma imamai jagorori sha biyu ne, amma ai littattafai kamar Muslim da sauransu sun fadi adadi ne kawai amma ba su kawo sunayen ba?

Sai mu ce: Alayen Annabi (s.a.w) sun ruwaito su waye da sunayensu. Sannan kuma shin akwai wani mai hankali da zai bar wani abu muhimmi da cewa na wasu ne bayan mutuwarsa, sannan sai ya yi shiru bai fadi su waye ba?! Balle addinin Allah madaukaki da yake makomar shiriya har tashin kiyama! Ko kuma an boye su ne saboda kawai suna Alayen Manzon Allah!? Ko kuwa akwai wani wanda zai iya kawo su a lokacin da hukuncin hakan yake nufin fille wuyansa?! Ko ba mu gani ba ne cewa; sanya sunan Ali kawai a wancan zamanin yana iya kaiwa ga hukuncin kisa?!

Yana da muhimmanci matuka mu koma wa tarihin Annabi (s.a.w) da daulolin da suka zo bayansa domin sanin makomar musulunci da musulmi bayansa, kamar dai yadda yahudawa da nasara suka kasance bayan annabawa, sai maganar Manzon Allah (s.a.w) ta gaskata cewa; al’ummarsa sai ta bi abin da suka yi taku-da-taku. Don haka mu yi hattara! mu san muna da nauyin amanar sakon Manzon Allah (s.a.w) a hannunmu. Kuma idan muka kiyaye to mu muka amfana, idan kuwa ba mu kiyaye ba, to ba zamu cutar da Allah da komai ba!.

Manzon Allah da Alayensa (a.s) sun yi mu'amala da wadanda ba musulmi ba kyakkyawar mu’amala fiye da ta sarakunan musulmi da aka yi a dauloli. Don haka ne ma zamu ga hatta da Kiristoci sun tausaya wa Alayen Manzon Allah (s.a.w) a lokutan wadannan dauloli fiye da yadda musulmi kansu suka tausaya musu. Hasali ma musulmin ba su tausaya musu ba sai ‘yan kadan daga ciki, kissoshin kisan kare dangi da aka yi musu lokacin sarakuna musamman irinsu Yazidu da Harunar Rashid ba boye suke ba. Bincika ka ga tarihin rashin imanin da ba a taba yin sa ba a tarihin dan Adam. Duba littattafan tarihi da musulmi suka rubuta kamar Makatilul Talibiyyin.

Don haka muna da aiki babba a gabanmu, mu koma cikin hayyacinmu, mu nisanci dimuwa, mu yi aiki da wasiyyar Annabi ga wannan al’umma, mu so juna, mu hade wuri daya, mu nuna wa duniya hakikanin sakon Annabi (s.a.w), da wannan ne Annabi zai yi farin ciki da mu a mauludinsa. Amma mu yabe shi mu fadi rayuwarsa, sannan kuma a aikace mu saba mata gaba daya, kamar muna isgili ne ma.



back 1 2 3 4 5 next