Bada'i(Canjawa)



3-Tasirin ayyuka a game da makomar mutum; wanan kuma gaskiya ce tabbatacciya ta kur’ani,  hada da cewa sunnar annabi mutawatira ta zo da karfafawa a kan hakan, da cewa ayyukan mutum na imani, da shirka, da biyayya, da sabo, da bin iyaye, da saba musu, da ciyar da talakawa, da kamewa ga barin hakan, da sadar da zumunci, da yankewa,… duk suna da tasiri wajan arziki da albarkar da kuma tsawon rayuwa da sa’ada. Wadannan al’amura suna daga abubuwan da kur’ani ya ambata saudayawa, kuma sunnar annabi ta karfafa su.

Fadinsa madaukaki “Allah ba ya canja abin da yake ga mutane har sai sun canja abin da yake garesu”. Wanda yake musun Bada musunsa zai kai shi zuwa ga musun wannan hakika bayyananniya ce koda kuwa yana imani da ita, ya sani cewa wannan abin da yake imani da shi, shi ne imamiyya take kira da Bada.

 

Maganar Malaman Imamiyya Game Da Bada

Wanann shi ne abin da malamai na imamiyya suka karfafa na da da na yanzu, Shaihul Mufid yana cewa: “Fadin imamiyya game da Bada an same shi ne daga ruwaya ba daga hankali ba… ba abin da ake nufi da shi sai bayyanar wani ra’ayi bayan waninsa da kuma bayyanar al’amari bayan ya buya, Ubangiji madaukakin sarki a dukkan ayyukansa bayyanannu ne a cikin halittarsa bayan ta kasance, kuma ayyukansa sanannu ne gunsa cikin abin da bai gushe ba”[12].

 Sheikh Tusi yana cewa: “Bada hakikarsa a luga shi ne bayyana saboda haka ne ake cewa katangun gari sun bayyana garemu kuma ra’ayin ya bayyana garemu… amma idan aka raba wannan lafazi zuwa ga Allah (S.W.T), to akwai abin da ya halatta a danganta shi gareshi da kuma abin da bai halatta ba; Amma abin da ya halatta Bada shi ne abin da yake halatta shafe hukuncin shari’a, a kan haka ne kuma ake fassara duk abin da ya zo na daga hadisan Bada wanda ya zo daga imamai (A.S) banda da ma’anar da ba ta halatta ba ga Allah madaukakin sarki na ma’anar samun ilimin da bai sani ba a da”[13].

Sayyid Abdullahi Shubbair ya ce: “Bada tana da ma’anoni masu yawa wasu ana iya siffanta Allah da su wasu kuma ba ya yiwuwa a sifatan shi da su, kuma al’umma ta hadu a kan cewa; ma’anar samuwar ilimi bayan jahilci ba ya halatta ga Allah kuma wanda ya daganta wa imamiyya wannan to ya yi musu kagen karya kuma imamiyya sun barranta da shi”[14].

Sayyid Abdulhusain Sharafuddin ya ce: “Abin da shi’a suke cewa shi ne Allah yana rage rashin lafiya ko ya dada shi, haka nan ma game da lafiya da cuta da dacewa da tabewa da bala’o’i da musibu da imani da kafirci da saurana abubuwa kamar yadda Allah (S.W.T) yake fada: “Yana shafe abin da ya so ya na kuma tabbatarwa kuma a gunsa akwai Ummul kitab”[15].

Wannan shi ne abin da Umar dan Khaddabi ya tafi akansa da dan Mas’ud da Abi Wa’il da Katada kuma Jabir ya rawaito shi daga manzon Allah (S.A.W), haka nan da yawa daga magabata suna addu’a suna kaskan da kai ga Allah da ya sanya su cikin masu arzuta ba masu tabewa ba, kuma hadisai mutawatirai sun zo daga imamanmu (A.S) a cikin addu’i da aka ruwaito, kuma ya zo a cikin littattafan Sunan masu yawa cewa sadaka, da bin iyaye, da aikata kyakkyawa, suna mayar da tabewa ta koma arzuta kuma su dada tsawon rayuwar mutum, kuma ya inganta daga Dan Abbas ya ce: “Daukar mataki ba ya kawar da kaddara sai dai Allah yana shafe abin da ya so na kaddara da addu’a”. Wannan kuma shi ne Bada din da shi’a suka tafi akansa kuma sabaninmu da Ahlussunna a Bada a lafazi ne… abin da shi’a suka fada game da Bada da wannan ma’ana da muka ambata dukkan musulmi sun tafi akansa…”[16].

Shaikh Aga Buzurg ya rubuta yana cewa: “Bada ma’anarsa a lugga shi ne; Bayyanar wani ra’ayi da babu shi a da da kuma canjin wani abu da aka sani bayan da ba a san shi ba. Wannan ita ce fahimtar dukkan mutane sai dai wannan mustahili ne ga Allah (S.W.T) saboda yana lizimtar bayyanar sani da wani abu da da dacan ba a san shi ba, ko kuma gajiya a kan aikata shi wanda Allah ya tsarakaka daga garesu… Bada da imamiyya suke kudurce shi; Shi ne wanda sauran musulmi suke imani da shi da yake sabanin abin da yahudawa suka tafi a kai na cewa; Allah ya riga ya gama komai kuma ba yadda za a yi wani abu ya canja gunsa “Hannun Allah abin yi wa kukumi ne”. Ko kuma idan ka bi maganganun yahudawa zaka ga cewa suna ganin Allah ya samar da dukkan halittu a tashi daya. Babu wani abu da za a samu gunsa sai ya kasance da ma can an same shi tun farko. Ko kuma masu ganin cewa Allah ya halicci mala’ika na farko da sauran rauhanai masu juya falaki kuma ya bar su su aiwatar da abin da su kan tafiyar da al’amuran bayi, shi kuma ya kau da hannunsa wajan tafiyarwa. To wadannan akidoji dole ne ga kowane musulmi ya kore su ya kuma kudurce cewa Allah madaukakin sarki: “Kowace rana shi yana cikin wani sha’ani...[17]”[18].

 

Muhimmancin Bada Wajan Tarbiyyantarwa

 

Da Ingantacciyar Akida

Ya bayyana kamar yadda ya rigaya cewa; Bada yana da ma’ana da take sananniya gun musulmi gaba daya kuma imamiyya ba su da wata ma’ana da ban da ta sabawa sauran musulmi, sai dai kawai ma’ana ta lugga da lafazi da aka fahimci kuskure ne dangantawa Allah jahilci kuma ya bayyana cewa bai halatta ba danganta wannan ma’ana ga Allah madaukakin sarki. Domin akidun musulmi ana auna su da ma’aunin asasinta na ilimi da kuma dalilanta na hankali ne wani lokacin kuma da sakamakon da take haifarwa, amma game da Bada akwai tambayoyi da zamu iya kawowa da kuma amsar su kamar haka:

*- Idan ya kasance Allah ya riga ya yi hukunci na farko kuma ya san ba shi ne zai yi tasiri ba zai kai ga wurgar da shi ne, to menene amfanin bayar da labarinsa? Menene kuma amfanin da za a samu daga Bada a wannan yanayin?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next