Sayyid Khomaini



Imam Khumaini ya yi aikin yada ilimi haikan, ta hanyar karantarwa da talife talife. A fannin karantarwa ya karantar da dalibai a fannonin ilimi a Makarantar Faidhiyya da Masallacin al-A'azam da Masallacin al-Muhammadiyya da Makarantar Al-Haj Mulla Sadik da Masallacin al-Silmasi duk a birnin Kum; ance daliban dake halartar karatuttukansa a wadannan wurare sun wuce dubu daya. Haka a lokacin zamansa a Najaf ta kasar Iraki ya karantar a Masallacin al-Ansari har na tsawon shekaru goma sha hudu (a nan ne ma ya fara bijiro da mas'alar Shika Shikan Gwamnatin Musulunci). Ta wannan hanya ce ya sami daman yaye wasu zakakurai wadanda suka kasance, kuma ba su gushe ba, masu misalta tunaninsa da halayyarsa, irin su Ayatullahi (Prof.) Shahid Murtdha Mutahhari (Allah Ya ji-kansa), da Ayatullahi Shahid Sayyid Baheshti (Allah Ya lullube shi da rahmarSa), da Ayatullahi (Dr.) Shahid Mufatteh (wanda ya hada baiwar zurfafawa a ilimin addini da na zamani). Sheikh Hashimi Rafsanjani da magajin Imam kuma ja-goran juyin Musulunci, Ayatullahi Sayyid Ali Khamina'i. Wadannan da ire irensu masu yawa sun haskaka da Imam a ilmance da tarbiyyance.

Bayan wafatin Ayatullahi al-Ha'iri ne wasu kwararru suka fara tuntubar Imam don rike akalar Marja'iyyar Kum (wanda shi ne matsayin addini da ya fi kowanne a tsarin Musuluncin Shi'a), amma tsantseninsa ya sa ya yi ta kau da kai. Sai ma ya shugabanci gungun wasu malaman Kum da suka nace har suka ga sun gamsar da Ayatullahi al-Burjurdi da ya baro Najaf ya dawo Kum don shugabatar Cibiyar.

Harkokin karatu da karantarwa ba su dauke hankalin Imam Kumaini daga talifi ba. A duk lokacin da ya fahimci bukatar wallafawa ko sharhi ko taliki a kan wani littafi yakan kebe lokaci don haka. Wannan ya sa Imam ya bar littafan da suka kai hamsin, tsakanin wadanda ya wallafa da wadanda ya yiwa taliki. Wasu daga cikinsu har yanzu ba a buga su ba. Daga wadanda aka buga an kididdige kimanin arba'in da biyar da suka hada da Kitabul-Bai'i (mai mujalladi biyar), da Bada'iul-Durar Fi Ka'idati Nafyil-Dharar, da Anwarul-Hidaya Fit Ta'alikti alal-Kifaya (kan Usulul-Fikh), da Sirrul-Salat, da Adaabul-Ma'anawiyyati Lis-Salat (duk a kan Irfani), da al-Hashiyatu ala Sharhi Fusus al-Hikam (wanda ya yi taliki a kan sharhin littafin Fusus al-Hikam na Ibin Arabi), da Misbahul-Hidaya, da al-Arba'una Haditha (inda ya zabi wasu hadisai arba'in ya yi sharhinsu kan kyautata hali da tarbiyya), da Jihadul-Akbar, da Manahijul-Wusuli Ila Ilmil-Usul, da Tahrirul-Wasila da wasu masu yawa.

Mujahidi Na Hakika

Karfin halin Jihadi saboda Allah da ruhin yunkurawa don tabbatar da adalci da kare mutuncin talakawa da wadanda ake zalunta da Imam Khumaini ke da shi sun samo asali ne daga akida da tarbiyyar gida da kyawawan dabi'u da zurfin ilimi da suka kewaye rayuwarsa, abin ya kuma hadu da tabarbarewar yanayin siyasa da na zamantakewa a duniya da Iran ta lokacin.

Imam bai fara yunkurin siyasa bisa tunanin kau da gwamnatin ba; ya fara ne da nasiha ga mahukunta da tsawatar da su a kan zalunci da irin makauniyar biyayyar da suke yi wa 'yan mulkin-mallakan kasashen Gabashi da Yammaci. Wannan ya sa ya rika bibiyar kudurorin hukuma da yadda take gudanar da mulki sau da kafa don cimma haka. Misali a ranar 8/10/1963 a gab da zabubbukan majalisun kananan hukumomi, gwamnatin Iran ta lokacin ta fitar da dokar share sharadin Musulunci a kan masu zabe da 'yan takara; haka nan ta musanya rantsar da zababbun wakilai da AlKur'ani zuwa rantsar da su da kundin tsarin mulki. Imam ya yi matukar adawa da wannan mataki, kuma ya sa shi ya zama asasin fadakar da jama'a wajen bijere wa gwanmatin Shah Ridha Pahlawi.

Imam bai kyamaci akidar "a shiga a gyara ba"; abin da ya kyamata shi ne "a shiga a zagwanye", wato tasirantuwa da mummunan yanayi. Wannan yasa ya yi amfani da hanyoyin gyara ta ciki da wajen hukuma; domin kuwa ya tura muridansa cikin gwamnati don kara kyautata abin da bai baci ba, da gyara mummunan yanayin da ya baci gwargwadon iko. Kamar yadda ya yi amfani da wadanda ba sa cikin gwamnati wajen ganin kiransa na kawo gyara ya yi tasiri, wannan ne ma ya sa juyin da ya ja-goranta daga baya ya hado kowa da kowa.

Imam ya iya hado kan da yawa daga malamai da daliban addini da na jami'o'i wajen shiga sahun hamayya da matakan gwamnati da suka zama hadari ga addini da al'umma a wannan kasa da musulmi suka wuce kashi casa'in da takwas bisa dari na duk al'ummarta. Wannan ya kuwa faru ne saboda yadda suka san cewa a tsawon rayuwarsa ya kasance tare da su (ta hanyar kasancewa dalibi ga wasu kuma malami ga wasu); ga shi dan kasa na gari da 'yan boko suka san shi da kishin kasa da taimakon jama'a. Tare da duk wadannan, ga yadda ya iya bayyana manufofinsa da kare su daidai da ka'idojin Musulunci ta yadda kowa ya fahimta. Kamar haka ya sami amincewar talakawa saboda kyawawan dabi'unsa da taimakonsa gare su da kulawa da rayuwarsu da lafiyarsu da son ci-gabansu da suka sani daga gare shi tuntuni.

Sabanin yadda Turawan Yamma ke son nuna shi, Imam ya kasance mai tausasawa a kiransa. Bai tsananta wa sarki Shah da mukarrabansa ba, duk kuwa da halin taurin kai da rashin jin nasiha da girman-kai da suka rika nunawa.

Shugaba Na Kowa Da Kowa

Bayan kafa gwamnatin Musulunci Imam ya misalta adalcin nan na Musulunci a kan al'umma. Ya kare mutuncin wadanda ake zalunta a kasashen duniya ta hanyar taimakon gwamnati da kariyar siyasa da addu'o'i. Bai taba gafala daga abin da ya shafi al'ummar Musulmi a duniya ba. Ya sauke nauyin da ya hau kan malaman addini kan hadin kai da al'amarin Falasdinu da mafi kyawun fuska. Ya samar wa al'umma da alkibla a lokacin da ake neman ruda ta da tsare tsare na yaudara a fannonin rayuwa. Ya daukaka matsayin al'ummar Musulmi a duniya ta hanyar kare mutuncinta da 'yancinta. Ya sadaukar da jin dadin mutanen kasarsa don kare martabar wadanda ake zalunta a duniya. Sai ga taimakonsa da goyon-bayansa sun isa ga 'yan gwagwarmayar neman 'yanci a Afrika Ta Kudu da Nicaragua da Namibiya. Ya bude kofofin Jumhuriyar Musulunci ga 'yan gudun hijra makota daga Afganistan da yaki ya daidaita, da wadanda suka gudo daga Iraki da mulkin danniya da kama-karyar Saddam Hussain ya hana numfashi, da sauran kasashen da aka hana 'yancin addini a tsohuwar Tarayyar Sobiet. Ya daidaita tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba a wajen adalci da 'yanci. Ya kawar da kai daga bambance bambancen mazhabobin musulmi, yayin da ya hada hankalinsa a kan abubuwan da suka hada kan Musulmi. Ya fitar da mata daga kangin bautar jiki da biyan bukatun maza zuwa bautar Allah da karimci. Mace ta yi kafada-da-kafada da namiji a fagagen rayuwa da ciyar da al'umma gaba bisa karantarwarsa.

A karshe ina cewa ne Imam samfuri ne na dalibi mai kokari da naci da aiki da ilimi, kuma misali ne mai kyau na nagartaccen malamin addini da bai taba kawar da kai daga ainihin ayyukansa na karantarwa da tarbiyya ba, mai kishin kasarsa da mutanensa da addininsa da bai taba sayar da daya daga wadannan ko watsar da shi da ci-gabayansa ba, miji na gari mai tausayi ga iyalinsa, uba mai tarbiyya da kulawa ga 'ya'yansa, gwarzon namiji da bai san tsoro ko ja da baya ba, shugaba mai adalci da bai bambanta kansa da talakawa da masu karamin karfi ba.

Wannan taliki zai saura abin koyin 'yantattu da wadanda suka fahimci manufar samuwarsu a duniya. Allah Ya saka masa da alheri a kan abin da ya gabatar ga 'yan Adam.

 



back 1 2