Aure Mai Iyaka



 

Hafiz Muhammad Sa'id

Aure Mai Iyaka (Auren Jin Dadi)

Yardajjen Tunani

Duk wani addini da ya kasa warware matsalar dan Adam to wannan addinin ba cikakken addini ba ne, don haka ba shi da wani matsayi a wurin Allah madaukaki, haka nan ma duk wata mazhaba da ta kasa warware matsalar dan Adam to a bisa hakika wannan mazhabar ba ta da wata kamala, kuma ta rasa yarda daga wurin Allah madaukaki. Akwai bambanci matuka tsakanin a samu ra'ayin mazhaba ko addini mai kamala da cika, da kuma gazawar masu wannan mazhabar ko addinin.

Auren mutu’a yana daga cikin abin da yake iya warware matsalar dan Adam ta kawar da fasadi a duniya a cikin al’ummu, don haka mazhabin da yake da wannan fikira mai kima shi ne ya kamata ya yi magana game da warware matsalar dan Adam. Imam Musa Sadar yana cewa: |"Musulunci shi ne addinin kadaita Allah madaukaki…". Kafin nan yana cewa: "Addinai sun kasance abu guda ta fuskacin cewa; dukkaninsu suna hidimar hadafi daya ne wadanda suka hada kira zuwa ga Allah da hidimar mutum, kuma wadannan abubuwa biyu fuska ne na abubuwa guda biyu"[1]. Wannan yana nufin cewa; imani da Allah ba ya zama na gaskiya sai idan imani da cewa; addini ya zo ne domin hidimar mutane, ba mutum ne zai kasance domin hidimar addini ba, kuma duk wani addini da ba zai iya warware matsalar dan Adam ba, kuma ba zai iya daukaka kimarsa ba, to wannan addinin ba na Allah ba ne, kuma Allah ya barranta daga wannan addini.

Aure mai iyaka, ko kuma auren jin dadi, ko kuma auren mutu'a, aure ne wanda yake daga mukullan kawar da fasadi a cikin kowace al'umma, sai dai magana kan hakan tana da tsawo. Sannan kuma aure ne wanda yana nan kan halaccinsa har abada, domin hadisi ya zo cewa: "Halal din Muhammad (s.a.w), halal ne har zuwa ranar kiyama, kuma haram dinsa, haram ne har zuwa ranar kiyama[2].

Saboda gobe ranar Laraba, ta yi daidai da ranar shahadar Imam Ja'afar Sadik (a.s), wato Imami na shida daga alayen manzon Allah (s.a.w), kuma wadanda aka sani da Ahlul Baiti (a.s), don haka ina mika ladan wannan rubutu zuwa gareshi!.

Hafiz Muhammad Sa'id, hfazah@yahoo.com,

Tuesday, October 13, 2009, Tuesday, Shawwal 24, 1430,

Tuesday, Mihir 21, 1388

Mene ne Aure

Aure alaka ce kebantacciya ta shari’a ko al’ada wacce ake kulla ta tsakanin mace da namiji, da lafazi na musamman, wacce take halatta wa kowanne daga bangarori biyu junansu.

Shari’ar musulunci ta nisantar da mutane daga zaman gwagwarci, ta kwadaitar da su yin aure domin samun al’umma ta gari mai kame kai, da kuma renon manyan gobe wadanda zasu ci gaba da shiryar da na baya masu zuwa, zuwa ga tafarkin tsira.

Nau’o’in Aure



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next